DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FARAWA 12-14
Yarjejeniyar da Ta Shafe Ka
12:1-3; 13:14-17
Jehobah ya yi wata yarjejeniya ko alkawari da Ibrahim, kuma hakan ya sa zai yiwu Yesu da abokan sarautarsa su yi sarauta daga sama
Wannan yarjejeniyar ta soma aiki a shekara 1943 kafin haihuwar Yesu, lokacin da Ibrahim ya ketare Kogin Yufiretis sa’ad da yake zuwa ƙasar Kan’ana
Yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki har sai Yesu ya halaka maƙiyan Allah kuma ya kawo albarka ga ’yan Adam a nan duniya
Jehobah ya yi wa Ibrahim albarka don bangaskiyarsa. Idan muka gaskata da alkawuran Jehobah, waɗanne albarka ne za mu samu don yarjejeniyar da Jehobah ya yi da Ibrahim?