Ka Ba da Gaskiya Sosai ga Mulkin
“Bangaskiya kuwa ita ce haƙƙaƙewar abubuwan da aka sa zuciya a kai.”—IBRAN. 11:1, Littafi Mai Tsarki.
1, 2. Mene ne zai ƙarfafa bangaskiyarmu cewa Mulkin zai cim ma nufin Allah ga ’yan Adam, kuma me ya sa? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.)
A MATSAYIN Shaidun Jehobah, muna koyar da mutane cewa Mulkin Allah ne kaɗai zai magance dukan matsalolinmu kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa. Ƙari ga haka, muna samun ƙarfafa sosai don abubuwan da Mulkin zai tanadar mana. Shin, mun tabbata da gaske cewa Mulkin ba ƙage ba ne kuma zai cim ma nufin Allah? Me ya sa muka ba da gaskiya cewa Mulkin zai cim ma nufin Allah?—Ibran. 11:1.
2 Allah Maɗaukakin Sarki da kansa ne ya kafa Mulkin Almasihu kuma ya yi hakan don ya cim ma nufinsa game da ’yan Adam. An kafa wannan Mulkin ne a kan tushe mai inganci sosai, wato, ikon da Jehobah yake da shi na yin sarauta. Allah ya tabbatar da fasaloli masu muhimmanci game da Mulkin. Waɗannan fasalolin su ne: Sarkin da abokan sarautarsa da kuma daular Mulkin. Ya tabbatar da hakan ta wajen alkawura ko kuma yarjejeniyoyi da Shi da Ɗansa Yesu Kristi suka yi. Tattauna waɗannan alkawuran zai sa mu ƙara fahimta cewa ba abin da zai hana nufin Allah cika, ƙari ga haka, zai sa mu gane cewa Mulkin tabbatacce ne.—Karanta Afisawa 2:12.
3. Mene ne za mu bincika a wannan talifin da kuma na biye da shi?
3 Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kan alkawura masu muhimmanci guda shida da suke da alaƙa da Mulkin Almasihu. Waɗannan su ne, (1) alkawarin da aka yi da Ibrahim, (2) alkawari bisa Doka, (3) alkawarin da aka yi da Dauda, (4) alkawari da aka yi na zama firist kamar Melchizedek, (5) sabon alkawari, da kuma (6) alkawari na Mulki. Bari mu bincika yadda kowane alkawari yake da alaƙa da Mulkin da kuma yadda yake tabbatar da cikar nufin Allah game da duniya da kuma ’yan Adam baki ɗaya.—Ka duba jadawalin nan “Yadda Allah Zai Cim ma Nufinsa.”
ALKAWARIN DA YA NUNA YADDA NUFIN ALLAH ZAI CIKA
4. Kamar yadda aka ambata a littafin Farawa, waɗanne dokoki da suka shafi ’yan Adam ne Jehobah ya kafa?
4 Jehobah ya yi duniya don ’yan Adam su zauna a cikinta. Bayan haka, sai ya kafa dokoki uku da suka shafi ’yan Adam: Na ɗaya, Allah zai halicci mutum a cikin kamaninsa. Na biyu, ’yan Adam za su mai da duniya Aljanna kuma su cika ta da ’ya’ya masu kirki. Na uku, an hana ’yan Adam cin ’ya’yan itacen sanin nagarta da mugunta. (Far. 1:26, 28; 2:16, 17) Bayan waɗannan, ba a bukatar ƙarin doka. Allah ya cika dokar farko ta wajen halittar Adamu. Bayan haka, abin da ake bukata don nufin Allah ya cika shi ne biyayya ga sauran dokoki biyun. Shin me ya sa kuma Allah ya yi alkawura daga baya?
5, 6. (a) Ta yaya Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya hana cikar nufin Allah? (b) Yaya Jehobah ya bi da ƙalubalen da Shaiɗan ya yi a Adnin?
5 Shaiɗan ya ƙulla maƙirci don ya hana cikar nufin Allah. Don ya cim ma aniyarsa, ya mai da hankali ga dokar da zai fi yin tasiri a kai, wato dokar da ta bukaci biyayyar Adamu. Ya yaudari macen farko, wato Hawwa’u ta karya dokar da Allah ya kafa game da sanin nagarta da mugunta. (Far. 3:1-5; R. Yoh. 12:9) Wannan matakin da Shaiɗan ya ɗauka ya nuna cewa yana ƙalubalantar ikon da Allah yake da shi na yin sarauta bisa halittunsa. Daga baya, Shaiɗan ya ƙara da’awa cewa ’yan Adam suna bauta wa Allah don abubuwan da yake yi musu ne.—Ayu. 1:9-11; 2:4, 5.
6 Ta yaya Jehobah zai bi da wannan ƙalubalen? Zai iya halaka ’yan tawayen idan ya ga dama. Amma idan ya yi hakan, ba zai cim ma nufinsa na cika duniya da ’ya’yan Adamu da Hawwa’u masu biyayya ba. Da yake shi Mahalicci ne mai hikima, bai halaka su nan take ba. A maimakon haka, ya furta wani annabci mai ban al’ajabi don ya tabbata cewa dukan abubuwan da ya faɗa za su cika. Wannan annabcin shi ne Alkawarin da aka yi a Adnin.—Karanta Farawa 3:15.
7. Mene ne alkawarin da aka yi a Adnin ya bayyana game da Shaidan da kuma zuriyarsa?
7 Sa’ad da Jehobah yake furta Alkawarin da ya yi a Adnin, ya yanke hukunci a kan macijin da zuriyarsa, wato Shaiɗan da dukan waɗanda suka goyi bayansa a batun ikon sarauta na Allah. Allah ya ba wa zuriyar macen da aka ambata a annabcin ikon halaka Shaiɗan. Ta hakan, alkawarin da aka yi a Adnin ya nuna cewa za a kawo ƙarshen Shaiɗan da kuma mugun sakamakon da tawayensa ya jawo. Ƙari ga haka, alkawarin ya nuna yadda za a cim ma hakan.
8. Mene ne muka koya game da ko wane ne macen da kuma zuriyarta?
8 Shin wane ne zai zama zuriyar macen? Tun da zuriyar ce za ta ƙuje kan macijin ko kuma halaka Shaiɗan Iblis, hakan ya nuna cewa wannan zuriyar ruhu ne. (Ibran. 2:14) Saboda haka, macen da za ta haifi wannan zuriyar ba mace na zahiri ba. Yayin da zuriyar macijin yake yaɗuwa, an yi kusan shekaru 4,000 bayan Jehobah ya yi alkawari a Adnin, ba a san ko wane ne macen da kuma zuriyarta ba. A cikin waɗannan shekarun, Jehobah ya yi alkawura da dama da suka bayyana ko wane ne zuriyar. Ƙari ga haka, ya tabbatar da bayinsa cewa ta wannan zuriyar ne zai magance dukan matsalolin da Shaiɗan ya hadassa.
ALKAWARIN DA YA BAYYANA ZURIYAR
9. Wane alkawari ne Allah ya yi da Ibrahim, kuma a wace shekara ce alkawarin ya soma cika?
9 Wajen shekaru dubu biyu bayan an yanke hukunci a kan Shaiɗan, Jehobah ya umurci Ibrahim cewa ya bar gidansa a birnin Ur da ke ƙasar Mesopotamiya kuma ya je ƙasar Kan’ana. (A. M. 7:2, 3) Jehobah ya ce masa: “Ka fita daga ƙasarka, daga danginka kuma, da gidan ubanka, zuwa ƙasa da zan nuna maka: daga wurinka zan yi al’umma mai-girma, zan albarkace ka kuma, in sa ka yi suna; ka zama albarka: waɗanda sun albarkace ka zan albarkace su, in la’antar da wanda ya la’antar da kai: a cikinka kuma dukan kabilan duniya za su yi albarka.” (Far. 12:1-3) Wannan shi ne Alkawarin da aka yi da Ibrahim. Ba a san ainihin lokacin da Jehobah ya yi wannan alkawarin da Ibrahim ba. Amma ya soma cika a shekara ta 1943 kafin zamaninmu, sa’ad da Ibrahim ya ƙetare Kogin Yufiretis daga Haran, a lokacin da yake da shekara 75.
10. (a) Ta yaya Ibrahim ya ba da gaskiya sosai ga alkawuran Allah? (b) Waɗanne bayanai ne Jehobah ya ƙara yi game da zuriyar macen da sannu-sannu?
10 Jehobah ya sake maimaita alkawarin da ya yi ga Ibrahim da dama, kuma ya ƙara wasu bayanai a kai. (Far. 13:15-17; 17:1-8, 16) Ibrahim ya ba da gaskiya ga alkawuran Allah ta wajen son ba da ɗansa tilo hadaya, saboda haka, Jehobah ya ƙara inganta alkawarin. Ya yi hakan ta wajen ba da tabbaci cewa zai cika alkawarin tabbas. (Karanta Farawa 22:15-18; Ibraniyawa 11:17, 18.) Bayan alkawarin da aka yi da Ibrahim ya soma cika, sai Jehobah ya soma bayyana wasu muhimman abubuwa game da zuriyar macen da sannu-sannu. Waɗannan abubuwa su ne cewa: Zuriyan zai fito daga iyalin Ibrahim kuma zai yaɗu, zai yi sarauta, ya halaka dukan magabta, ƙari ga haka, zai sa mutane da yawa su sami albarka.
11, 12. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Alkawarin da aka yi da Ibrahim zai sake cika, kuma ta yaya za mu amfana?
11 Ko da yake, alkawarin da aka yi da Ibrahim ya cika da farko sa’ad da waɗanda suka fito daga zuriyarsa suka mallaki Ƙasar Alkawari, duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa wannan alkawarin zai sake cika. (Gal. 4:22-25) Allah ya hure manzo Bulus ya bayyana cewa a wannan cika ta biyu mai muhimmanci, Kristi ne ainihin zuriyar Ibrahim kuma Kiristoci shafaffu 144,000 ne sauran waɗanda zuriyar ta ƙunsa. (Gal. 3:16, 29; R. Yoh. 5:9, 10; 14:1, 4) Macen da aka ambata a alkawarin da aka yi a Adnin ita ce sashen ƙungiyar Allah da ke sama kuma ta ƙunshi amintattun halittu na ruhu. (Gal. 4:26, 31) Kamar yadda alkawarin da aka yi da Ibrahim ya nuna, zuriyar macen zai sa ’yan Adam su sami albarka.
12 Alkawarin da aka yi da Ibrahim ya ba da tabbaci cewa Mulkin sama zai kasance kuma cewa Sarkin da abokan sarautarsa za su gāji Mulkin. (Ibran. 6:13-18) Shin yaushe ne wannan alkawarin zai gama cika? Littafin Farawa 17:7 ta ce alkawari nan “madawwami” ne. Zai ci gaba da cika har sai Mulkin Almasihu ya halaka magabtan Allah kuma dukan al’umman duniya sun sami albarka. (1 Kor. 15:23-26) Hakika, waɗanda za su yi rayuwa a duniya a lokacin za su amfana har abada. Babu shakka, alkawarin da Allah ya yi da Ibrahim ya nuna cewa Jehobah ya ƙudiri niyyar cim ma nufinsa na sa mutane masu adalci su “mamaye duniya!”—Far. 1:28.
ALKAWARIN DA YA TABBATAR CEWA MULKIN ZAI DAWWAMA
13, 14. Mene ne alkawarin da aka yi da Dauda ya tabbatar game da Mulkin Almasihu?
13 Alkawarin da aka yi a Adnin da Alkawarin da aka yi da Ibrahim sun nuna cewa sarautar Jehobah na adalci ne kuma an kafa Mulkin Almasihu bisa ƙa’idodin Allah na adalci. (Zab. 89:14) Shin Mulkin Almasihu zai lalace ne kuma a kawar da shi? Wani alkawari da Allah ya yi ya tabbatar mana cewa hakan ba zai taɓa faruwa ba.
14 Jehobah ya yi wani alkawari da Sarki Dauda na Isra’ila ta dā kuma wannan shi ne alkawarin da aka yi da Dauda. (Karanta 2 Sama’ila 7:12, 16.) Jehobah ya yi wannan alkawarin da Dauda sa’ad da yake sarauta a Urushalima, kuma ya ce masa Almasihu zai fito daga iyalinsa. (Luk 1:30-33) Ta hakan, Jehobah ya ba da takamaiman bayani sa’ad da ya ce wani daga iyalin Dauda ne zai zama “mai shi,” wato wanda ya cancanta ya yi sarauta a Mulkin Almasihu. (Ezek. 21:25-27, LMT) Ta wurin Yesu, mulkin Dauda zai “kafu . . . har abada.” Hakika, zuriyar Dauda “za ta tabbata har abada, Kursiyinsa kuma kamar rana.” (Zab. 89:34-37) Babu shakka, sarautar Yesu ba za ta taɓa lalacewa ba, kuma abubuwan da za ta cim ma za su dawwama!
