LITTAFI MAI TSARKI YANA GYARA RAYUWAR MUTANE
“Mutane Da Yawa Sun Tsane Ni”
SHEKARAR HAIHUWA: 1978
ƘASAR HAIHUWA: CHILE
TARIHI: MAI ZAFIN HALI DA RASHIN IMANI
RAYUWATA A DĀ:
Na girma a Santiago, babban birnin ƙasar Chile, a unguwar da ake yawan shan ƙwayoyi da aikata laifi kuma ’yan dabā sun cika ko’ina. An kashe mahaifina sa’ad da nake ɗan shekara biyar. Daga nan ne mahaifiyata ta yi zaman dadiro da wani mutum azzalumi. Yakan yi mana dūka a kowane lokaci. Har wa yau ba zan taɓa mantawa da wannan lokacin ba.
Sa’ad da nake girma, wannan mummunan tasirin ya sa na soma yi wa mutane rashin imani. Ina yawan shan giya da sauraron kiɗa da ke da ƙara mai tsanani kuma nakan sha ƙwayoyi a wasu lokatai. Na sha yin faɗa da dillalan ƙwayoyi a kan titi kuma sau da sau sun yi ƙoƙarin kashe ni. Akwai ma lokacin da suka aiki wani ƙwararren mai kisan gilla ya kashe ni, amma na kuɓuce masa kuma ya ji mini rauni kaɗan ne kawai. A wani sa’i kuma wani rukunin dillalan ƙwayoyi sun riƙe bindiga a goshina kuma sun yi ƙoƙarin rataye ni.
A shekara ta 1996, na haɗu da wata mai suna Carolina kuma muka yi aure a shekara ta 1998. Bayan haihuwar ɗanmu na fari, sai na soma damuwa cewa da yake ni mai zafin hali ne, zan wulaƙanta iyalina kamar mahaifina na rana. Saboda haka, na je wani asibiti da ke unguwar don su taimaka mini in daina nuna zafin hali, amma duk jinyar da suka yi mini ta ci tura. Na ci gaba da kasancewa da zafin rai kuma ɗan ƙanƙanin abu yana ɓata mini rai. Wata rana, na yi ƙoƙarin kashe kaina, wai don ina so in daina wulaƙanta iyalina. Abin farin ciki, ban yi nasara ba.
Ko da yake na daɗe ba na gaskata da Allah, amma a wannan lokacin na so in yi imani da shi. Hakan ya sa na soma zuwa wani coci. A wannan lokacin matata tana nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Na tsani Shaidun Jehobah kuma sau da yawa nakan zuba musu ashar. Amma a kowane lokaci suna mini ladabi, maimakon su rama. Hakan ya ba ni mamaki.
Wata rana, matata Carolina ta ce in karanta littafin Zabura 83:18 a nawa Littafi Mai Tsarki. Wannan ayar ta ce sunan Allah Jehobah ne. Na yi mamaki ƙwarai cewa a addinina, na koya game da wani alla ne kawai, ba game da Jehobah ba. Saboda haka, ni ma na soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah a shekara ta 2000.
YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA CANJA RAYUWATA:
Yayin da na ci gaba da koyo game da Jehobah, sai na ga cewa shi Allah ne mai tausayi da kuma gafartawa kuma hakan ya ƙarfafa ni sosai. Alal misali, littafin Fitowa 34:6, 7 ya ce Jehobah “Allah ne cike da juyayi, mai-alheri kuma, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai da gaskiya; yana tsaron jinƙai domin dubbai, yana gafarta laifi da saɓo da zunubi.”
Duk da haka, bai kasance mini da sauƙi in bi abin da nake koya ba. Na tabbatar wa kaina cewa ba zan iya daina kasancewa da zafin hali ba. Amma duk lokacin da na kasa kame kaina, Carolina takan ƙarfafa ni kuma ta tuna mini cewa Jehobah yana ganin ƙoƙarin da nake yi. Yadda ta ƙarfafa ni ya taimake ni in ci gaba da yin ƙoƙari don in faranta wa Jehobah rai, ko da yake nakan ji kamar na yi nisa kuma ba zan iya jin kira ba.
Wata rana, Alejandro wanda yake yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ni ya ce in karanta Galatiyawa 5:22, 23. Ayoyin nan sun nuna cewa ’ya’yan ruhu mai tsarki “ƙauna ne, farinciki, salama, tsawon jimrewa, nasiha, nagarta, aminci, tawali’u, kamewa.” Sai Alejandro ya bayyana mini cewa kasancewa da waɗannan halayen bai dangana ga iyawata ba, amma sai da taimakon ruhu mai tsarki. Hakan ya sa na canja ra’ayina game da kaina.
Bayan haka, na halarci wani taron gunduma na Shaidun Jehobah. Na lura da yadda ko’ina yake da tsabta da yadda suka yi kome bisa tsari da cuɗanyar da ke tsakaninsu, kuma hakan ya ba ni tabbaci cewa na sami addini na gaskiya. (Yohanna 13:34, 35) Na yi baftisma a watan Fabrairu, 2001.
YADDA NA AMFANA:
Jehobah ya gyara ni kuma na canja daga azzalumi zuwa mutum mai son zaman lafiya. Ina ji kamar ya cire ni daga cikin taɓo mai zurfi. Mutane da yawa sun tsane ni, amma ba na ganin laifinsu. A yanzu ina jin daɗin bauta wa Jehobah tare da matata da yaranmu biyu cikin kwanciyar hankali.
Dangina da kuma abokaina na dā suna mamakin ganin yadda na canja halina, kuma hakan ya sa wasu cikinsu sun soma koyon gaskiya da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Na sami gatan taimaka ma wasu su soma bauta wa Jehobah. Hakika, na yi farin cikin ganin yadda gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki take gyara rayuwarsu!