Bari Maganar Allah Ta Haskaka Hanyarka
“Maganarka . . . haske ne kuma a kan hanyata.”—ZABURA 119:105.
1, 2. A kan wane yanayi ne maganar Jehobah za ta haskaka hanyarmu?
MAGANAR Jehobah za ta haskaka hanyarmu idan muka ƙyale ta. Idan muna so mu more irin wannan haske na ruhaniya, dole ne mu zama ɗaliban rubutacciyar Maganar Allah kuma mu yi amfani da shawararta. Ta haka ne kawai za mu iya cewa kamar mai zabura: “Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni, haske ne kuma a kan hanyata.”—Zabura 119:105.
2 Bari yanzu mu tattauna Zabura 119:89-176. Waɗannan ayoyi suna ɗauke da cikakken bayani, kuma an tsara su cikin baiti 11! Suna iya taimaka mana mu kasance a hanyar rai madawwami.—Matiyu 7:13, 14.
Me Ya Sa Za Ka Ƙaunaci Maganar Allah?
3. Ta yaya ne Zabura 119:89, 90 suka nuna cewa za mu iya dogara ga maganar Allah?
3 Ƙaunar maganar Jehobah tana kawo ruhaniya mai ƙarfi. (Zabura 119:89-96) Mai zabura ya rera: “Maganarka tabbatacciya ce, ya Ubangiji, a kafe take a sama. . . . Ka kafa duniya a inda take, tana nan kuwa a wurin.” (Zabura 119:89, 90) Ta maganar Allah—“ka’idodin sammai”—halitta na samaniya suna tafiya a yadda aka tsara su kuma an kafa duniya sosai har abada. (Ayuba 38:31-33; Zabura 104:5) Muna iya gaskatawa da dukan wata magana da ta fito daga bakin Jehobah, abin da Allah ya ce ‘za ta yi kowane abu’ domin cika nufinsa.—Ishaya 55:8-11.
4. Mecece ƙaunar maganar Allah za ta yi wa bayinsa da suke wahala?
4 ‘Da ba domin dokar Allah ce sanadin farin cikin’ mai zabura ba, ‘da ya mutu saboda hukuncin da ya sha.’ (Zabura 119:92) ’Yan Isra’ila masu taka doka waɗanda suka ƙi jinin mai zabura ne suka tsananta masa, ba baƙi ba. (Littafin Firistoci 19:17) Amma hakan bai sha kansa ba, domin yana ƙaunar dokar Allah da ke kāre shi. A Koranti, manzo Bulus ya “sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya,” wataƙila har da ‘mafifitan manzanni’ da suke zarginsa. (2 Korantiyawa 11:5, 12-14, 26) Duk da haka, Bulus ya tsira a ruhaniya domin yana ƙaunar maganar Allah. Tun da yake muna ƙaunar rubutacciyar Maganar Jehobah kuma muna amfani da abin da ta ce, muna ƙaunar ’yan’uwanmu. (1 Yahaya 3:15) Duk da cewa duniya ta ƙi mu, hakan bai sa mun mance da umurnan Allah ba. Muna ci gaba da yin nufinsa a cikin haɗin kai da yan’uwanmu, yayin da muke jiran lokacin da za mu bauta wa Jehobah cikin farin ciki har abada.—Zabura 119:93.
5. Ta yaya ne Sarki Asa ya nemi Jehobah?
5 Sa’ad da muke nuna yadda muka ba da kanmu ga Jehobah, muna iya yin addu’a kamar mai zabura: “Ni naka ne, ka cece ni! Na yi ƙoƙari in yi biyayya da umarnanka.” (Zabura 119:94) Sarki Asa ya nemi Allah kuma ya halaka ’yan ridda a Yahuda. A shekara ta goma sha biyar ta sarautar Asa, a wata babban taro (shekara ta 963 K.Z.), mutanen Yahuda “suka ƙulla alkawari cewa za su nemi Ubangiji Allah.” Allah ya bari “sun kuwa same shi,” kuma “ya hutasshe su a kowane al’amari.” (2 Tarihi 15:10-15) Wannan misalin ya kamata ya ƙarfafa duk wanda ya riga ya bar ikilisiyar Kirista ya sake neman Allah. Zai albarkaci waɗanda suka dawo kuma suka soma tarayya da mutanensa kuma zai kāre su.
6. Wane tafarki ne zai kāre mu daga lahani ta ruhaniya?
6 Maganar Jehobah tana ba mu hikimar da za ta iya kāre mu daga lahani ta ruhaniya. (Zabura 119:97-104) Dokokin Allah suna sa mu kasance da hikima fiye da maƙiyanmu. Kiyaye koyarwarsa na ba mu fahimi, kuma ‘yin biyayya ga umarninsa ya sa mun fi tsofaffi hikima.’ (Zabura 119:98-100) Idan ka’idodin Jehobah ‘suna da zaƙi a dasashenmu har sun fi zuma zaƙi,’ za mu ƙi kuma za mu kauce wa “halin da yake ba daidai ba.” (Zabura 119:103, 104) Hakan zai kāre mu daga lahani na ruhaniya sa’ad da muka sadu da masu girman kai, masu zafin hali, da mutane marasa ibada, a wannan zamanin ƙarshe.—2 Timoti 3:1-5.
Fitila Wadda Za ta Bi da Mu
7, 8. Cikin jituwa da Zabura 119:105, menene muke bukatar mu yi?
7 Maganar Allah ita ce tushen fitila ta ruhaniya marar ƙarewa. (Zabura 119:105-112) Idan mu Kiristoci ne shafaffu ko kuwa abokanansu “waɗansu tumaki,” mu ce: “Maganarka fitila ce wadda za ta bi da ni, haske ne kuma a kan hanyata.” (Yahaya 10:16; Zabura 119:105) Maganar Allah kamar fitila take da ke haskaka hanyarmu, saboda kada mu yi tuntuɓe ko mu faɗi a ruhaniya. (Karin Magana 6:23) Dole ne mu da kanmu mu ƙyale maganar Jehobah ta zama fitila wadda za ta bi da mu.
8 Dole ne mu kasance da irin aniyar marubucin Zabura ta 119. Ya ƙudurta cewa ba zai ƙyale umurnin Allah ba. Ya ce: “Zan cika muhimmin alkawarina, in yi biyayya da koyarwarka [Jehobah] mai adalci.” (Zabura 119:106) Ya kamata mu ga muhimmancin yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da kuma halartan taron Kirista.
9, 10. Ta yaya muka sani cewa waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah suna iya ‘yin rashin biyayya ga umarninsa,’ amma ta yaya za mu iya kauce wa hakan?
9 Mai zabura ‘bai yi rashin biyayya da umarnin Allah ba,’ amma hakan na iya faruwa ga mutanen da suka keɓe kansu ga Jehobah. (Zabura 119:110) Sarki Sulemanu ya yi rashin biyayya, duk da cewa shi ɗan al’umma ne da aka keɓe wa Jehobah kuma a dā ya yi aiki cikin jituwa da hikima daga Allah. “Baren mata suka sa shi ya yi zunubi” ta wajen rinjayar shi ya bauta wa allolin ƙarya.—Nehemiya 13:26; 1 Sarakuna 11:1-6.
10 Shaiɗan wanda shi ne “mai-farauta,” ya ƙafa tarkuna masu yawa. (Zabura 91:3 Litafi Mai-Tsarki) Alal misali, wanda muke yin bauta tare da shi a dā zai so ya janye mu daga hanyar haske ta ruhaniya zuwa cikin duhu na ’yan ridda. A cikin Kiristocin da suke a Tayatira, akwai wata ‘mata Yezebel,’ wataƙila rukunin matan da suke koya wa wasu su bauta wa gumaka kuma su yi zina. Yesu bai yarda da irin wannan muguntar ba kuma mu ma ya kamata mu yi haka. (Wahayin Yahaya 2:18-22; Yahuza 3, 4) Bari mu yi addu’a ga Jehobah ya taimaka mana saboda kada mu kauce wa umurninsa amma mu ci gaba da kasancewa a cikin hurarren haskensa.—Zabura 119:111, 112.
Maganar Allah Tana Kiyaye Mu
11. In ji Zabura 119:119, yaya Allah yake ɗaukan mugaye?
11 Allah zai ci gaba da kiyaye mu idan ba mu fanɗare daga umurninsa ba. (Zabura 119:113-120) Ba ma yarda da ‘marasa aminci,’ kamar yadda Yesu ya ƙi waɗanda suka ce su Kiristoci ne amma “tsakatsaki ne” a yau. (Zabura 119:113; Wahayin Yahaya 3:16) Domin muna bauta wa Jehobah da dukan zuciyarmu, ‘shi ne ke kāre mu’ kuma zai kiyaye mu. Zai ‘rabu da dukan waɗanda ba sa biyayya da dokokinsa’ domin dabarunsu da yaudara. (Zabura 119:114, 117, 118; Karin Magana 3:32) Ya ɗauki irin waɗannan mugayen a matsayin datti da aka cire daga azurfa da zinariya. (Zabura 119:119; Karin Magana 17:3) Domin ba ma so mu kasance a cikin mugayen da za a halaka, bari mu ci gaba da ƙaunar tunasarwar Allah.
12. Me ya sa tsoron Jehobah ke da muhimmanci?
12 “Saboda kai [Jehobah], nake jin tsoro,” in ji mai zabura. (Zabura 119:120) Muna bukatar jin tsoron Allah da ƙin abubuwa da ya ƙi, idan muna so ya kiyaye mu bayinsa. Tsoron Jehobah ya sa Ayuba ya yi rayuwa mai aminci. (Ayuba 1:1; 23:15) Tsoronmu na ibada zai iya taimaka mana mu nace wa tafarkin da Allah ke so duk da matsalar da za mu fuskanta. Domin mu jimre, muna bukatar addu’a da aka yi cikin bangaskiya.—Yakubu 5:15.
Ka Yi Addu’a da Bangaskiya
13-15. (a) Me ya sa ya kamata mu gaskata cewa za a amsa addu’o’inmu? (b) Menene ke iya faruwa idan ba mu san abin da za mu ce ba a addu’a? (c) Ka kwatanta yadda Zabura 119:121-128 za su iya jituwa da ‘nishe-nishenmu da ba su hurtuwa’ a addu’a.
13 Muna iya yin addu’a a cikin bangaskiya cewa Allah zai aikata a madadinmu. (Zabura 119:121-128) Kamar mai zabura, muna da tabbacin cewa za a amsa addu’armu. Me ya sa? Domin muna ƙaunar dokokin Allah “fiye da zinariya, fiye da zinariya tsantsa.” Bugu da ƙari, ‘muna bin dukan koyarwansa.’—Zabura 119:127, 128.
14 Jehobah yana jin roƙonmu domin muna yin addu’a cikin bangaskiya kuma muna bin umurninsa. (Zabura 65:2) Idan muka fuskanci wahaloli masu yawa har ba mu san abin da za mu ce a addu’a ba fa? “Ruhu kansa yana mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.” (Romawa 8:26, 27) A irin waɗannan lokatai, Allah na karɓan kalamai da ke cikin Kalmarsa a matsayin addu’a game da bukatunmu.
15 Nassosi na cike da addu’a da tunani da za su jitu da “nishe-nishen da ba su hurtuwa.” Alal misali, yi la’akari da Zabura 119:121-128. Yadda abubuwa suke a ciki na iya dacewa da yanayinmu. Alal misali, idan muna tsoron kada a zambace mu, muna iya neman taimako daga Allah kamar yadda mai zabura ya yi. (Ayoyi 121-123) Idan muna so mu yanke shawara mai wuya fa? Muna iya yin addu’a cewa ruhun Jehobah ya taimaka mana mu tuna kuma mu yi amfani da tunasarwarsa. (Ayoyi 124, 125) Ko da yake mun ƙi “dukan mugayen al’amura,” muna iya roƙon Allah ya taimaka mana domin kada mu fāɗa cikin gwaji kuma mu taka dokarsa. (Ayoyi 126-128) Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, wurare masu taimakawa, suna iya faɗowa a cikin zuciyarmu sa’ad da muke roƙon Jehobah cikin addu’a.
Tunasarwar Jehobah Tana Taimakawa
16, 17. (a) Me ya sa muke bukatar tunasarwar Allah, kuma yaya ya kamata mu ɗauke su? (b) Yaya mutane suke iya ɗaukanmu, amma menene ya fi muhimmanci?
16 Idan muna so Allah ya ji addu’armu kuma muna so mu more tagomashin Allah, dole ne mu kiyaye tunasarwarsa. (Zabura 119:129-136) Tun da yake muna yawan mantuwa, muna bukatar tunasarwar Jehobah da za su tuna mana umurninsa da kuma dokokinsa. Hakika, muna godiya ga haske na ruhaniya da ke haskaka sabuwar fahimta ta maganar Allah. (Zabura 119:129, 130) Kuma muna godiya cewa Jehobah ya ‘sa mana albarka da kasancewarsa da mu’ ko da yake ‘hawaye suna malalowa kamar kogi’ daga idanunmu domin mutane suna taka dokarsa.—Zabura 119:135, 136; Littafin Ƙidaya 6:25.
17 Muna da tabbacin cewa Jehobah zai ci gaba da nuna mana tagomashi idan muka saurari amintaccen tunasarwarsa. (Zabura 119:137-144) Da yake mu bayin Jehobah ne, mun yarda cewa yana da ikon ba mu tunasarwarsa masu aminci kuma ya kafa mana su a matsayin dokokin da dole ne mu bi su. (Zabura 119:138) Tun da yake mai zabura yana yin biyayya ga dokokin Allah, me ya sa ya ce: “Ni ba kome ba ne, rainanne ne”? (Zabura 119:141) Babu shakka, yana nuni ne ga yadda maƙiyansa suka ɗauke shi. Idan muka manne wa mizanai na aminci, mutane suna iya raina mu. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, Jehobah yana nuna mana tagomashi domin muna bin tunasarwarsa masu aminci.
Kwanciyar Hankali da Zaman Lafiya
18, 19. Wane sakamako ne za mu samu idan muka bi tunasarwar Allah?
18 Bin tunasarwar Allah na jawo mu kusa da shi. (Zabura 119:145-152) Domin muna bin tunasarwar Jehobah, mun sami gaba gaɗin yin kira a gare shi da dukan zuciyarmu, kuma muna da tabbacin cewa zai ji mu. Muna iya tashi “kafin fitowar rana” mu nemi taimako a wurinsa. Wannan lokaci ne mai kyau na yin addu’a! (Zabura 119:145-147) Allah na kusa da mu domin mun ƙi ƙazaman halaye, kuma domin mun ɗauki maganarsa gaskiya ce kamar yadda Yesu ya yi. (Zabura 119:150, 151; Yahaya 17:17) Dangantakarmu da Jehobah na kāre mu daga wannan duniya da ta wahala kuma za ta kāre mu a yaƙinsa mai girma a Armagedon.—Wahayin Yahaya 7:9, 14; 16:13-16.
19 Domin muna daraja maganar Allah, muna more kwanciyar rai ta gaske. (Zabura 119:153-160) Ba kamar mugayen da suka ‘fasa yin biyayya da dokokin Jehobah ba.’ Muna ƙaunar umurnan Allah, shi ya sa muka sami kwanciyar rai bisa ga madawwamiyar ƙaunarsa. (Zabura 119:157-159) Tunasarwar Jehobah na motsa mu mu tuna abubuwan da yake bukata a gare mu a wasu yanayi. A wata sassa, umurnan Allah na yi mana ja-gora, kuma mun yarda da ’yancin da Mahaliccinmu ke da shi na yi mana ja-gora. Sanin cewa ‘cibiyar dokar Allah gaskiya ce,’ kuma ba ma iya kiyaye takawarmu da kanmu, ya sa mun yarda da ja-gorar Allah.—Zabura 119:160; Irmiya 10:23.
20. Me ya sa muke da “cikakken zaman lafiya”?
20 Ƙaunar da muke yi wa dokar Jehobah na ba mu salama a yalwace. (Zabura 119:161-168) Tsanantawa ba zai iya ɗauke “salamar Allah” da muke da ita ba. (Filibiyawa 4:6, 7) Saboda irin ƙaunar da muke yi wa shari’un Jehobah masu adalci, muna gode masa “sau bakwai” a kowace rana. (Zabura 119:161-164) “Waɗanda ke ƙaunar dokarka sun sami cikakken zaman lafiya,” in ji mai zabura, “ba wani abin da zai sa su fāɗi.” (Zabura 119:165) Idan kowanenmu ɗai-ɗai yana ƙauna kuma yana bin dokar Jehobah, ba za mu yi tuntuɓe a ruhaniya ba domin abin da wani ya yi ko kuwa domin wasu al’amura.
21. Waɗanne misalai na Nassi ne suka nuna cewa bai kamata mu yi tuntuɓe ba idan matsaloli suka taso a cikin ikilisiya?
21 Mutane da yawa da labarinsu ke cikin Littafi Mai Tsarki, ba su ƙyale wani abu ya zame musu abin tuntuɓe ba. Alal misali, wani Kirista mai suna Gayus bai yi tuntuɓe ba, amma ya ci gaba da “bin gaskiya” duk da halin rashin ibada na Diyotarifis. (3 Yahaya 1-3, 9, 10) Wataƙila domin matsalar da ta taso tsakanin Afodiya da Sintiki, Bulus ya gargaɗe su “su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.” Hakika, an taimaka musu su magance matsalar kuma sun ci gaba da bauta wa Jehobah da aminci. (Filibiyawa 4:2, 3) Idan matsaloli suka taso a cikin ikilisiya, kada mu bari hakan ya sa mu tuntuɓe. Bari mu mai da hankali ga bin umurnan Jehobah, muna tunawa cewa ‘yana ganin dukan abin da muke yi.’ (Zabura 119:168; Karin Magana 15:3) Ta haka, babu abin da zai janye mana ‘kwanciyar ranmu.’
22. (a) Wane gata ne za mu more idan muka yi wa Allah biyayya? (b) Yaya ya kamata mu ɗauki waɗanda suka bar ikilisiyar Kirista?
22 Idan muka ci gaba da yin biyayya ga Jehobah, za mu sami gatar yin yabonsa a kowane lokaci. (Zabura 119:169-176) Ta yin rayuwa da ta jitu da ka’idodin Allah, zai sa mu mori kāriya ta ruhaniya, kuma ‘za mu yabi Jehobah kullayaumin.’ (Zabura 119:169-171, 174) Wannan shi ne gata mafi muhimmanci da za mu iya samu a wannan zamani na ƙarshe. Mai zabura yana son ya rayu kuma ya yabi Jehobah, amma a wasu hanyoyi da ba mu sani ba, yana “kai da kawowa kamar ɓatacciyar tunkiya.” (Zabura 119:175, 176) Mutanen da suka bar ikilisiyar Kirista wataƙila har ila suna ƙaunar Allah kuma suna so su yabe shi. Saboda haka, bari mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka musu domin su sake samun kāriya ta ruhaniya, kuma su sami farin ciki na yabon Jehobah tare da mutanensa.—Ibraniyawa 13:15; 1 Bitrus 5:6, 7.
Haske na Dindindin ga Hanyarmu
23, 24. Waɗanne amfani ne ka samu a cikin Zabura ta 119?
23 Zabura ta 119 tana iya taimaka mana a hanyoyi masu yawa. Alal misali, tana iya sa mu dogara ga Allah, domin ta nuna cewa ana iya samun farin ciki ne daga bin “dokar Ubangiji.” (Zabura 119:1) Mai zabura ya tuna mana cewa ‘cibiyar dokar Allah gaskiya ce.’ (Zabura 119:160) Ya kamata hakan ya sa mu ƙara nuna godiya ga dukan rubutacciyar Maganar Allah. Yin bimbini a kan Zabura ta 119, ya kamata ya motsa mu mu yi nazarin Nassosi sosai. Mai zabura ya roƙi Allah a kai a kai: “Ka koya mini dokokinka.” (Zabura 119:12, 68, 135) Ya kuma yi roƙo: “Ka ba ni hikima da ilimi domin ina dogara ga umarnanka.” (Zabura 119:66) Ya kamata mu ma mu yi addu’a kamar haka.
24 Koyarwar Jehobah tana sa mu yi dangantaka ta kud da kud da shi. Sau da yawa, mai zabura ya kira kansa bawan Allah. Shi ya sa ya yi wa Jehobah magana da waɗannan kalamai masu taɓa zuciya: “Ni naka ne.” (Zabura 119:17, 65, 94, 122, 125; Romawa 14:8) Gata ce mai girma mu bauta kuma mu yabi Jehobah a matsayin Shaidunsa! (Zabura 119:7) Kana bauta wa Jehobah da farin ciki a matsayin mai shelar Mulki kuwa? Idan haka ne, ka tabbata cewa Jehobah zai ci gaba da taimakonka kuma zai albarkace ka a wannan aiki na gata, idan ka dogara ga maganarsa kuma ka ƙyale ta ta haskaka hanyarka a kowane lokaci.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa ya kamata mu ƙaunaci maganar Allah?
• Ta yaya maganar Allah ke kiyaye mu?
• A waɗanne hanyoyi ne tunasarwar Jehobah ke taimaka mana?
• Me ya sa mutanen Jehobah ke da kwanciyar rai da salama?
[Hoto a shafi na 10]
Maganar Allah tushe ce ta haske na ruhaniya
[Hoto a shafi na 11]
Idan muka ƙaunaci tunasarwar Jehobah, ba zai taɓa ɗaukanmu marasa amfani ba
[Hotuna a shafi na 12]
Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, akwai wuraren da za su faɗo mana a zuciya sa’ad da muke addu’a