Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w14 12/15 pp. 22-26
  • Yadda Za Mu Fuskanci Karshen Zamani Tare

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Za Mu Fuskanci Karshen Zamani Tare
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • SUN TALLAFA WA JUNA
  • KU KASANCE DA HAƊIN KAI KAFIN RANAR JEHOBAH TA ZO
  • “MU GAƁAƁUWA NE NA JUNANMU”
  • YADDA ZA MU NUNA CEWA MU “GAƁAƁUWA NE NA JUNANMU”
  • Haɗin Kai Na Kiristoci Yana Ɗaukaka Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ana Gane Masu Bauta Ta Gaskiya Ta Haɗin Kansu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Bauta Cikin Haɗin Kai a Lokacinmu—Menene Take Nufi?
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
w14 12/15 pp. 22-26

Yadda Za Mu Fuskanci Ƙarshen Zamani Tare

“Mu gaɓaɓuwa ne na junanmu.”—AFIS. 4:25.

MECE CE AMSARKA?

  • Wane hali ne ya kamata matasa su guje wa, kuma me ya sa?

  • Me ya sa muke bukatar mu kasance “harhaɗe wuri ɗaya” cikin haɗin kai?

  • Ta yaya za ka nuna cewa kana son ka kasance cikin ’yan’uwanka masu haɗin kai?

1, 2. Mene ne Allah yake son dukan mutanensa, yara da manya su yi?

KAI matashi ne? Idan haka ne, ka kasance da tabbaci cewa kana da muhimmanci a ƙungiyar Jehobah a duk faɗin duniya. A ƙasashe da yawa, matasa ne suka fi yawa a cikin waɗanda suke yin baftisma. Abin ban ƙarfafa ne mu ga cewa matasa da yawa suna tsai da shawarar bauta wa Jehobah!

2 Idan kai matashi ne, kana jin daɗin cuɗanya da tsaranka? Wataƙila kana jin daɗin hakan. Muna farin cikin kasancewa tare da tsaranmu. Ko da a ina ne muka fito, Allah yana so dukan mutanensa, yara da manya, su kasance da haɗin kai. Manzo Bulus ya rubuta cewa nufin Allah ne “dukan [ire-iren, NW] mutane su tsira, kuma su kawo ga sanin gaskiya.” (1 Tim. 2:3, 4) A cikin Ru’ya ta Yohanna 7:9, mun ga kwatancin masu bauta wa Allah da suka fito daga cikin “kowane iri, da dukan kabilai da al’ummai da harsuna.”

3, 4. (a) Wane hali ne matasan zamani suke da shi a yau? (b) Wane hali ne ya jitu da abin da Afisawa 4:25 ya faɗa?

3 Akwai bambanci sosai tsakanin matasa da suke bauta wa Jehobah da matasan duniyar nan! Matasa da yawa da ba sa bauta wa Jehobah suna rayuwa ta son zuciya, wato suna mai da hankali ga abubuwa da suke so ne kawai. Wasu masu bincike sun kira su zamanin son zuciya. Ta yadda suke magana da kuma adonsu, suna nuna cewa sun rena tsofaffi, kuma suna ɗaukansu ba su waye ba.

4 Ana ganin wannan halin a ko’ina. Saboda haka, matasa da suke bauta wa Jehobah sun fahimta cewa guje wa wannan halin don su bi ra’ayin Allah bai da sauƙi. Ko a ƙarni na farko, Bulus ya umurci ’yan’uwa su guji “ruhun da ke aiki yanzu a cikin ’ya’yan kangara” da suka kasance da shi a “dā.” (Karanta Afisawa 2:1-3.) Ya kamata a yaba wa matasa da suka guji wannan halin kuma suna hidima da haɗin kai tare da ’yan’uwansu. Wannan matakin da suka ɗauka ya jitu da abin da Manzo Bulus ya faɗa cewa “mu gaɓaɓuwa ne na junanmu.” (Afis. 4:25) Yin hidima tare da haɗin kai yana da muhimmanci sosai yayin da ƙarshen wannan zamanin yake gabatowa. Bari mu tattauna wasu labaran Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu ga muhimmancin kasancewa da haɗin kai yayin da muke hidima tare.

SUN TALLAFA WA JUNA

5, 6. Wane darasi game da haɗin kai ne muka koya daga labarin Lutu da ’ya’yansa?

5 A dā, Jehobah ya ji daɗin kāre mutanensa sa’ad da suka tallafa wa juna a lokacin da suke fuskantar mawuyacin hali. Bayin Allah na zamani, manya da ƙanana za su iya koyan darasi daga waɗannan labaran Littafi Mai Tsarki. Lutu yana ɗaya daga cikinsu.

6 Lutu da iyalinsa sun sami kansu a mawuyacin yanayi a lokacin da ake so a halaka birnin Saduma da suke zama a ciki. Sai mala’iku suka gaya wa Lutu ya bar birnin kuma ya gudu zuwa duwatsu inda zai sami mafaka. Suka ce masa: ‘Ka tsere da ranka.’ (Far. 19:12-22) Lutu ya yi biyayya kuma yaransa mata biyu sun ba shi haɗin kai kuma suka bi shi sa’ad da yake barin birnin. Amma abin baƙin ciki, wasu na kusa da shi sun ƙi su bi shi. Samaran da za su auri ’ya’yan Lutu mata sun aza wannan tsohon “wasa yake yi.” Kuma hakan ya sa sun halaka. (Far. 19:14, Littafi Mai Tsarki) Lutu da ’ya’yansa mata da suka ba shi haɗin kai ne kaɗai suka tsira.

7. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa waɗanda suka kasance da haɗin kai sa’ad da Isra’ilawa suke barin ƙasar Masar?

7 Ka yi la’akari da wani misali. A lokacin da Isra’ilawa suke barin ƙasar Masar, ba su raba kansu rukuni-rukuni don kowa ya kama tafiyarsa ba. A lokacin da Musa ya “miƙa hannunsa bisa teku,” kuma Jehobah ya raba tekun, Musa bai haye tekun shi kaɗai ko kuma da wasu Isra’ilawa kaɗan ba. A maimakon haka, dukan taron jama’a ne suka wuce da taimakon Jehobah. (Fit. 14:21, 22, 29, 30) Sun ba da haɗin kai tare da “taron tattarmuka” wato mutanen da ba Isra’ilawa ba da suka bi su. (Fit. 12:38) Zai kasance wauta da a ce wasu matasa sun ware kansu kuma suka bi wata hanya da suke gani ya dace musu. Hakika, da a ce sun yi hakan, da Jehobah bai kāre su ba.—1 Kor. 10:1.

8. Ta yaya mutanen Allah suka kasance da haɗin kai a zamanin Jehoshaphat?

8 A zamanin Sarki Jehoshaphat, mutanen Allah sun fuskanci wani farmaki. “Runduna mai-girma” da ke kewaye da su sun kawo musu hari. (2 Laba. 20:1, 2) Mutanen Allah ba su yi ƙoƙari su yaƙi magabtansu da ƙarfinsu ba. Maimakon haka, sun dogara ga Jehobah. (Karanta 2 Labarbaru 20:3, 4.) Kowa bai yi hakan yadda ya ga dama ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Dukan Yahuda suka tsaya a gaban Ubangiji, tare da ƙananansu, da matansu, da ’ya’yansu.” (2 Laba. 20:13) Dukan al’ummar, da yara da manya suka haɗa hannu suka bi ja-gorar Jehobah, kuma ya kāre su daga hannun magabtansu. (2 Laba. 20:20-27) Wannan misali ne mai kyau na yadda mutanen Allah za su fuskanci ƙalubale a matsayin rukuni, ko ba haka ba?

9. Mene ne za mu iya koya game da haɗin kai daga ayyuka da halin Kiristoci a ƙarni na farko?

9 Kiristoci a ƙarni na farko sun bauta wa Allah da haɗin kai. Alal misali, bayan Yahudawa da yawa da waɗanda ba Yahudawa ba suka zama Kiristoci, sun lizima “a cikin koyarwar manzanni da zumunta da kakkaryawar gurasa da addu’o’i.” (A. M. 2:42) Sun kasance da haɗin kai sosai musamman sa’ad da ake tsananta musu don a wannan lokacin ne suka fi bukatar juna. (A. M. 4:23, 24) Babu shakka, yana da muhimmanci mu kasance da haɗin kai sa’ad da muke fuskantar mawuyacin hali!

KU KASANCE DA HAƊIN KAI KAFIN RANAR JEHOBAH TA ZO

10. A wane lokaci ne haɗin kai zai kasance da muhimmanci sosai?

10 Ba da daɗewa ba, za mu fuskanci yanayi mafi wuya a tarihin ’yan Adam. Annabi Joel ya kwatanta shi kamar rana “ta duhu da kududu.” (Joel 2:1, 2; Zaf. 1:14) Mutanen Allah za su kasance da haɗin kai a wannan lokacin. Ka tuna da kalmomin Yesu: “Kowanne mulkin da ya rabu biyu gāba da kansa, ya risbe.”—Mat. 12:25.

11. Wane kwatanci da ke Zabura 122:3, 4 ne ya shafi mutanen Allah a yau? (Ka duba hoton da ke shafi na 22.)

11 Muna bukatar mu kasance da haɗin kai saboda mawuyacin yanayi da zai faru a nan gaba. Za a iya kwatanta haɗin kai da muke bukatar mu kasance da shi da yadda gidaje a Urushalima ta dā suka yi kusa da juna. Gidajen sun yi kurkusa da juna sosai shi ya sa marubucin zabura ya kwatanta Urushalima kamar birni “da ke harhaɗe wuri ɗaya.” Hakan ya taimaka wa mazauna birnin su taimaka da kuma kāre juna. Bugu da ƙari, yadda suka yi kusa da juna ya tuna wa marubucin zabura yadda al’ummar, wato ‘ƙabilun Ubangiji’ suka kasance da haɗin kai sa’ad da suka taru don su bauta wa Jehobah. (Karanta Zabura 122:3, 4.) Hakazalika, muna bukata mu kasance a “harhaɗe wuri ɗaya” yanzu da kuma a nan gaba don mawuyacin kwanaki.

12. Mene ne zai taimaka mana mu tsira a lokacin farmakin da za a kai wa mutanen Allah?

12 Me ya sa kasancewa da haɗin kai yake da muhimmanci a wannan lokacin? Ezekiyel sura ta 38 ta yi annabcin wani farmaki da “Gog, na ƙasar Magog” zai kai wa mutanen Allah. Wannan ba lokacin da za mu bar kome ya shiga tsakaninmu ba. Ba za mu nemi taimako daga mutanen duniya ba. Maimakon haka, ya kamata mu kusaci yan’uwanmu sosai. Hakika, kasancewa a cikin rukuni ɗaya ba shi ne zai sa mu sami ceto ba. Jehobah da Ɗansa za su ceci waɗanda suke kiran sunan Jehobah a wannan lokacin wahala. (Joel 2:32; Mat. 28:20) Amma, kada mu ɗauka cewa za a ceci waɗanda suka ƙi yin tarayya da mutanen Allah, wato, waɗanda suka daina bauta wa Allah kuma suka yi ta kansu.—Mi. 2:12.

13. Waɗanne darussa ne matasa masu bauta wa Allah za su koya daga abin da muka tattauna?

13 Saboda haka, wauta ce matasa su bi tafarkin waɗanda suka ware kansu daga ’yan’uwa, ko ba haka ba? Lokacin da za mu bukaci junanmu sosai ya yi kusa. Kuma hakan ya shafi dukanmu, yara da manya! Hakika, yanzu ne lokaci da za mu koyi yin aiki tare kuma mu kasance da haɗin don hakan zai taimaka mana sosai a nan gaba.