ALKAWARI NA YIN HIDIMA A MATSAYIN FIRIST
15-17. Bisa ga alkawari da aka yi na zama firist kamar Melchizedek, wane ƙarin matsayi ne zuriyar za ta samu, kuma me ya sa?
15 Alkawarin da aka yi da Ibrahim da kuma alkawarin da aka yi da Dauda sun tabbatar mana cewa waɗanda suka ƙunshi zuriyar macen za su zama sarakuna, amma ba wannan matsayin ne kawai zai sa a albarkaci mutanen dukan al’ummai ba. Kafin su sami albarka na gaske, wajibi ne su sami ’yanci daga zunubi kuma su kasance cikin iyalin Jehobah. Don a cim ma hakan, za a bukaci zuriyar ya yi hidima a matsayin firist. Da yake Mahaliccinmu mai hikima ne, ya tabbatar da hakan ta wajen yin wani alkawari, wato Alkawari da aka yi na zama firist kamar Melchizedek.
16 Jehobah ya bayyana ta wurin Dauda cewa zai yi wani alkawari tsakaninsa da Yesu kaɗai, kuma wannan alkawarin ya ƙunshi abubuwa biyu: zai sa Yesu ya ‘zauna ga hannun damar [Allah]’ har sai ya halaka magabtansa kuma ya zama ‘firist har abada bisa ɗabi’ar Melchizedek.’ (Karanta Zabura 110:1, 2, 4.) Me ya sa aka ce ‘bisa ɗabi’ar Melchizedek’? Don tun da daɗewa kafin zuriyar Ibrahim su gāji Ƙasar Alkawari, Melchizedek, Sarkin Salima, “firist na Allah Maɗaukaki” ne. (Ibran. 7:1-3) Jehobah ne da kansa ya naɗa shi firist. Shi kaɗai ne ya taɓa yin hidima a matsayin sarki da firist kafin zamanin Yesu. Ƙari ga haka, bai gāji wannan matsayin daga wani ba kuma babu wanda ya gāje shi. Saboda haka, za a iya ce shi “firist” ne har abada.
17 Bisa ga wannan alkawarin ne Jehobah da kansa ya naɗa Yesu firist, kuma zai kasance ‘firist . . . har abada bisa ɗabi’ar’ Melchizedek. (Ibran. 5:4-6) Wannan ya ba da tabbaci cewa Jehobah zai yi amfani da Mulkin Almasihu don ya cim ma nufinsa ga ’yan Adam a duniya.
ALKAWURA NE TUSHEN MULKIN
18, 19. (a) Mene ne alkawura da muka tattauna suka nuna game da Mulkin? (b) Wace tambaya ce za mu tattauna?
18 Daga alkawura da muka tattauna, mun koyi yadda kowanne yake da alaƙa da Mulkin Almasihu da kuma yadda aka kafa Mulkin ta yarjejeniyoyi. Alkawarin da aka yi a Adnin ya tabbatar cewa Jehobah zai yi amfani da zuriyar macen don ya cim ma nufinsa ga duniya da kuma ’yan Adam. Wane ne zuriyar, kuma a wane matsayi ne wannan zuriyar zai yi hidima? Alkawarin da aka yi da Ibrahim ya ba da amsar.
19 Alkawarin da aka yi da Dauda ya ba da takamaiman bayani game da ainihin zuriyar da kuma iyalin da zuriyar zai fito a ciki. Ƙari ga haka, ya ba zuriyar izinin yin sarauta bisa duniya don abubuwan da Mulkin zai cim ma su dawwama. Alkawarin da aka yi na zama firist kamar Melchizedek ya tabbatar cewa zuriyar zai yi hidima a matsayin firist. Ba Yesu kaɗai ba ne zai taimaka wajen mai da mutane kamiltattu. Akwai shafaffun da za su yi hidima tare da shi a matsayin sarakuna da firistoci har ila. Daga ina za su fito? Za a tattauna wannan a talifin da ke gaba.