Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 5/1 pp. 4-9
  • Ka Dogara Ga Maganar Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Dogara Ga Maganar Jehobah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka yi Biyayya ga Maganar Allah Ka yi Farin Ciki
  • Maganar Jehobah Tana Tsabtace Mu
  • Maganar Allah Tana Sa Mu Kasance da Aminci
  • Maganar Jehobah Tana Ba da Gaba Gaɗi
  • Maganar Allah Tana Sanyaya Mana Zuciya
  • Ka Yi Godiya Domin Maganar Jehobah
  • Ka Ba da Gaskiya ga Maganar Allah
  • Ka Dogara ga Jehobah a Kowane Lokaci
  • Bari Maganar Allah Ta Haskaka Hanyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ka Yi “Tafiya Cikin Shari’ar Ubangiji”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Kana Ƙaunar Ƙa’idodin Jehovah Da Zuciya Ɗaya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • “Ina Ƙaunar Shari’arka Ba Misali!”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 5/1 pp. 4-9

Ka Dogara Ga Maganar Jehobah

“Na dogara ga maganarka.”—Zabura 119:42.

1. Menene za ka iya cewa game da halin marubucin Zabura 119?

MARUBUCIN Zabura 119 yana ƙaunar maganar Jehobah sosai. Wataƙila Hezekiya ɗan sarkin Yahuza ne. Abubuwan da aka furta a cikin wannan hurarriyar waƙar sun yi daidai da halin Hezekiya, wanda ya “manne wa Ubangiji” sa’ad da yake sarauta a Yahuza. (2 Sarakuna 18:3-7) Abu ɗaya shi ne: Marubucin ya san talaucinsa na ruhaniya.—Matiyu 5:3.

2. Menene jigon Zabura 119, kuma yaya aka tsara wannan waƙar?

2 Abu na musamman game da Zabura 119 shi ne daraja maganar Allah ko saƙonsa.a Wataƙila domin yana taimakawa wajen tuni, marubucin wannan waƙar ya rubuta ta a cikin haruffa. An rubuta ayoyinta 176 ne a haruffan Ibrananci. A Ibrananci na asali, wannan zabura tana da baiti 22, kowane baiti yana da layi 8 da suka fara da kalamai iri ɗaya. Wannan zabura ta kira maganar Allah, doka, umurnai, hanyoyi, da kuma ƙa’idodi. A cikin wannan talifin da na gaba, za a tattauna Zabura ta 119. Idan muka yi tunani a kan labaran da suka shafi bayin Jehobah na dā da na zamani, hakan zai ƙara godiyarmu ga wannan hurarriyar waƙa kuma zai ƙara godiyarmu ga rubutacciyar Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki.

Ka yi Biyayya ga Maganar Allah Ka yi Farin Ciki

3. Ka bayyana kuma ka ba da misalin abin da zama marasa laifi ke nufi.

3 Farin ciki na gaskiya ya dangana ne a kan yin biyayyarmu ga dokar Allah. (Zabura 119:1-8) Idan muka yi haka, Jehobah zai ɗauke mu ‘marasa laifi cikin zamanmu.’ (Zabura 119:1) Zama marasa laifi ba wai yana nufin cewa mu kamilai ba ne, amma yana nufi ne cewa muna ƙoƙarin yin nufin Jehobah Allah. Nuhu “salihi ne kuma cikin zamaninsa” mutum ne wanda “ya yi tafiya tare da Allah.” Wannan amintacce, uban iyali da iyalansa sun tsira daga Rigyawa domin ya bi tafarkin da Jehobah ya tsara. (Farawa 6:9; 1 Bitrus 3:20) Hakazalika, tsirarmu daga ƙarshen wannan duniyar ta dangana ne a kan bin ‘dokokin’ Allah, wanda ke nufin yin nufinsa.—Zabura 119:4.

4. Farin cikinmu da nasara sun dangana ne a kan me?

4 Jehobah ba zai taɓa ƙyale mu ba idan ‘muka yabe shi da tsattsarkar zuciya. Kuma muka ci gaba da yin biyayya ga dokokinsa.’ (Zabura 119:7, 8) Allah bai yi watsi da shugaban Isra’ila, Joshuwa ba, wanda ya bi shawarar karanta littafin dokoki ‘dare da rana domin ya kiyaye kuma ya aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki.’ Hakan ya taimaka masa ya yi nasara kuma ya aikata da hikima. (Joshuwa 1:8) Har ƙarshen rayuwarsa, Joshuwa ya ci gaba da yabon Allah kuma ya tuna wa Isra’ilawa cewa: “Ku duka kuwa, a zukatanku da rayukanku, kun sani dukan abubuwan alheri da Ubangiji Allahnku ya alkawarta muku sun tabbata, ba ɗayan da bai tabbata ba.” (Joshuwa 23:14) Kamar Joshuwa da kuma marubucin Zabura ta 119, muna iya samun farin cikin ta yaba wa Jehobah da kuma amincewa da kalmarsa.

Maganar Jehobah Tana Tsabtace Mu

5. (a) Ka bayyana yadda za a iya kasancewa da tsabta na ruhaniya. (b) Wane taimako ne matashi da ya yi zunubi mai tsanani zai samu?

5 Muna iya kasancewa da tsabta a ruhaniya idan muka bi abin da maganar Allah ta ce. (Zabura 119:9-16) Wannan haka yake, har ma idan iyayenmu ba su kafa misali mai kyau ba. Ko da yake baban Hezekiya mai bautar gunki ne, Hezekiya ya ‘kiyaye ransa da tsarki’ daga rinjayar arnanci. Idan matashi wanda yake bauta wa Allah a yau ya yi zunubi mai tsanani. Tuba, addu’a, da kuma taimako na iyaye, da taimako na ƙauna daga dattawa Kirista zai iya taimaka masa ya zama kamar Hezekiya kuma ya “kiyaye ransa da tsarki.”—Yakubu 5:13-15.

6. Waɗanne mata ne suka ‘kiyaye ransu da tsarki kuma suka yi biyayya ga umurnin Allah’?

6 Ko da yake sun rayu kafin a rubuta Zabura ta 119, Rahab da Rut sun ‘kiyaye ransu da tsarki.’ Rahab karuwa ce a Ka’anan, amma duk da haka, ta zama sananniya domin bangaskiyarta na mai bauta wa Jehobah. (Ibraniyawa 11:30, 31) Rut Bamowabiya ta yi watsi da allolinta, ta fara bauta wa Jehobah kuma ta bi Dokar da ya kafa wa Isra’ilawa. (Rut 1:14-17; 4:9-13) Waɗannan mata da ba Ba’isra’ilawa ba sun ‘yi biyayya da umurnin Allah’ kuma sun sami gatar zama kakannin Yesu Kristi.—Matiyu 1:1, 4-6.

7. Ta yaya Daniyel da Ibraniyawa uku suka kafa misali mai kyau na kasancewa da tsabta na ruhaniya?

7 “Zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa,” amma matasa na iya bin tafarki mai tsarki, duk da cewa wannan lalatacciyar duniya tana hannun Shaiɗan. (Farawa 8:21; 1 Yahaya 5:19) Duk da cewa suna zaman bauta a Babila, Daniyel da Ibraniyawa matasa uku sun ‘kiyaye ransu da tsarki kuma sun yi biyayya ga umurnin Allah.’ Alal misali, sun ƙi su ƙazantar da kansu da “abinci irin na sarki.” (Daniyel 1:6-10) Babiloniyawa suna cin haramtaccen dabba, wadda Dokar Musa ta hana. (Littafin Firistoci 11:1-31; 20:24-26) Ba sa yanka dabba, kuma dokar Allah ta haramta hakan. (Farawa 9:3, 4) Ba abin mamaki ba ne da Ibraniyawa huɗun suka ƙi cin abincin sarki! Waɗannan matasa masu tsoron Allah sun riƙe tsabta na ruhaniya, da haka, sun kafa misali mai kyau.

Maganar Allah Tana Sa Mu Kasance da Aminci

8. Wane irin hali da sani muke bukata idan muna so mu fahimci dokar Allah kuma mu yi amfani da ita?

8 Ƙaunar maganar Allah ita ce muhimmiyar aba da ke taimaka mana mu kasance da aminci ga Jehobah. (Zabura 119:17-24) Idan kamar marubucin wannan waƙar da aka hure muna so mu fahimci abubuwa masu “banmamaki” na ‘shari’ar’ Allah, za mu so ‘sanin hukuncin Jehobah’ kuma ‘umurnansa za su faranta mana rai’ a kowane lokaci. (Zabura 119:18, 20, 24) Ko ba mu daɗe da keɓe kanmu ga Jehobah ba, muna “marmarin shan madara marar gami mai ruhu,” kuwa? (1 Bitrus 2:1, 2) Muna bukatar mu fahimci muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki saboda ya zame mana da sauƙi mu fahimci dokar Allah kuma mu yi amfani da ita.

9. Me ya kamata mu yi sa’ad da aka samu saɓani tsakanin dokar Allah da bukatun mutane?

9 Wataƙila muna ƙaunar tunasarwar Allah, amma idan “sarakuna” suka kushe mu don wani dalili fa? (Zabura 119:23, 24) A yau, mutanen da suke da iko sukan yi ƙoƙari su matsa mana mu ɗora dokar mutum bisa dokar Allah. Idan aka sami saɓani tsakanin bukatun mutane da nufin Allah, menene za mu yi? Ƙaunar da muke yi wa maganar Allah za ta taimaka mana mu kasance da aminci ga Jehobah. Kamar manzannin Yesu Kristi da aka tsananta wa, mu ma za mu ce: “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.”—Ayyukan Manzanni 5:29.

10, 11. Ka kwatanta yadda za mu iya riƙe aminci ga Jehobah sa’ad da muka fuskanci jaraba na ƙwarai.

10 Muna iya riƙe amincinmu ga Jehobah har ma sa’ad da muka fuskanci jaraba. (Zabura 119:25-32) Idan muna so mu sami nasara a riƙe amincinmu ga Allah, dole ne mu yi na’am da abin da aka koya mana kuma mu yi addu’a sosai domin umurninsa. Kuma dole ne mu zaɓi tafarkin “biyayya.”—Zabura 119:26, 30.

11 Hezekiya wanda wataƙila shi ne marubucin Zabura ta 119, ya zaɓi tafarkin “biyayya.” Ya yi hakan ne duk da cewa addinan ƙarya sun kewaye shi, kuma wataƙila ’yan fada sun yi masa ba’a. Kuma ƙila ransa ya ‘ɓaci’ saboda wannan yanayi. (Zabura 119:28) Hezekiya sarki ne nagari, kuma ya dogara ga Allah, ya kuma aikata “abin da ke mai kyau a gaban Ubangiji.” (2 Sarakuna 18:1-5) Idan muka dogara ga Allah, za mu iya jimre wa jaraba kuma za mu riƙe amincinmu.—Yakubu 1:5-8.

Maganar Jehobah Tana Ba da Gaba Gaɗi

12. Ta yaya ne za mu iya yin amfani da Zabura 119:36, 37?

12 Bin ja-gorancin maganar Allah tana ba mu gaba gaɗin da muke bukata domin mu jimre wa jaraba na rayuwa. (Zabura 119:33-40) Muna biɗar umurnin Jehobah da tawali’u saboda mu riƙe dokarsa “da zuciya ɗaya.” (Zabura 119:33, 34) Kamar mai zabura, mu riƙa roƙon Allah: “Ka sa ni in so yin biyayya da ka’idodinka, fiye da samun dukiya,” wato “dukiya ta hanyar ha’inci.” (Zabura 119:36) Kamar manzo Bulus, mu riƙa “tafiyar da al’amuranmu da halin kirki.” (Ibraniyawa 13:18) Idan shugaban aikinmu yana so mu yi wani abu na rashin gaskiya, dole ne mu yi gaba gaɗi mu bi ja-gorar Allah, kuma zai albarkaci irin wannan tafarkin a kowane lokaci. Hakika, yana taimaka mana mu sarrafa duk wani mugun tunani. Saboda haka, bari mu yi addu’a: “Ka kiyaye ni daga mai da hankali ga abin da yake marar amfani.” (Zabura 119:37) Kada mu so wani abu marar amfani da Allah ya ƙi. (Zabura 97:10) Ban da waɗannan, hakan kuma yana motsa mu mu ƙi hotunan batsa da kuma ayyukan sihiri.—1 Korantiyawa 6:9, 10; Wahayin Yahaya 21:8.

13. Ta yaya ne almajiran Yesu da aka tsananta wa suka sami ƙarfin zuciya na yin shaida da gaba gaɗi?

13 Cikakken sani na maganar Allah na ba mu tabbacin yin shaida da gaba gaɗi. (Zabura 119:41-48) Muna bukatar gaba gaɗi domin mu ‘amsa wa waɗanda ke cin mutuncinmu.’ (Zabura 119:42) A wasu lokatai, muna iya zama kamar almajiran Yesu da suka yi addu’a sa’ad da aka tsananta musu: “Ya Mamallaki . . . ka yi wa bayinka baiwar yin maganarka da iyakar ƙarfin hali.” Menene sakamakon haka? “Sai duk aka cika su da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta faɗar maganar Allah [da] gabagaɗi.” Ubangiji mai ikon mallaka shi ne yake ba mu ƙarfin zuciya na faɗin maganarsa da gaba daɗi.—Ayyukan Manzanni 4:24-31.

14. Menene ke taimaka mana mu ba da shaida da gaba gaɗi kamar yadda Bulus ya yi?

14 Idan muka ƙaunaci ‘saƙon Allah na gaskiya’ kuma muka yi ‘biyayya ga dokarsa a kowane lokaci,’ za mu sami gaba gaɗin yin shaida ba za mu ji tsoron jin kunya ba. (Zabura 119:43, 44) Yin nazarin rubutacciyar maganar Allah da ƙwazo zai taimaka mana mu ‘hurta umurninsa ga sarakuna.’ (Zabura 119:46) Addu’a da kuma ruhun Jehobah za su taimaka mana mu faɗi abin da ya dace a hanyar da ta dace. (Matiyu 10:16-20; Kolosiyawa 4:6) Bulus ya gaya wa masarauta na ƙarni na farko ƙa’idodin Allah da gaba gaɗi. Alal misali, ya yi wa Gwamnan Roma Filikus, shaida, wanda “ya kuwa saurare shi kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu.” (Ayyukan Manzanni 24:24, 25) Bulus ya kuma ba da shaida a gaban Festas da Sarki Agaribas. (Ayyukan Manzanni 25:22–26:32) Da goyon bayan Jehobah, mu ma muna iya zama shaidu masu gaba gaɗi, waɗanda ba sa “jin kunyar bishara.”—Romawa 1:16.

Maganar Allah Tana Sanyaya Mana Zuciya

15. Ta yaya ne Kalmar Allah za ta iya ta’azantar da mu sa’ad da wasu suka raina mu?

15 Maganar Jehobah tana ba da tabbatacciyar ta’aziyya. (Zabura 119:49-56) Akwai lokatai na musamman da muke bukatar ta’aziyya. Ko da yake muna magana da gaba gaɗi a matsayin Shaidun Jehobah, “masu girman kai,” waɗanda suke nuna girman kai ga Allah a wasu lokatai ‘suna raina mu.’ (Zabura 119:51) Sa’ad da muke yin addu’a, muna iya tunawa da wani abu mai kyau da aka ambata a cikin Kalmar Allah, kuma hakan, ‘za su ta’azantar da mu.’ (Zabura 119:52) Sa’ad da muke yin addu’a, muna iya tunawa da wata doka ta Nassi ko kuwa mizani da za ya ta’azantar da mu kuma ya ba mu gaba gaɗin da muke bukata a yanayi mai wuya.

16. Menene mu bayin Allah ba mu yi ba duk da tsanantawa?

16 Isra’ilawa masu girman kai sun raina mai zabura—waɗanda suke cikin al’umma da aka keɓe wa Allah. Wannan abin kunya ne! Akasarin haka, bari mu ƙudurta cewa ba za mu taɓa bijire wa dokar Allah ba. (Zabura 119:51) Duk da tsanantawa daga ’yan Nazi da kuma makamancin su na shekaru da yawa, dubban bayin Allah sun ƙi su bijire wa dokar Allah da kuma mizanansa da ke cikin Kalmarsa. (Yahaya 15:18-21) Yin biyayya ga Jehobah ba tsanantawa ba ne, domin umurnansa kamar waƙoƙi suke masu ta’azantar da mu. (Zabura 119:54; 1 Yahaya 5:3)

Ka Yi Godiya Domin Maganar Jehobah

17. Godiya ga maganar Allah tana motsa mu mu yi menene?

17 Muna nuna godiya ga Maganar Allah ta wajen yin biyayya da ita. (Zabura 119:57-64) Mai zabura ya yi alkawarin ‘yin biyayya da dokokin Jehobah’ har ma ‘a tsakar dare yakan farka, ya yabe Allah saboda hukuncinsa masu adalci.’ Idan muka farka a tsakar dare, wannan lokaci ne mai kyau na yin godiya ga Allah a cikin addu’a! (Zabura 119:57, 62) Godiyarmu ga maganar Allah na motsa mu mu nemi hurarriyar koyarwa kuma ta sa mu ‘mu yi abuta da duk waɗanda suke bauta wa Jehobah’—mutane masu tsoron Allah. (Zabura 119:63, 64) A ina za mu iya samun tarayya mai kyau kamar wannan a duniya?

18. Ta yaya ne Jehobah yake amsa addu’o’inmu sa’ad da ‘mugaye suka ɗaure mu tam da igiyoyi’?

18 Idan muka yi addu’a da dukan zuciyarmu kuma muka roƙi Jehobah cikin tawali’u cewa ya koyar da mu, muna ‘roƙonsa ne’ domin mu more tagomashinsa. Muna bukatar mu yi addu’a sa’ad da ‘mugaye suka ɗaure mu tam da igiyoyi.’ (Zabura 119:58, 61) Jehobah zai iya yanke igiyoyin mugaye kuma ya cece mu saboda wa’azin Mulki da kuma aikin almajirantarwa. (Matiyu 24:14; 28:19, 20) Irin hakan ya faru a kai a kai a ƙasashen da aka hana aikinmu.

Ka Ba da Gaskiya ga Maganar Allah

19, 20. Me ya sa yake da kyau a hori mutum?

19 Ba da gaskiya ga maganar Allah na taimaka mana mu jimre wa azaba kuma mu yi nufinsa. (Zabura 119:65-72) Ko da yake masu girman kai ‘sun faɗi ƙarairayi a kansa,’ mai zabura ya rera: “Horon da aka yi mini ya yi kyau.” (Zabura 119:66, 69, 71) Me ya sa yake da kyau bayin Jehobah su jimre wa azaba?

20 Sa’ad da muka fuskanci azaba, muna yin addu’a ga Jehobah, kuma hakan na jawo mu kusa da shi. Muna iya ƙara ba da lokaci a yin nazarin rubutacciyar Maganar Allah kuma mu yi ƙoƙarin yin amfani da ita. Hakan na kawo rayuwa mai daɗi. Amma idan muka nuna halin da bai dace ba domin azaba, kamar rashin haƙuri da fahariya fa? Da taimakon addu’a da kuma Maganar Allah da ruhunsa, za mu iya mu sha kan irin wannan kasawa kuma mu “ɗau sabon halin.” (Kolosiyawa 3:9-14) Bugu da ƙari, bangaskiyarmu tana ƙarfafa sa’ad da muka jimre wa wahala. (1 Bitrus 1:6, 7) Bulus ya amfana daga wahalolin da ya sha domin sun sa ya ƙara dogara ga Jehobah. (2 Korantiyawa 1:8-10) Muna ƙyale wahala ta ba da sakamako mai kyau a kanmu kuwa?

Ka Dogara ga Jehobah a Kowane Lokaci

21. Menene zai faru sa’ad da Allah ya kunyatar da masu girmankai?

21 Maganar Allah ta ba mu tabbataccen dalilin dogara ga Jehobah. (Zabura 119:73-80) Idan muka dogara ga Mahaliccinmu da gaske, ba za mu taɓa jin kunya ba. Domin abubuwan da wasu suka yi mana, muna bukatar ta’aziyya kuma mukan ji kamar mu yi addu’a: “Ka kunyatar da masu girmankai.” (Zabura 119:76-78) Sa’ad da Jehobah ya kunyatar da su, zai fallasa hanyoyinsu na mugunta kuma hakan zai tsarkake sunansa. Muna da tabbacin cewa masu tsananta wa mutanen Allah ba su sami amfanin komi ba. Alal misali, ba su taɓa, kuma ba za su taɓa halaka Shaidun Jehobah waɗanda suka dogara ga Allah da zuciyar ɗaya ba.—Karin Magana 3:5, 6.

22. A wane azanci ne mai zabura ya zama “kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita”?

22 Maganar Allah tana ƙarfafa dogarar da muka yi masa sa’ad da aka tsananta mana. (Zabura 119:81-88) Domin masu girmankai na tsananta masa, mai zabura ya zama “kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita.” (Zabura 119:83, 86) A lokacin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, ana amfani da salkuna domin a zuba ruwa, inabi, da sauran abin sha. Sa’ad da aka ƙi yin amfani da ita, salkar na iya yin yaushi idan aka ajiye ta a ɗakin da ke cike da hayaki. Wahala ko kuwa tsanani ta taɓa sa ka ka ji “kamar salkar ruwan inabi wanda aka jefar da ita”? Idan haka ne, to, ka dogara ga Jehobah kuma ka yi addu’a: “Saboda madawwamiyar ƙaunarka, ka yi mini alheri, domin in yi biyayya da dokokinka.”—Zabura 119:88.

23. Menene muka tattauna a binciken da muka yi na Zabura 119:1-88 kuma me ya kamata mu tambayi kanmu yayin da muke sa ran yin nazarin Zabura 119:89-176?

23 Abubuwa da muka tattauna a rabin Zabura ta 119, sun nuna cewa Jehobah na nuna ƙauna ta alheri ga bayinsa domin sun dogara ga kalmarsa kuma suna ƙaunar dokarsa, umurnansa, hanyoyinsa, da kuma ka’idodinsa. (Zabura 119:16, 47, 64, 70, 77, 88) Yana so waɗanda suka ba da ransu a gare shi su yi biyayya da umarnansa. (Zabura 119:9, 17, 41, 42) Yayin da kake sauraron yin nazarin sauran wannan zabura mai wartsakewa, kana iya tambayar kanka, ‘Ina ƙyale maganar Jehobah ta haskaka hanyata kuwa?’

[Hasiya]

a A nan ana nuni ne ga saƙon Jehobah, ba dukan abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki—Kalmar Allah ba.

Yaya Za Ka Amsa?

• Farin ciki na gaskiya ya dangana a kan menene?

• Ta yaya ne maganar Jehobah take tsarkake mu a ruhaniya?

• A waɗanne hanyoyi ne maganar Allah ke ƙarfafa mu da ta’azantar da mu?

• Me ya sa ya kamata mu ba da gaskiya ga Jehobah da kuma maganarsa?

[Hotuna a shafi na 5]

Rut, Rahab, da kuma Ibraniyawa matasa da suke zaman bauta a Babila ‘sun yi biyayya da umarnan Allah’

[Hoto a shafi na 6]

Bulus da gaba gaɗi ‘ya hurta umarnan Allah ga sarakuna’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba