Ka Kusaci Allah
“Allah na Dukan Ta’aziyya”
ABUBUWA masu yawa a rayuwa kamar su wahala, sanyin gwiwa, da kewa suna iya jawo baƙin ciki, har ma su kai ga fid da zuciya. A irin waɗannan yanayin kana iya tambaya, ‘Ina zan sami taimako?’ Kalmomin manzo Bulus da ke 2 Korinthiyawa 1:3, 4 suna nuni ne ga wani tushen ta’aziya da ba ya kasawa, wato Jehobah Allah.
A aya ta 3, an kira Allah “Uban jiyejiyenƙai.” Menene hakan ke nufi? Kalmar Hellenanci da aka fasara “jiyejiyenƙai” tana iya nufin yin juyayi domin wahala da wasu suke sha. Wani bincike na Littafi Mai Tsarki da aka yi ya nuna cewa kalmar tana iya nufin “jin tausayi” ko kuma “kulawa sosai.” ‘Jiyejiyenƙai’ na Allah ne ke motsa shi ya aikata wani abu.a Fahimtar wannan fasali na halin Allah yana motsa mu mu kusace shi, ko ba haka ba ne?
Bulus ya ce da Jehobah, “Allah na dukan ta’aziyya.” A nan Bulus ya yi amfani da kalmar da ta ƙunshi “sanyaya zuciyar wanda ke cikin damuwa ko wanda ke baƙin ciki da kuma ma’anar ba da taimako ko ƙarfafawa.” The Interpreter’s Bible ya yi bayani cewa: “Muna sanyaya zuciyar wanda ke cikin matsala sa’ad da muka ba shi ƙarfin zuciya ya jimre azabarsa.”
Kana iya tambaya, ‘Ta yaya Allah ke mana ta’aziya kuma ya ba da ƙarfin zuciya domin mu jimre azabarmu?’ Yana haka musamman ta wajen Kalmarsa, wato Littafi Mai Tsarki da kuma ta wajen addu’a. Bulus ya gaya mana cewa Allah ya ba mu Kalmarsa cikin ƙauna domin “ta wurin haƙuri da ta’aziyar litattafai mu zama da bege.” Bugu da kari, ta wajen yin addu’a daga zuciya muna shaida “Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka.”—Romawa 15:4; Filibbiyawa 4:7.
Yaya yawar ta’aziya da Allah ke yi wa mutanensa? Bulus ya ce Allah yana “yi mana ta’aziyya cikin dukan ƙuncinmu.” (2 Korinthiyawa 1:4) Ko da wane irin matsi, ko baƙin ciki, ko azaba muke fuskanta, Allah yana iya ba mu gaba gaɗi da kuma ƙarfi da zai taimake mu mu jimre. Wannan ba abin ƙarfafawa ba ne?
Ta’aziya da Allah ke bayarwa ba ta ƙarewa kawai a kan wanda ya karɓe ta. Bulus ya ci gaba da cewa Allah yana mana ta’aziya “har da za mu iya ta’azantarda waɗanda ke cikin kowane irin ƙunci, ta wurin ta’aziyya wadda mu da kanmu muka ta’azantu da ita daga wurin Allah.” Da yake an yi mana ta’aziyya cikin ƙuncinmu, zuciyarmu na motsa mu mu ji tausayin wasu kuma mu taimaka wa mabukata.
Ko da yake shi “Allah na dukan ta’aziyya” ne, ba lallai ba ne Jehobah ya sa dukan wahalarmu ko azabarmu su ƙare ba. Amma da wani abin tabbaci: Idan muka juya gareshi domin ta’aziyya, zai ƙarfafa mu mu jimre wa kowane ɓakin ciki ko damuwa da muke fuskanta. Hakika, Allahn nan mai juyayi ya cancanci mu bauta masa kuma mu yaba masa.
[Hasiya]
a An kira Allah “Uban [ko tushen] jiyejiyenƙai.” Shi ne mafarin Jiyejiyenƙai kuma halinsa ne.