“MU GAƁAƁUWA NE NA JUNANMU”

14, 15. (a) Me ya sa Jehobah yake koyar da mutanensa yara da manya a yau? (b) Wace shawara ce Jehobah ya ba mu don mu kasance da haɗin kai?

14 Jehobah yana taimaka mana mu “bauta masa da zuciya ɗaya.” (Zaf. 3:8, 9) Yana koyar da mu don mu cim ma nufinsa a nan gaba. Mene ne nufinsa ya ƙunsa? Yana son ya “tattara dukan abu cikin Kristi.” (Karanta Afisawa 1:9, 10.) Jehobah yana son ya sa dukan halittu su kasance da haɗin kai, kuma zai yi nasara a yin hakan. Saboda haka, a matsayin matashi, shin kana ganin muhimmancin ba wa ƙungiyar Jehobah haɗin kai?

15 Jehobah yana koya mana yadda za mu kasance da haɗin kai yanzu don mu ci gaba da yin hakan har abada. An sha bayyana mana a Nassosi cewa mu “yi wa juna tattali,” mu ‘yi zaman daɗin soyayya da juna,’ mu “yi wa juna ta’aziyya,” kuma mu riƙa “gina juna.” (1 Kor. 12:25; Rom. 12:10; 1 Tas. 4:18; 5:11) Jehobah ya san cewa Kiristoci ajizai ne, kuma hakan zai sa haɗin kai ya yi wuya, saboda haka muna bukatar mu riƙa ‘yi ma junanmu gafara.’—Afis. 4:32.

16, 17. (a) Wane dalili ɗaya ne ya sa muke halartar taro? (b) Wane darasi ne matasa za su koya daga misalin da Yesu ya kafa sa’ad da yake matashi?

16 Jehobah ya yi mana tanadin taron ikilisiya don mu kasance da haɗin kai. Sau da yawa mukan karanta abin da ke Ibraniyawa 10:24, 25. Manufar waɗannan taron da muke yi shi ne “mu lura da juna domin mu tsokani [ƙarfafa] juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka.” An yi mana tanadin zuwa taro don mu riƙa ‘gargaɗar da juna; balle fa yanzu, da muna ganin ranan nan tana gusowa.’

17 Yesu bai ɗauki halartan taro da wasa ba a lokacin da yake matashi. A lokacin da yake shekara 12, ya bi iyayensa zuwa wani babban taro. Ana nan a wurin wannan babban taron sai aka rasa inda Yesu yake. Shin ya je wurin ’yan’uwansa matasa ne? A’a. Maimakon haka, iyayensa sun same shi a haikali yana tattaunawa da manyan malamai.—Luk. 2:45-47.

18. Ta yaya addu’o’inmu za su inganta haɗin kanmu?

18 Ban da ƙauna da ƙarfafa junanmu a taro, za mu iya yi wa juna addu’a. Idan muka ambaci wasu abubuwa na musamman a madadin ’yan’uwanmu sa’ad da muke addu’a, hakan yana inganta ƙaunarmu ga juna. Ba Kiristoci da suka manyanta kawai ba ne za su riƙa yin hakan. Idan kai matashi ne, kana yin amfani da waɗannan zarafin don ka ƙarfafa dangantakarka da ’yan’uwanka? Yin hakan zai sa ka kasance da tabbaci cewa za ka sami ceto a lokacin da za a halaka wannan muguwar duniyar.

YADDA ZA MU NUNA CEWA MU “GAƁAƁUWA NE NA JUNANMU”

19-21. (a) A wace hanya ta musamman ce muke nuna cewa ‘dukanmu gaɓaɓuwa ne na junanmu’? Ka ba da misali. (b) Wane darasi ne muka koya daga yadda wasu ’yan’uwa suka taimaka a lokacin bala’i?

19 Bayin Jehobah suna bin ƙa’idar da ke Romawa 12:5 da ta ce: ‘Dukanmu gaɓaɓuwa ne na junanmu.’ Ana ganin tabbacin hakan a lokacin da bala’i ya auku. An yi wata guguwar ruwa da iska da ta jawo ambaliya a tsibirin Mindanao a ƙasar Filifin, a Disamba na shekara ta 2011. Ruwa ya mamaye gidaje fiye da 40,000 a dare ɗaya kuma hakan ya haɗa da gidajen ’yan’uwanmu da yawa. Ofishin Shaidun Jehobah da ke ƙasar ta ba da rahoto cewa, “’Yan’uwa daga wasu wurare sun yi ta tura kayan agaji kafin kwamitin da ke ba da kayan agaji su iso.”

20 Hakazalika, a lokacin da aka yi wata gagarumar girgizar ƙasa da tsunami a gabashin Japan, ’yan’uwanmu da yawa sun yi asarar kayayyakinsu. Wasu sun tsira da rayukansu ne kawai. Wata ’yar’uwa mai suna Yoshiko ta yi asarar gidanta da ke wajen kilomita 40 daga Majami’ar Mulki. Ta ce: “Daga baya, mun yi mamakin sanin cewa mai kula da da’ira da kuma wani ɗan’uwa sun zo nemanmu washegari bayan girgizar ƙasar.” Ta yi murmushi kuma ta ce: “Mun yi godiya sosai da yadda ’yan’uwa a ikilisiya suka ƙarfafa mu don mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Ƙari ga haka, sun ba mu kwat da takalma da jakunkuna da kuma rigunan barci.” Wani Ɗan’uwa da ke kwamitin ba da kayan agaji ya ce: “’Yan’uwa da ke ƙasar Japan sun nuna haɗin kai wajen taimaka wa juna. Har wasu ’yan’uwa daga ƙasar Amirka sun zo don su taimaka. Sa’ad da aka tambaye su dalilin da ya sa suka yi wannan doguwar tafiyar, sun ce: ‘Muna da haɗin kai da ’yan’uwanmu da ke Japan, kuma suna bukatar taimako.’” Shin, ba ka farin cikin kasancewa cikin ƙungiyar Jehobah da take kula da membobinta? Ka tabbata cewa Jehobah yana jin daɗin ganin yadda muke nuna haɗin kai ga junanmu.

21 Kasancewa da irin wannan halin yanzu zai taimaka mana mu kasance da haɗin kai lokacin da muke fuskantar mawuyacin yanayi a nan gaba ko da muna nesa daga wasu ’yan’uwanmu da ke wasu ƙasashe. Hakika, irin wannan halin zai horar da mu don mu iya jimre mawuyacin yanayi da wataƙila za mu fuskanta yayin da ƙarshen wannan zamanin yake gabatowa. Wata ’yar’uwa mai suna Fumiko da ta tsira daga wata guguwar iska da ta auku a Japan, ta ce: “Ƙarshen ya yi kusa sosai. Don haka, ya kamata mu riƙa taimaka wa ’yan’uwanmu yayin da muke jiran lokacin da za a kawo ƙarshen bala’i.”

22. Ta yaya haɗin kai da ’yan’uwa zai taimaka mana a nan gaba?

22 ’Yan’uwa, yara da manya da suke ƙoƙarin kasancewa da haɗin kai yanzu suna shirin tsira ma wannan muguwar duniya da babu haɗin kai. Allahnmu zai ceci mutanensa kamar yadda ya yi a dā. (Isha. 52:9, 10) Ya kamata ka riƙa tunawa cewa za ka iya zama cikin waɗanda za a cece su idan ka yi ƙoƙarin kasancewa da mutanen Allah masu haɗin kai. Wani abu kuma da zai taimaka mana shi ne nuna godiya ga abin da muka samu. Za a tattauna wannan batun a talifi na gaba.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba