Kai Za Ka Zaɓi Yadda Rayuwarka Za Ta Kasance a Nan Gaba!
SHIN ZA KA IYA ZAƁAN YADDA RAYUWARKA ZA TA KASANCE A NAN GABA? Wasu sun gaskata cewa duk abin da ya faru da mu a rayuwa kadara ce, don haka, ba mu da zaɓi game da hakan. Idan ba su cim ma wani abin da suke so ba, sai su ce, “Ba mu da zaɓi don haka Allah ya kadara.”
Wasu suna baƙin ciki sosai idan ba su iya magance matsaloli da rashin adalcin da muke fuskanta a duniya ba. Sun yi ƙoƙarin kyautata rayuwarsu amma abubuwa kamar su yaƙi da bala’i da rashin lafiya sun sa ba su iya yin hakan ba. Saboda haka, sun karaya kuma suka fid da rai game da rayuwa.
A gaskiya, matsalolin rayuwa suna iya ɓata wasu abubuwan da kake burin yi. (Mai Wa’azi 9:11) Amma idan ya zo ga batun rayuwarka a nan gaba, kai ne za ka tsai da shawara. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kai ne za ka zaɓi yadda kake son rayuwarka ta kasance a nan gaba. Ka ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce.
Sa’ad da Isra’ilawa suke gab da shiga Ƙasar Alkawari, Musa, wanda ya ja-gorance su ya gaya musu cewa: “Na shimfiɗa a gabanku rai da mutuwa, albarka da la’ana. Ku zaɓi rai domin ku da zuriyarku ku rayu. Ku ƙaunaci Yahweh Allahnku, ku yi masa biyayya, ku manne masa.”—Maimaitawar Shari’a 30:15, 19, 20.
Hakika, Allah ya ceci Isra’ilawa daga hannun mutanen Masar kuma ya yi musu alkawari cewa za su ji daɗin rayuwa a Ƙasar Alkawari. Amma akwai abin da suke bukatar su yi don su more wannan albarkar. Suna bukatar su “zaɓi rai.” Ta yaya za su yi hakan? Ta wurin ‘ƙaunar Yahweh Allahnsu, su yi masa biyayya, su manne masa’ kuma.
A yau ma, kana da zaɓin da za ka yi kuma zaɓin zai shafi yadda rayuwarka za ta kasance a nan gaba. Idan ka ƙaunaci Allah, ka saurare shi kuma ka zama amininsa, hakan yana nufin cewa ka zaɓi yin rayuwa har abada a aljanna a nan duniya. Amma mene ne ƙaunar Allah da saurarar sa da kuma zama amininsa suka ƙunsa?
KA ƘAUNACI ALLAH
Ƙauna ita ce hali na farko mai muhimmanci da Allah yake da shi. Shi ya sa manzo Yohanna ya ce, “Allah ƙauna ne.” (1 Yohanna 4:8) Da aka tambayi Yesu wacce ce doka mafi muhimmanci, ya ce: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka.” (Matiyu 22:37) Idan kana so ka kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah Allah, wajibi ne ka ƙaunace shi da dukan zuciyarka ba wai don kana tsoron sa ko kuma ka rasa na yi ba. Amma me ya sa yake da muhimmanci mu ƙaunace shi da son ranmu?
Kamar yadda iyaye suke ƙaunar yaransu, haka ma Jehobah yake ƙaunar ’yan Adam. Ko da yake iyaye ajizai ne, suna ƙaunar yaransu, shi ya sa suke koyar da su da ƙarfafa su da taimaka musu da kuma yi musu horo. Suna yin hakan don suna son yaran su yi farin ciki kuma su yi nasara a rayuwa. Mene ne iyaye kuma suke son yaransu su yi musu? Suna son yaransu su ƙaunace su kuma su bi shawarwarin da suka ba su don su amfana. Ba ka ganin ya dace mu ƙaunaci Ubanmu na sama don dukan abubuwa masu kyau da ya ba mu?
KA SAURARI ALLAH
A asalin yaren da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “saurara” ta ƙunshi yin “biyayya.” Idan muka gaya wa yaro, “Ka riƙa saurarar iyayenka,” muna nufin ya riƙa yi wa iyayensa biyayya, ko ba haka ba? Don haka, saurarar Allah tana nufin mu riƙa yi masa biyayya. Tun da Allah ba ya magana da mu gar-da-gar, muna saurarar sa ta wajen karanta da kuma bin umurninsa da ke Littafi Mai Tsarki.—1 Yohanna 5:3.
Yesu ya nuna muhimmancin saurarar Allah sa’ad da ya ce: “Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga wurin Allah.” (Matiyu 4:4) Ko da yake abinci yana da muhimmanci sosai a gare mu, koyan Kalmar Allah ya fi abinci muhimmanci. Me ya sa? Sarki Sulemanu mai hikima ya ce: “Gama hikima takan tsare mutum kamar yadda kuɗi yakan yi. Hikima takan kiyaye ran mai ita, wannan ita ce amfanin sani.” (Mai Wa’azi 7:12) Kasancewa da hikima da kuma ilimin Littafi Mai Tsarki za su taimaka mana sosai. Ban da haka, za mu iya yin zaɓi mai kyau wanda zai kai mu ga samun rai na har abada.
KA ZAMA AMININSA
Ka tuna da kwatancin Yesu da muka ambata a talifin baya. Yesu ya ce: “Ƙofar zuwa rai, ƙarama ce. Hanyarta kuma da wuyar bi. Masu bin ta kuma ba sa da yawa.” (Matiyu 7:13, 14) Idan muna bin wannan hanyar, babu shakka za mu bukaci wani da ya san hanyar sosai don ya ja-gorance mu mu isa inda za mu je. Don haka, yana da muhimmanci mu zama aminan Allah. (Zabura 16:8) Amma ta yaya za mu yi hakan?
A kowace rana, muna da abubuwa da yawa da ya wajaba mu yi da waɗanda muke so mu yi. Irin waɗannan abubuwan suna iya ɗauke hankalinmu kuma su sa ba za mu sami lokacin yin abubuwan da Allah yake so mu yi ba. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa: “Ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku. Kada ku zama kamar wawaye, sai dai kamar masu hikima. Ku yi amfani da kowane zarafi na yin kirki, gama kwanakin da muke ciki yanzu mugaye ne.” (Afisawa 5:15, 16) Za mu zama aminan Allah idan muka ɗauki yin ibadarmu da muhimmanci fiye da kowane abu.
KAI NE ZA KA YI ZAƁIN
Ko da yake ba za ka iya gyara irin rayuwar da ka yi a dā ba, amma za ka iya tsai da shawarar kyautata rayuwarka da na iyalinka a nan gaba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Ubanmu na sama, wato Jehobah yana ƙaunar mu sosai kuma ya gaya mana abubuwan da yake so mu riƙa yi. Ka ga abin da annabi Mika ya ce:
“A’a, ya kai ɗan Adam, Yahweh ya riga ya nuna maka abin da yake mai kyau. Ya faɗa maka abin da yake nema daga gare ka. Abin da yake nema shi ne ka yi adalci, ka ƙaunaci yin jin ƙai, ka yi tafiyarka da Allahnka cikin sauƙin kai.”—Mika 6:8.
Za ka amince ka bauta wa Jehobah don ka sami albarkar da zai yi maka? Kai ne za ka yi zaɓin!
“Na shimfiɗa a gabanku rai da mutuwa, albarka da la’ana. Ku zaɓi rai.”—Maimaitawar Shari’a 30:19