Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 1/15 pp. 7-11
  • Ka Bauta wa Jehobah, Sarki na Zamanai

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bauta wa Jehobah, Sarki na Zamanai
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SARKIN ZAMANAI YA HALICCI MALA’IKU DA MUTANE
  • ’YA’YA MASU TAWAYE SUN ƘI DA SARAUTAR ALLAH
  • SARAUTAR JEHOBAH BAYAN RIGYAWA
  • JEHOBAH YA ZAMA SARKI GA ISRA’ILAWA
  • JEHOBAH YA NAƊA SABON SARKI
  • KA BAUTA WA SARKIN ZAMANAI
  • Jehobah Yana Bayyana Nufinsa
    Mulkin Allah Yana Sarauta!
  • Al’amari da Dukanmu Dole Mu Fuskanta
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 1/15 pp. 7-11

Ka Bauta wa Jehobah, Sarkin Zamanai

“Girma da ɗaukaka su tabbata ga Sarkin zamanai . . . har abada.”—1 TIM. 1:17, Littafi Mai Tsarki.

MECE CE AMSARKA?

  • Me ya sa muke son yadda Jehobah yake sarauta?

  • Ta yaya Jehobah ya ci gaba da yin ƙaunar ’yan Adam?

  • Me ya sa kake so ka bauta wa Sarkin zamanai?

1, 2. (a) Wane ne “Sarkin zamanai,” kuma me ya sa laƙabin ya dace da shi? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.) (b) Me ya sa muke so Jehobah ya mulke mu?

SARKI SOBHUZA na biyu ya yi sarauta kusan shekaru 61 a ƙasar Suwazilan. Ko da yake abin mamaki ne ɗan Adam ya jima yana sarauta haka, amma akwai wani sarki wanda sarautarsa ba kamar na ’yan Adam waɗanda suke rayuwa na ɗan lokaci ba. Hakika, Littafi Mai Tsarki ya ce da shi “Sarkin zamanai.” (1 Tim. 1:17, LMT) Wani marubucin zabura ya ambata sunan wannan Sarki Mai-girma, ya ce: “[Jehobah] Sarki ne har abada.”—Zab. 10:16.

2 Tsawon lokacin da Allah yake sarauta ne ya bambanta sarautarsa da ta ’yan Adam. Amma, yadda Jehobah yake sarautarsa ne ya sa muke kusantar shi. Wani sarki da ya yi sarautar tsawon shekaru 40 bisa Isra’ila ta dā ya yabi Allah sa’ad da ya ce: “Ubangiji cike da tausayi yake, mai-alheri, mai-jinkirin fushi, mai-yalwar jinƙai kuma. Ubangiji ya kafa kursiyinsa a cikin sammai; Mulkinsa kuwa yana bisa kowa.” (Zab. 103:8, 19) Jehobah sarkinmu ne kuma shi ƙaunataccen Ubanmu na sama ne. Amma, a wace hanya ce Jehobah ya zama Ubanmu? Ta yaya Jehobah ya nuna cewa shi sarki ne tun daga lokacin da aka yi tawaye a Adnin? Amsoshin waɗannan tambayoyin za su sa mu kusaci Jehobah kuma mu bauta masa da dukan zuciyarmu.

SARKIN ZAMANAI YA HALICCI MALA’IKU DA MUTANE

3. Wane ne halittar Jehobah na farko, kuma su waye ne aka halitta a matsayin “’ya’yan Allah”?

3 Babu shakka, Jehobah ya yi farin ciki sa’ad da ya halicci Ɗansa na fari! Jehobah bai bi da ɗansa na fari kamar bawa ba. Maimakon hakan, ya ƙaunace shi a matsayin Ɗa kuma ya gayyace shi ya saka hannu wajen halittar miliyoyin kamiltattun mala’iku. (Kol. 1:15-17) Littafi Mai Tsarki ya ce waɗannan mala’ikun suna farin cikin bauta wa Jehobah a matsayin “masu-hidima nasa, waɗanda ke aika yardarsa.” Jehobah ya ɗaukaka su sa’ad da ya kira su ‘’ya’yansa.’ Kuma suna cikin halittunsa na sama da ƙasa.—Zab. 103:20-22; Ayu. 38:7.

