Gabatarwa
MENE NE RA’AYINKA?
A cikin dukan kyaututtuka da Allah ya ba mu, wanne ne ya fi daraja?
Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya, ya ba da makaɗaicin Ɗansa.’—Yohanna 3:16, Littafi Mai Tsarki.
Wannan talifin ya nuna dalilin da ya sa Allah ya aiko Yesu duniya don ya mutu a madadinmu da kuma yadda za mu nuna godiya don kyautar.