Umurnan Jehobah Tabbatattu Ne
‘[Umurnan] Ubangiji tabbatattu ne, suna sa mara-sani ya zama mai-hikima.’—ZAB. 19:7.
1. Waɗanne batutuwa ne ake yawan tattaunawa a taronmu, kuma ta yaya muke amfana daga maimaita su?
SA’AD DA kake shirya wani talifin Hasumiyar Tsaro da za a tattauna a taro, wataƙila ka taɓa cewa, ‘Ai mun taɓa nazarta wannan batun.’ Idan ka daɗe da zama Mashaidin Jehobah, za ka ga cewa an taɓa tattauna wasu batutuwa sau da sau. Mukan yi nazarin wasu batutuwa kamar su Mulkin Allah da fansa da aikin wa’azi da kuma wasu halaye kamar su ƙauna da bangaskiya a kai a kai. Maimaita waɗannan batutuwa a kai a kai yana ƙarfafa bangaskiyarmu, kuma yana taimaka mana mu “zama masu-aika magana, ba masu-ji kaɗai ba.”—Yaƙ. 1:22.
2. (a) A yawancin lokaci, mene ne umurnin Allah yake nufi? (b) Ta yaya umurnan Allah ya sha bambam da na mutane?
2 A cikin Littafi Mai Tsarki, “umurni” a yawancin lokaci yana nufin dokoki da ƙa’idodin da Allah yake ba mutanensa. Umurnan Jehobah tabbatattu ne amma na ’yan Adam suna bukatar gyara a kai a kai. Saboda haka, za mu iya gaskata cewa za mu amfana idan muka yi biyayya ga dokokin Allah. Ko da yake Allah ya ba mutanensa wasu dokoki a dā da ba ma bukatar su a yau, hakan bai nuna cewa waɗannan dokokin ba su da kyau ba. Domin marubucin zabura ya ce: “[Umurnanka] masu-adalci ne har abada.”—Zab. 119:144.
3, 4. (a) Mene ne umurnan Jehobah suka ƙunsa a wasu lokatai? (b) Ta yaya Isra’ilawa za su amfana idan suka yi biyayya ga umurnan Allah?
3 A wasu lokatai, umurnan Jehobah suna ɗauke da kashedi. Allah ya tura annabawansa a kai a kai a dā don su yi wa Isra’ilawa kashedi. Alal misali, Musa ya yi wa Isra’ilawa kashedi kafin su shiga Ƙasar Alkawari. Ya ce: “Ku yi lura da kanku, domin kada zuciyarku ta ruɗe, har ku ratse ku bauta wa waɗansu alloli, ku yi masu sujada; kāna fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kanku.” (K. Sha 11:16, 17) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah ya ba mutanensa wasu umurnai ma da yawa.
4 A lokatai da yawa, Allah ya gaya wa mutanensa su ji tsoronsa, su saurare shi kuma su tsarkake sunansa. (K. Sha 4:29-31; 5:28, 29) Idan suka yi biyayya ga waɗannan umurnan, za su sami albarka sosai.—Lev. 26:3-6; K. Sha 28:1-4.
YADDA ISRA’ILAWA SUKA ƊAUKI UMURNAN ALLAH
5. Me ya sa Jehobah ya yi yaƙi domin Sarki Hezekiya?
5 Allah ya cika alkawarinsa a duk sha’anin da ya yi da Isra’ilawa. Alal misali, sa’ad da Sarkin Assyria Sennakerib ya kai hari a ƙasar Yahuda kuma ya yi wa Sarki Hezekiya barazana, Jehobah ya aika mala’ikansa ya taimaka wa mutanensa. A dare ɗaya kawai, mala’ikan Allah ya halaka “dukan jarumawa, da manya da shugabannai, a cikin sansanin sarkin Assyria. Ya fa koma garinsa da kunya.” (2 Laba. 32:21; 2 Sar. 19:35) Me ya sa Allah ya yi yaƙi domin Sarki Hezekiya? Domin Hezekiya “ya manne wa Ubangiji, ba ya rabu da binsa ba, amma ya kiyaye umurnansa.”—2 Sar. 18:1, 5, 6.
6. Ta yaya Sarki Josiah ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah?
6 Wani kuma da ya yi biyayya ga umurnin Jehobah shi ne Sarki Josiah. Josiah “ya yi abin da ke daidai a gaban Ubangiji” tun yana ƙarami, “ba ya ratse ga hannun dama ko hagu ba.” (2 Laba. 34:1, 2) Josiah ya nuna cewa ya dogara ga Jehobah ta wurin halaka dukan gumaka a ƙasar Isra’ila kuma ya sa aka soma bauta ta gaskiya. Abin da Josiah ya yi ya sa shi da dukan al’ummar Isra’ila sun sami albarka.—Karanta 2 Labarbaru 34:31-33.
7. Me ya sami Isra’ilawa sa’ad da suka ƙi bin umurnan Jehobah?
7 Abin baƙin ciki shi ne, mutanen Allah sun riƙa yin biris da umurnan Jehobah. Sa’ad da bangaskiyarsu ta yi sanyi, an riƙa rinjayarsu su bauta wa wasu allolin ƙarya. (Afis. 4:13, 14) Allah ya gaya musu cewa idan ba su bi umurnansa ba, za su sha wuya sosai.—Lev. 26:23-25; Irm. 5:23-25.
8. Mene ne za mu iya koya daga labarin Isra’ilawa?
8 Mene ne za mu iya koya daga labarin Isra’ilawa? A yau ma, mutanen Allah suna samun umurnai da kuma horo kamar Isra’ilawa. (2 Bit. 1:12) A duk lokacin da muka karanta Littafi Mai Tsarki, muna tuna wa kanmu umurnan Allah. Jehobah kuma yana barin mu mu zaɓa mu bi umurninsa ko kuma mu yi abin da muke ganin ya dace. (Mis. 14:12) Bari mu tattauna wasu dalilan da suka sa za mu dogara ga umurnan Jehobah da yadda za mu amfana daga bin su.
KA SAURARI ALLAH DON KA RAYU
9. Sa’ad da Isra’ilawa suke jeji, ta yaya Jehobah ya tabbatar musu cewa yana mara musu baya?
9 Sa’ad da Isra’ilawa suka soma gantali a cikin jeji har tsawon shekara arba’in, Jehobah bai gaya musu dalla-dalla abin da zai yi don ya ja-gorance su da cece su da kuma kula da su ba. Amma ya tabbatar musu a hanyoyi da yawa cewa za su amfana idan suka dogara gare shi kuma suka bi umurnansa. Ta yin amfani da umudin girgije da rana da kuma umudin wuta da dare, Jehobah ya tabbatar wa mutanensa cewa yana mara musu baya a wannan tafiya mai wuya da sa suke yi. (K. Sha 1:19; Fit. 40:36-38) Kuma Allah ya tanadar musu da bukatunsu. Ta yaya muka sani? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tufafinsu ba su tsufa ba, ƙafafunsu ba su kumbura ba.” Hakika “ba su rasa komi ba.”—Neh. 9:19-21.
10. A wace hanya ce Jehobah yake ja-gorar mutanensa a yau?
10 Nan ba da daɗewa ba, bayin Allah za su shiga sabuwar duniya mai adalci. Shin mun dogara ga Jehobah cewa zai tanadar mana da bukatunmu don mu tsira wa “ƙunci mai-girma” da ke tafe? (Mat. 24:21, 22; Zab. 119:40, 41) Ko da yake Jehobah ba ya yin amfani da umudin girgije da na wuta don ya ja-gorance mu zuwa sabuwar duniya, amma yana amfani da ƙungiyarsa don ya taimaka mana mu kasance a faɗake. Alal misali, an ƙarfafa mu mu riƙa karatun Littafi Mai Tsarki da Bauta ta Iyali da yamma da halartan taro da kuma yin wa’azi, don mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Zai dace mu yi wasu gyare-gyare a salon rayuwarmu don mu bi waɗannan umurnan, ko ba haka ba? Yin hakan zai taimaka mana mu kasance da bangaskiyar da za ta sa mu tsira zuwa sabuwar duniya.
11. A waɗanne hanyoyi ne Allah ya nuna cewa yana kula da mu?
11 Ban da taimaka mana mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah, ƙungiyar Jehobah tana ba mu umurnai a yadda za mu iya tsai da shawarwari da suka dace a rayuwarmu na yau da kullum. Wasu cikin waɗannan misalan su ne ƙarfafawa da muka samu na kasancewa da ra’ayin da ya dace game da abin duniya da kuma yin rayuwa mai sauƙi don mu rage ɗawainiya. Har ila, mun sami ƙarfafa a yadda za mu riƙa yin ado da zaɓan nishaɗi da kuma zuwa wasu makarantun gaba da sakandare kamar jami’a. An sake ba mu wasu umurnan kiyaye haɗari a gidajenmu da motocinmu da Majami’un Mulki da kuma yadda za mu kasance a faɗake don tsautsayi ko bala’i. Waɗannan umurnan sun nuna cewa Allah yana kula da mu sosai.
UMURNAI SUN TAIMAKI KIRISTOCI NA DĀ SU KASANCE DA AMINCI
12. (a) Wane batu ne Yesu ya tattauna da almajiransa a kai a kai? (b) Mene ne Yesu ya yi da Bitrus bai manta ba, kuma wane darasi ne za mu iya koya?
12 A ƙarni na farko, mutanen Allah sun sami umurnai a kai a kai. Sau da yawa, Yesu ya gaya wa almajiransa su riƙa kasancewa da tawali’u. Ba wai Yesu ya gaya musu kawai ma’anar tawali’u ba, amma ya nuna musu yadda za su kasance da tawali’u. A daren da za a kashe Yesu, ya tara manzanninsa waje ɗaya don su yi Idin Ƙetarewa. Sa’ad da suke cin abinci, Yesu ya tashi kuma ya wanke ƙafafunsu. Wannan aikin bayi ne a zamanin dā. (Yoh. 13:1-17) Wannan abin da Yesu ya yi ya koya wa almajiransa darasi mai kyau sosai da ba za su taɓa mantawa ba. Shekaru 30 bayan haka, Bitrus wanda ɗaya ne cikin manzannin da Yesu ya wanke ƙafafunsu, ya gargaɗi ’yan’uwansa game da tawali’u. (1 Bit. 5:5) Misalin da Yesu ya kafa zai taimaka wa dukanmu mu kasance da tawali’u a yadda muke bi da juna.—Filib. 2:5-8.
13. Wane hali mai muhimmanci ne Yesu ya koya wa almajiransa?
13 Wani batu kuma da Yesu ya tattauna da almajiransa a kai a kai shi ne amfanin kasancewa da bangaskiya sosai. A wani lokaci, almajiran Yesu sun kasa fitar da aljani daga jikin wani mutum. Sai suka tambayi Yesu, suka ce: “Don me mu ba mu iya fitar da shi ba?” Yesu ya ce: “Saboda ƙaramtar bangaskiyarku: gama ina ce muku, Hakika, idan kuna da bangaskiya kwatancin ƙwayar mustard, . . . babu abin da ba za shi yiwu gareku ba.” (Mat. 17:14-20) A cikin shekarun da Yesu ya yi yana wa’azi a duniya, ya koya wa almajiransa cewa kasancewa da bangaskiya yana da muhimmanci sosai. (Karanta Matta 21:18-22.) Halartar dukan taron gunduma da na da’ira da kuma na musamman za ta ƙarfafa bangaskiyarmu. Muna halartar waɗannan taron ba don mu shaƙata ba, amma don mu nuna cewa muna dogara ga Jehobah.
14. Me ya sa yake da muhimmanci mu nuna ƙauna ba tare da son kai ba a yau?
14 Nassosin Helenanci na Kirista sun nanata muhimmancin nuna ƙauna ga mutane. Yesu ya ce doka ta biyu mafi muhimmanci ita ce, “ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” (Mat. 22:39) Hakazalika, Yaƙub ɗan’uwan Yesu ya ce ƙauna ce “shari’an nan ba-sarauciya.” (Yaƙ. 2:8) Manzo Yohanna ya ce: “Masoya, ba wata sabuwar doka ni ke rubuta maku ba, amma tsofuwar doka wadda kuke da ita tun daga farko.” (1 Yoh. 2:7, 8) Mene ne “tsofuwar doka” da Yohanna ya ambata yake nufi? Yana nufin dokar da aka ba mu cewa mu riƙa nuna ƙauna. Dokar ‘tsofuwa’ ce domin Yesu ya ba da ita shekaru da yawa da suka shige, wato “tun daga farko.” Amma dokar ‘sabuwa’ ce kuma domin sa’ad da almajiran Yesu suka fuskanci wasu sababbin yanayi a nan gaba, za su bukaci nuna ƙauna ta wajen sadaukar da kansu. Muna hamdala domin an ba mu gargaɗin da zai taimaka mana mu guji nuna son kai kamar yadda yawancin mutane suke yi a yau. Amma, ya kamata mu nuna ƙauna ba tare da son kai ba.
15. Mene ne ainihin aikin da Yesu ya yi a duniya?
15 Yesu ya kula da mutane sosai. Ya yi hakan ta wajen warkar da marasa lafiya da kuma ta da mutane daga mutuwa. Amma, ba ainihin abin da ya kawo shi duniya ke nan ba. Ya zo ne musamman don ya yi wa’azi da kuma koyar da mutane. Ta yaya hakan ya fi amfanar mutane? Dukan mutanen da Yesu ya warkar da kuma ta da daga mutuwa sun sake tsufa kuma sun mutu, amma waɗanda suka saurari wa’azin da ya yi sun sami zarafin yin rayuwa har abada.—Yoh. 11:25, 26.
16. A wace hanya ce Shaidun Jehobah suke bin umurnin da Yesu ya bayar cewa a almajirtar da mutane a yau?
16 Yesu ya umurci almajiransa cewa: “Ku tafi fa, ku almajirtarda dukan al’ummai.” (Mat. 28:19) Kiristoci a ƙarni na farko sun ci gaba da yin aikin da Yesu ya soma, kuma mu ma muna wannan wa’azin ga mutane da yawa da kuma a wurare da yawa sosai fiye da dā. Shaidun Jehobah fiye da miliyan bakwai suna wa mutane wa’azi game da Mulkin Allah a ƙasashe fiye da 230, kuma suna nazarin Littafi Mai Tsarki da miliyoyin mutane a kai a kai. Wannan wa’azin ya nuna cewa ƙarshen wannan mugun zamani ya kusa.
KA DOGARA GA JEHOBAH A YAU
17. Wane umurni ne Bulus da Bitrus suka bayar?
17 Hakika, umurnai sun taimaka wa Kiristoci a ƙarni na farko su ƙarfafa bangaskiyarsu. Alal misali, sa’ad da manzo Bulus yake cikin fursuna a ƙasar Roma, ya ce wa Timotawus: ‘Ka kiyaye kwatancin sahihiyan kalmomi waɗanda ya ji daga gare shi.’ (2 Tim. 1:13) Babu shakka, wannan furucin ya ƙarfafa Timotawus sosai. Bitrus ya ƙarfafa ’yan’uwansa su kasance da jimiri da ƙauna da kuma kamun kai. Bayan haka, sai ya ce “Zan fa kasance da shiri kullayaumi garin in tuna muku da waɗannan al’amura, ko da shi ke kun san su, kun kuwa kahu cikin gaskiya.”—2 Bit. 1:5-8, 12.
18. Yaya Kiristoci a ƙarni na farko suka ɗauki umurnan da aka ba su?
18 Hakika, wasiƙun da Bulus da kuma Bitrus suka rubuta sun jitu da “zantattuka waɗanda aka faɗi a dā ta bakin annabawa masu-tsarki.” (2 Bit. 3:2) Shin ’yan’uwanmu a ƙarni na farko sun yi fushi ne sa’ad da aka ba su waɗannan umurnan? A’a. Sun san cewa Allah yana ƙaunarsu kuma yana so su kasance da aminci, shi ya sa ya ba su umurnan.—2 Bit. 3:18.
19, 20. Me ya sa ya kamata mu dogara ga umurnan Jehobah, kuma ta yaya muke amfana idan muka yi hakan?
19 A yau ma, ya kamata mu dogara ga umurnan da Jehobah yake ba mu a cikin Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki kuma mu amince cewa za su amfane mu. (Karanta Joshua 23:14.) Littafi Mai Tsarki ya gaya mana yadda Allah ya bi da mutane cikin shekaru dubbai. An rubuta Littafi Mai Tsarki ne don mu amfana. (Rom. 15:4; 1 Kor. 10:11) Kuma muna ganin yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika a yau. Za a iya kamanta annabci da umurnan da aka rubuta shekaru da yawa kafin a soma bin su. Alal misali, miliyoyin mutane sun soma bauta wa Jehobah kamar yadda aka annabta cewa zai faru a “cikin kwanaki na ƙarshe.” (Isha. 2:2, 3) Yanayin duniyar nan yana daɗa muni kuma hakan cikar annabcin Littafi Mai Tsarki ne. Kuma kamar yadda muka tattauna, wa’azin bishara da ake yi a dukan duniya cikar annabcin Yesu ne.—Mat. 24:14.
20 Abubuwan da mahaliccinmu ya yi sun tabbatar mana cewa za mu iya dogara gare shi. Shin muna amfana daga umurnansa kuwa? Wata ’yar’uwa mai suna Rosellen ta ce: “Yayin da na soma dogara sosai ga Jehobah, sai na soma ganin yadda yake kula da kuma ƙarfafa ni.” Bari mu ma mu amfana daga bin umurnan Jehobah.