4. A wane lokaci ne ’yan Adam suka zama iyali guda da mala’ikun Jehobah?

4 Bayan Jehobah ya halicci sama da ƙasa, sai ya yi wasu halittu da za su haɗin kai da mala’ikun da suke sama. Ta yaya ya yi hakan? Sa’ad da ya shirya duniya kuma ya sa ta zama waje mai kyau, sai ya halicci mutum na farko, wato Adamu a surarsa. (Far. 1:26-28) Da yake Jehobah ne Mahalicci, ya so Adamu ya yi biyayya. A matsayin Uba, Jehobah ya umurci Adamu cikin ƙauna da kuma kirki. Bai kafa wa Adamu dokokin da suka fi ƙarfinsa ba.—Karanta Farawa 2:15-17.

5. Wane shiri ne Jehobah ya yi don mutane su cika duniya?

5 Akasin sarakuna ’yan Adam, Jehobah yana bi da mutanensa kamar iyali. Ya amince da su kuma ya ɗanka musu hakki da yawa da kuma ikon yin ayyukansu. Alal misali, ya ba wa Adamu iko bisa wasu halittun, kuma ya ba shi wani aiki mai daɗi, wato ya sa wa dabbobin sunaye. (Far. 1:26; 2:19, 20) Allah bai halicci miliyoyin mutane kamiltattu kawai kuma ya saka su cika duniya ba. Maimakon haka, ya halicce wa Adamu kamiltacciyar mace, wato Hawwa’u. (Far. 2:21, 22) Bayan haka, sai ya ba wa ma’auratan zarafin cika duniya da ’ya’ya. A cikin yanayi mai kyau, Adamu da Hawwa’u za su ci gaba da faɗaɗa Aljanna a duniya baƙi ɗaya. Hakan zai sa dukan ’yan Adam da kuma mala’iku su bauta wa Jehobah har abada a matsayin iyali ɗaya. Hakika, wannan abin al’ajabi ne! Da gaske, Jehobah ya nuna wa Adamu da Hawwa’u ƙauna irin ta uba.

’YA’YA MASU TAWAYE SUN ƘI DA SARAUTAR ALLAH

6. (a) Ta yaya aka soma tawaye a iyalin Allah? (b) Ta yaya muka san cewa har ila Jehobah yana sarauta bisa mutane?

6 Abin baƙin ciki, Adamu da Hawwa’u ba su so Jehobah a matsayin Sarkinsu ba. Maimakon hakan, sun bi Shaiɗan wanda ya yi tawaye da Allah. (Far. 3:1-6) A sakamako, sun jawo wa kansu da yaransu baƙin ciki da wahala da kuma mutuwa. (Far. 3:16-19; Rom. 5:12) Hakan ya sa Jehobah ya rasa ’ya’ya masu biyayya a duniya. Shin hakan ya nuna cewa ya kasa ne, wato ba zai iya yin sarauta bisa mutane kuma ba? A’a. Jehobah ya kori Adamu da Hawwa’u daga lambun Adnin kuma ya sanya cherubim a mashigin lambun don kada su sake dawowa. (Far. 3:23, 24) A daidai wannan lokacin kuma Jehobah ya sake nuna ƙauna irin ta uba. Ya yi hakan ta wajen yin alkawari cewa zai cika maƙasudansa na kasancewa da halittu da ya ƙunshi ’yan Adam da kuma mala’iku masu aminci. Ya yi alkawari cewa ɗaya daga cikin ’ya’yan Adamu zai halaka Shaiɗan kuma ya kawar da matsalolin da zunubi ya jawo.—Karanta Farawa 3:15.

7, 8. (a) Yaya yanayin duniya yake a lokacin Nuhu? (b) Mene ne Jehobah ya yi don ya tsabtacce duniya kuma ya kāre iyalin ’yan Adam?

7 A cikin karnukan da suka shige, mazaje kamar su Habila da kuma Anuhu sun zaɓi su kasance da aminci ga Jehobah. Amma, yawanci ’yan Adam sun ƙi Jehobah a matsayi Ubansu da kuma Sarkinsu. A lokacin Nuhu, duniya kuwa ta “cika da zalunci.” (Far. 6:11) Shin hakan yana nufi cewa Jehobah ba zai iya sarauta bisa duniya ba? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce?

8 Ka yi la’akari da labarin Nuhu. Jehobah ya ba shi umurni dalla-dalla a kan yadda zai gina jirgin da zai kāre shi da iyalinsa. Allah ya kuma nuna ƙauna ga ’yan Adam sa’ad da ya naɗa Nuhu a matsayin “mai-shelan adalci.” (2 Bit. 2:5) Babu shakka, Nuhu ya ce su tuba kuma ya gargaɗar da su game da halakar da ke tafe, amma sun yi kunnen uwar shegu. Nuhu da iyalinsa sun yi shekaru da yawa suna zama cikin duniyar da ke cike da mugunta da kuma lalata. A matsayinsa na Uba mai ƙauna, Jehobah ya kāre kuma ya ja-goranci waɗannan mutane takwas masu aminci. Rigyawar da Jehobah ya kawo ta nuna ikonsa bisa ’yan Adam masu tawaye da kuma mugayen mala’iku. Babu shakka, hakan ya nuna cewa har ila shi ne ke sarauta bisa duniya.—Far. 7:17-24.

SARAUTAR JEHOBAH BAYAN RIGYAWA

9. Wane zarafi ne Jehobah ya ba ’yan Adam bayan Rigyawar?

9 Babu shakka, Nuhu da iyalinsa sun yi godiya ga Jehobah sa’ad da suka fito daga cikin jirgi domin irin kula da kuma kāriya da ya yi musu. Nan da nan, Nuhu ya gina bagadi kuma ya miƙa hadaya ga Jehobah don ya bauta masa. Allah ya albarkaci Nuhu da iyalinsa kuma ya ba su umurni cewa: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓanɓanya, ku mamaye duniya.” (Far. 8:20–9:1) ’Yan Adam yanzu kuma suna da zarafin bauta wa Jehobah tare kuma su cika duniya.

10. (a) A ina ne mutane suka soma tawaye da Jehobah bayan Rigyawar, kuma ta yaya? (b) Mene ne Jehobah ya yi don ya tabbata cewa an yi nufinsa?

10 Rigyawa ba ta cire ajizanci ba, kuma mutane har ila suna bukata su jure da tasirin Shaiɗan da kuma aljanu. Ba da daɗewa ba, mutane kuma suka sake soma yin tawaye da sarautar Jehobah mai kyau. Alal misali, tattaɓa kunnen Nuhu, wato Nimrod, ya yi adawa da sarautar Jehobah. Nimrod ‘ƙaƙarfan mai-farauta ne a gaban Ubangiji.’ Ya gina manyan birane, har da Babel, kuma ya sanya kansa a matsayin sarki a “cikin ƙasar Shinar.” (Far. 10:8-12) Wane mataki ne Sarkin zamanai zai ɗauka a kan wannan sarkin da ya yi tawaye kuma yake ƙoƙari ya ɓata nufin Allah? Jehobah ya dagula harshen mutanen, kuma “ya warwatsar da su ko’ina bisa fuskar dukan duniya.” Kuma, ko’ina da suka je, sun tafi da bautarsu ta ƙarya da kuma tsarin sarautarsu.—Far. 11:1-9.

11. Ta yaya Jehobah ya nuna aminci ga abokinsa Ibrahim?

11 Mutane da yawa sun ci gaba da bauta wa allolin ƙarya bayan Rigyawar, amma akwai wasu mazaje masu aminci da suka ci gaba da bauta wa Jehobah. Ɗaya cikinsu shi ne Ibrahim. Ya ƙaura daga birnin Ur kuma ya kwashi shekaru yana zama a tanti. (Far. 11:31; Ibran. 11:8, 9) Ibrahim bai dogara ga kāriyar da sarakuna ’yan Adam ko kuma ganuwar birni suke yi ba. Maimakon hakan, Jehobah ne ya kāre shi da iyalinsa. Wani marubucin zabura ya ce game da Jehobah: “[Allah] ba ya bar wani mutum shi zalunce su ba; I, ya tsauta wa sarakuna sabili da su.” (Zab. 105:13, 14) Da yake Jehobah ya amince da abokinsa Ibrahim, ya yi masa alkawari cewa: “Sarakuna kuma za su fito daga cikinka.”—Far. 17:6; Yaƙ. 2:23.

12. Ta yaya Jehobah ya nuna ikonsa bisa ƙasar Masar, kuma ta ya hakan ya taimaki mutanensa?

12 Jehobah ya yi wa ɗan Ibrahim, Ishaƙu da kuma jikansa Yaƙubu alkawari cewa zai albarkace su kuma zuriyarsu za su zama sarakuna. (Far. 26:3-5; 35:11) Amma, sai da zuriyar Yaƙubu suka zama bayi a ƙasar Masar kafin suka zama sarakuna. Shin hakan yana nufin cewa Jehobah ba zai cika alkawarinsa ba ne, ko kuma ya kasa yin sarauta bisa duniya? Ko kaɗan! Jehobah ya nuna ikonsa kuma ya tabbatar wa Fir’auna mai taurin kai cewa shi ke sarauta bisansa a daidai lokacin da ya ƙayyade. Isra’ilawa sun kasance da bangaskiya ga Jehobah, kuma ya cetar da su a hanya mai ban mamaki ta Jan Teku. Babu shakka, Jehobah ne yake sarauta bisa duniya baƙi ɗaya a lokacin kuma a matsayin Uba mai kula, yana amfani da ikonsa don kāre mutanensa.—Karanta Fitowa 14:13, 14.

JEHOBAH YA ZAMA SARKI GA ISRA’ILAWA

13, 14. (a) Mene ne Isra’ilawa suka ce a game da Sarautar Jehobah a waƙar da suka rera? (b) Wane alkawarin sarauta ne Allah ya yi wa Dauda?

13 Bayan Jehobah ya ceci Isra’ilawa daga ƙasar Masar, sai suka yi masa waƙar yabo da aka rubuta a littafin Fitowa sura 15. Aya ta 18 ta ce: “Ubangiji za ya yi mulki har abada abadin.” Hakika, Jehobah ya zama Sarki ga Isra’ilawa. (K. Sha 33:5) Amma, Isra’ilawa ba su daraja Jehobah sosai a matsayin Sarkinsu ba. Wajen shekaru 400 bayan sun bar ƙasar Masar, sun ce Allah ya naɗa musu sarki ɗan Adam kamar yadda wasu al’umman arna suka yi. (1 Sam. 8:5) A zamanin Dauda, Jehobah ya nuna cewa har ila shi Sarki ne.

14 Dauda ya kawo sunduƙin alkawari cikin Urushalima. A wannan lokaci na farin ciki, Lawiyawa sun rera wata waƙar yabo da ke ɗauke da wasu kalmomi masu muhimmanci da ke littafin 1 Labarbaru 16:31. Ayar ta ce: “A cikin al’ummai kuma ku ce, Ubangiji yana mulki [‘Jehobah ya zama Sarki!’ NW]” Wani zai iya yin tunani cewa, ‘Tun da Jehobah ne Sarkin zamanai, me ya sa aka ce ya zama Sarki a wannan lokacin?’ Jehobah ya zama Sarki sa’ad da ya yi amfani da ikonsa ko kuma ya naɗa wani ya wakilce shi. Yana da muhimmanci mu fahimci yadda Jehobah ya zama Sarki. Kafin Dauda ya mutu, Jehobah ya yi masa alkawari cewa sarautarsa za ta ci gaba har abada, ya ce: “Zan kafa zuriyarka daga bayanka, wanda za ya fito daga tsatsonka, zan kuma kafa mulkinsa.” (2 Sam. 7:12, 13) Wannan alkawarin ya cika sa’ad da ‘zuriya’ ko kuma ɗan Dauda ya bayyana bayan shekaru fiye da 1,000. Wane ne wannan ɗan, kuma a yaushe ne ya zama Sarki?

