Ina Yin Iya Ƙoƙarina Kuwa?
1. Waɗanne abubuwa ne za su iya dami Kirista mai aminci?
1 Ka taɓa yi wa kanka wannan tambayar kuwa? Wataƙila ƙwazonka a hidima ya ragu saboda tsufa, rashin lafiya, ko kuma ƙarin hakkoki na iyali, kuma hakan yana sa ka sanyin gwiwa. Wata ’yar’uwa mai ’ya’ya uku ta rubuta cewa tana jin laifi a wasu lokatai domin lokaci da ƙarfin da take amfani da shi don kula da iyalinta ya rage abin da za ta iya yi a hidima. Menene zai taimaka mana mu kasance da daidaitaccen ra’ayi?
2. Menene Jehobah yake bukata a garemu?
2 Abin da Jehobah Yake Bukata a Garemu: Babu shakka, dukanmu za mu so mu saka hannu sosai a hidima. Amma akwai bambanci sosai tsakanin abin da muke son mu yi da kuma abin da za mu iya yi da gaske. Niyyar da muke da ita na son saka hannu sosai ya nuna cewa ba ma sakaci. Ya kamata mu tuna cewa Jehobah ya san kasawarmu sosai kuma ba ya bukatan abin da ya fi ƙarfinmu. (Zab. 103:13, 14) Menene yake bukata a gare mu? Yana son mu bauta masa da zuciya ɗaya, wato, mu yi iya ƙoƙarinmu.—Kol. 3:23.
3. Ta yaya za mu iya bincika ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu a hidima?
3 Menene zai taimake mu mu san abin da ya dace da mu? Za mu iya roƙi Jehobah ya taimaka mana mu fahimci yanayinmu sosai. (Zab. 26:2) Zai dace mu nemi taimakon aboki na gaske wanda Kirista ne da ya manyanta kuma wanda ba zai ji tsoron gaya mana inda muke bukatar yin gyara ba. (Mis. 27:9) Ka tuna cewa, tun da yanayi yana canjawa, yana da muhimmanci mu riƙa bincika yanayinmu akai-akai.—Afis. 5:10.
4. Yaya ya kamata mu ɗauki tunasarwa daga Littafi Mai Tsarki game da hidima?
4 Yadda Ya Kamata Mu Ɗauki Tunasarwa: Sa’ad da mutum yake gasar tsere, abokansa sukan ƙarfafa shi. Manufarsu ita ce taimaka wa masu tseren su cim ma makasudinsu, ba don su yi sanyin gwiwa ba. Hakazalika, ƙarfafawa da tunasarwa daga Littafi Mai Tsarki da muke samu a tarurrukanmu da kuma a littattafanmu na ‘mu yi wa’azin maganar Allah da gaggawa’ don amfaninmu ne, ba sa nufin cewa ba ma yin iya ƙoƙarinmu. (2 Tim. 4:2) Muna da tabbaci cewa idan muka ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu, Jehobah zai tuna ‘ƙaunarmu da ayyukanmu.’—Ibran. 6:10.