Gabatarwa
MENE NE RA’AYINKA?
Rayuwa a duniyar nan tana cike da matsaloli. Shin akwai inda za mu iya samun taimako da kuma ƙarfafa?
Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Uban jiyejiyenƙai, Allah na dukan ta’aziyya; yana mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.’—2 Korintiyawa 1:3, 4.
Wannan talifin Hasumiyar Tsaro ya tattauna yadda Allah yake ƙarfafa mu.