JEHOBAH YA NAƊA SABON SARKI

15, 16. A yaushe ne aka naɗa Yesu a matsayin Sarki na nan gaba, kuma sa’ad da Yesu yake duniya, waɗanne shirye-shirye ne ya yi don Mulkinsa?

15 A shekara ta 29 a zamaninmu, Yohanna Mai Baftisma ya soma wa’azi cewa “Mulkin sama ya kusa.” (Mat. 3:2) Sa’ad da Yohanna ya yi wa Yesu baftisma, Jehobah ya shafe Yesu a matsayin Almasihu da kuma Sarkin Mulkin Allah na nan gaba. Jehobah ya nuna wa Yesu ƙauna irin ta Uba yayin da ya ce: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.”—Mat. 3:17.

16 Sa’ad da Yesu yake hidimarsa, ya ɗaukaka Ubansa, wato Jehobah. (Yoh. 17:4) Ya yi hakan ta wajen yin wa’azi game da Mulkin Allah. (Luk 4:43) Ya ma koya wa mabiyansa su yi addu’a don wannan Mulkin ya zo. (Mat. 6:10) A matsayin Sarkin da aka zaɓa, Yesu ya gaya wa masu adawa da shi cewa: “Mulkin Allah yana cikinku.” (Luk 17:21) Daga baya, daddare kafin Yesu ya mutu, ya yi wa mabiyansa alkawarin “Mulki.” Hakan yana nufi cewa wasu almajiran Yesu masu aminci za su zama sarakuna tare da shi a cikin Mulkin Allah.—Karanta Luka 22:28-30.

17. A wace hanya ce Yesu ya soma sarauta a shekara ta 33, kuma don me yake bukata ya ɗan jira?

17 A yaushe ne Yesu zai soma sarauta a matsayin Sarkin Mulkin Allah? Ba zai yi hakan nan da nan ba. Washegari da rana aka kashe Yesu kuma almajiransa suka warwatse. (Yoh. 16:32) Amma har ila, Jehobah bai daina sarauta ba. A rana ta uku, ya ta da Ɗansa kuma a ranar Fentakos ta shekara ta 33 a zamaninmu, Yesu ya soma sarauta bisa ikilisiyar Kirista. (Kol. 1:13) Amma Yesu, wato ɗan Dauda da aka yi alkawarinsa, yana bukatar ya jira sai ya sami dukan iko bisa duniya. Saboda haka, Jehobah ya gaya wa Ɗansa cewa: “Ka zauna ga hannun damana, har in maida maƙiyanka matashin sawunka.”—Zab. 110:1.

KA BAUTA WA SARKIN ZAMANAI

18, 19. Mene ne ya kamata mu yi, me za mu koya a talifi na gaba?

18 A cikin shekaru aru-aru, mala’iku da kuma mutane sun yi tawaye da sarautar Jehobah. Amma, har ila Jehobah ya ci gaba da sarauta. A matsayin Uba mai ƙauna, ya kula da kuma kāre mutanensa masu aminci, kamar su Nuhu da Ibrahim da kuma Dauda. Babu shakka, ya kamata hakan ya motsa mu mu kusaci Sarkinmu kuma mu yi biyayya a gare shi.

19 Amma za mu iya cewa: Ta yaya Jehobah ya zama Sarki a zamaninmu? Ta yaya za mu kasance mutanensa masu aminci kuma mu zama ’ya’ya kamiltattu cikin haɗin kai da mala’ikunsa? Shin mene ne yake nufi sa’ad da muka yi addu’a cewa bari Mulkin Allah ya zo? Za a amsa waɗannan tambayoyin a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba