Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp22 Na 1 pp. 12-13
  • 4 | Ka Nemi Taimakon Allah don Ka Daina Kin Mutane

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • 4 | Ka Nemi Taimakon Allah don Ka Daina Kin Mutane
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:
  • Abin da Ayar Take Nufi:
  • Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:
  • Littafi Mai Tsarki Yana Gyara Rayuwar Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Abin da Mutum Zai Yi don Ya Daina Kin Mutane
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Zai Yiwu Mu Daina Nuna Kiyayya!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
  • Me Ya Sa Kiyayya Ta Yi Yawa Haka?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2022
wp22 Na 1 pp. 12-13
Mutane suna matsowa kusa da wani Littafi Mai Tsarki da aka bude kuma yana haska su. Inuwarsu ce take kwatanta halin kiyayyarsu da suka bari.

ABIN DA MUTUM ZAI YI DON YA DAINA KIN MUTANE

4 | Ka Nemi Taimakon Allah Don Ka Daina Ƙin Mutane

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce:

“Halin da ruhun Allah yake haifar shi ne ƙauna, da farin ciki, da salama, da haƙuri, da kirki, da nagarta, da aminci, da tawali’u, da kuma shan ƙarfin sha’awar jiki.”​—GALATIYAWA 5:​22, 23.

Abin da Ayar Take Nufi:

Da taimakon Allah mutum zai iya daina ƙin mutane. Ruhu mai tsarki da Allah yake bayarwa zai iya taimaka mana mu zama da halaye masu kyau ko da muna ganin ba za mu iya canja halinmu ba. Don haka, abin da zai fi mana alheri shi ne mu dogara da Allah, maimakon mu yi ƙoƙarin daina ƙiyayya da kanmu. Idan muka dogara da Allah, mu ma za mu ga gaskiyar abin da manzo Bulus ya faɗa cewa: “Cikakken ikon da ya fi duka daga wurin Allah ne, ba daga wurinmu ba.” (2 Korintiyawa 4:7) Har ma za mu iya cewa: “Taimakona zai fito daga wurin Yahweh.”​—Zabura 121:2.

Yadda Za Ka Bi Wannan Ayar:

“Jehobah ya gyara ni. Na canja daga azzalumi zuwa mutum mai son zaman lafiya.”—WALDO

Ka roƙi Jehobah ya ba ka ruhu mai tsarki. (Luka 11:13) Ka ce ya taimake ka ka kasance da halayen kirki irin nasa. Ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da halaye da suke kawar da ƙiyayya, irin su ƙauna da salama da haƙuri da kuma kamun kai. Ka yi ƙoƙarin nuna waɗannan halayen a rayuwarka. Kuma ka riƙa yin tarayya da mutanen da su ma suke yin hakan. Waɗannan mutane za su ‘iza ka ka nuna ƙauna kuma ka yi nagarta.’​—Ibraniyawa 10:24.

Labarin Wani Mutum​—WALDO

Ya Daina Ƙiyayya da Zafin Hali

Waldo.

Akwai wani mutum mai suna Waldo. A lokacin da yake tasowa, rayuwa ba ta yi masa sauƙi ba. Don haka, ya taso da ƙiyayya a zuciyarsa. Waldo ya ce: “Na sha yin faɗa da dillalan ƙwayoyi a kan titi . . . Akwai ma lokacin da suka aiki wani ƙwararren mai kisa ya kashe ni, amma na kuɓuce masa kuma ya ji mini rauni kaɗan ne kawai.”

Da matar Waldo ta soma nazari da Shaidun Jehobah, bai so hakan ba. Ya ce: “Na tsani Shaidun Jehobah, kuma sau da yawa nakan zuba musu ashar. Amma a kowane lokaci suna yi mini ladabi maimakon su rama.”

A kwana a tashi, Waldo ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma ya ce: “Bai yi mini sauƙi in bi abin da nake koya ba. Na ɗauka cewa ba zan iya daina wannan zafin halin nawa ba.” Amma akwai wani abin da ya karanta a Littafi Mai Tsarki da ya shiga zuciyarsa sosai.

Waldo ya ce: “Wata rana, Alejandro wanda yake yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ni ya ce in karanta Galatiyawa 5:​22, 23. . . . Sai Alejandro ya bayyana mini cewa idan da iyawata ne, ba zan iya kasancewa da halayen nan ba, amma da taimakon ruhu mai tsarki zan iya kasancewa da su. Hakan ya sa na ga cewa ashe zan iya canja halina.”

Waldo ya daina ƙin mutane domin ya dogara ga Allah ya taimake shi. Waldo ya ce: “Dangina da kuma abokaina na dā suna mamakin ganin yadda na canja halina.” Ya kuma ƙara da cewa: “Jehobah ya gyara ni. Na canja daga azzalumi zuwa mutum mai son zaman lafiya.”

Za ka iya karanta cikakken labarin Waldo a Hasumiyar Tsaro na 1 ga Oktoba, 2013 shafi na 12-13, akwai shi a dandalin jw.org/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba