‘Ka Zaɓi Rai Domin Ka Rayu’
“Na sa rai da mutuwa a gabanka, albarka da la’ana: ka zaɓi rai fa, domin ka rayu.”—KUBAWAR SHARI’A 30:19.
1, 2. A wace hanya ce aka halicci mutum a cikin surar Allah?
“BARI mu yi mutum a cikin surarmu, bisa ga kamaninmu.” Wannan abin da Allah ya ce yana rubuce cikin surar farko na Littafi Mai Tsarki. Hakanan, “Allah fa ya halitta mutum cikin suratasa, cikin surar Allah ya halicce shi,” in ji Farawa 1:26, 27. Saboda haka mutum na farko ya bambanta da dukan wasu halittu da suke duniya. Yana kama da Mahaliccinsa, yana iya nuna halaye irin na Allah a tunaninsa, wajen nuna ƙauna, shari’a, hikima, da iko. Yana da lamiri da zai taimake shi ya yanke shawarar da za ta amfane shi ta kuma faranta wa Ubansa na samaniya rai. (Romawa 2:15) A taƙaice, Adamu yana da yancin yin zaɓe. Jehobah ya lura da siffar ɗansa na duniya, ya ce game da shi: “Yana da kyau ƙwarai.”—Farawa 1:31; Zabura 95:6.
2 Mu ’ya’yan Adamu ma, an yi mu cikin sura da kuma kamanin Allah ne. Amma, muna da zaɓi kuwa a abin da muke yi? Ko da yake Jehobah yana iya sanin abin da zai faru a nan gaba, bai ƙaddara rayuwarmu da kuma ayyukanmu ba. Bai taɓa barin ƙaddara ta mallaki rayuwar ’ya’yansa na duniya ba. Domin mu fahimci muhimmancin yancinmu na zaɓe, bari mu koyi wani darassi daga al’ummar Isra’ila.—Romawa 15:4.
’Yancin Zaɓe a Isra’ila
3. Mecece doka ta farko a Dokoki Goma, kuma ta yaya Isra’ila suka zaɓi su yi biyayya?
3 “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fishe ka daga ƙasar Masar, daga gidan bauta,” Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa. (Kubawar Shari’a 5:6) A shekara ta 1513 K.Z., al’ummar Isra’ila ta sami ceto na mu’ujiza daga bauta a ƙasar Masar kuma saboda haka ba su da wani dalilin shakkar waɗannan kalmomi. A doka ta farko cikin Dokoki Goma, ta bakin kakakinsa Musa, Jehobah ya ce: “Ba za ka yi waɗansu alloli ba sai ni.” (Fitowa 20:1, 3) A wannan lokaci, al’ummar Isra’ila ta zaɓi ta yi biyayya. Da son ransu suka bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya.—Fitowa 20:5; Litafin Lissafi 25:11.
4. (a) Wane zaɓe Musa ya saka a gaban Isra’ilawa? (b) Wane zaɓe muke fuskanta a yau?
4 Bayan shekara 40, Musa ya tuna wa wata tsara ta Isra’ilawa zaɓin da ke gabansu. “Ina kira sama da ƙasa su shaida a kanku yau,” in ji shi, “na sa rai da mutuwa a gabanka, albarka da la’ana: ka zaɓi rai fa, domin ka rayu, da kai da zuriyarka.” (Kubawar Shari’a 30:19) Hakazalika a yau, muna da ’yancin zaɓe. Hakika, muna iya zaɓan ko mu bauta wa Jehobah cikin aminci da begen rai madawwami, ko kuma mu yi rashin biyayya mu fuskanci sakamakon haka. Ka yi la’akari da misalin mutane biyu da zaɓinsu ya bambanta.
5, 6. Wane zaɓi ne Joshua ya yi kuma menene sakamakon haka?
5 A shekara ta 1473 K.Z., Joshua ya kai Isra’ilawa Ƙasar Alkawari. A gargaɗi da ya yi kafin ya mutu, Joshua ya shawarci al’ummar: ‘Idan a gareku mummunan abu ne ku bauta ma Ubangiji, ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa; ko alloli na ƙetaren Kogin, waɗanda ubanninku suka bauta ma, ko kuwa alloli na Amoriyawa waɗanda ku ke zaune a cikin ƙasarsu.’ Sai ya yi magana game da iyalinsa, kuma ya ci gaba yana cewa: “Amma da ni da gidana, Ubangiji za mu bauta ma.”—Joshua 24:15.
6 Kafin wannan lokaci, Jehobah ya aririci Joshua ya yi ƙarfi ya yi gaba gaɗi, ya umurce shi kada ya ƙauce daga yi wa Dokar Allah biyayya. Maimakon haka, ta wajen karanta littafin Dokoki dare da rana, Joshua zai yi nasara a al’amuransa. (Joshua 1:7, 8) Kuma hakan ya kasance. Zaɓin da Joshua ya yi ya sa ya sami albarka. “Cikin dukan alherin da Ubangiji ya yi zancensa ga gidan Isra’ila babu wani abin da ya sare,” in ji Jeshua. “Dukan abu ya tabbata.”—Joshua 21:45.
7. A zamanin Ishaya, wane zaɓe ne wasu Isra’ilawa suka yi, kuma menene sakamakon haka?
7 Akasarin haka, ka yi la’akari da yanayin da ya kasance a Isra’ila shekaru 700 bayan haka. A wannan lokacin, Isra’ilawa da yawa suna bin al’adun arna. Alal misali, a rana ta ƙarshe ta shekara, mutane suna taruwa domin liyafa na abinci mai kyau da giya mai daɗi. Wannan ba liyafa ba ce kawai ta iyali. Maimakon haka, biki ne na addini da yake ɗaukaka wasu allolin arna guda biyu. Annabi Ishaya ya rubuta ra’ayin Allah game da wannan aikin rashin aminci: “Ku da ke yasda Ubangiji, kuna manta da dutsena mai-tsarki, ku da ke shirya [tabur] domin Gad, ku da ke dama ruwan anab ga Meni ku cika.” Sun gaskata cewa girbin amfanin gona bai dangana ga albarkar Jehobah ba, amma a kan bauta wa allan ƙaddara “Gad” da kuma na sa’a “Meni.” Amma a gaskiya, hanyarsu ta tawaye ta kafa ƙaddararsu. “Zan ƙaddara ku ga kaifin takobi,” in ji Jehobah, “dukanku kuma za ku sunkuya ga yanka; domin sa’anda na kira, ba ku amsa ba: sa’anda na yi magana, ba ku ji ba; amma kun yi abin da ke mugu a idona, kuka zaɓi abin da ban ji daɗinsa ba.” (Ishaya 65:11, 12) Zaɓinsu na rashin hikima ya jawo musu halaka, kuma allolin ƙaddara da na sa’a ba su da iko su hana.
Zaɓen da Ya Dace
8. Dangane da Kubawar Shari’a 30:20, menene yin zaɓe mai kyau ya ƙunsa?
8 Sa’ad da Musa ya shawarci Isra’ilawa su zaɓi rai, ya gaya musu matakai uku da za su ɗauka: ‘Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku ji muryatasa, ku manne masa.’ (Kubawar Shari’a 30:20) Bari mu bincika dukan waɗannan ɗaiɗai domin zaɓenmu ya kasance da kyau.
9. Ta yaya za mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah?
9 Ta wurin ƙaunar Jehobah Allahnmu: Mun zaɓi mu bauta wa Jehobah ne domin muna ƙaunarsa. Bin misalan gargaɗi na zamanin Isra’ilawa, muna guje wa dukan jaraba mu yi lalata kuma muna guje wa salon rayuwa da zai sa mu faɗa cikin tarkon duniya na tara dukiya. (1 Korinthiyawa 10:11; 1 Timothawus 6:6-10) Muna manne wa Jehobah kuma muna kiyaye farillansa. (Joshua 23:8; Zabura 119:5, 8) Kafin Isra’ilawa su shiga Ƙasar Alkawari, Musa ya yi musu gargaɗi: “Ga shi, na koya maku farillai da shari’u, kamar yadda Ubangiji Allahna ya umurce ni, domin ku yi su cikin ƙasa da za ku tafi garin ku ci ta. Ku kiyaye su fa ku aikata; gama hikimarku da azancinku ke nan a idanun al’ummai, waɗanda za su ji dukan waɗannan farillai.” (Kubawar Shari’a 4:5, 6) Yanzu ne lokaci da ya kamata mu nuna ƙaunarmu ga Jehobah ta wajen saka nufinsa farko a rayuwarmu. Babu shakka za mu sami albarka idan muka zaɓi mu yi haka.—Matta 6:33.
10-12. Wane darasi muka koya daga yin la’akari da abin da ya faru da zamanin Nuhu?
10 Ta wajen jin muryatasa: Nuhu “mai-shelan adalci” ne. (2 Bitrus 2:5) Kusan dukan mutane da suka rayu kafin Rigyawa sun shagala cikin ayyukansu saboda haka ba su lura da gargaɗin Nuhu ba. Menene sakamakon haka? “Rigyawa ta zo ta kwashe su duka.” Yesu ya yi gargaɗi cewa a zamaninmu, lokacin “bayanuwar ɗan mutum,” za ta zama haka. Abin da ya faru a zamanin Nuhu gargaɗi ne mai tsanani ga mutanen yanzu waɗanda suka ƙi zaɓan su bi saƙon Allah.—Matta 24:39.
11 Waɗanda suke wa gargaɗin Allah ta bakin bayinsa na zamani ba’a, ya kamata su fahimci abin da ƙin bin wannan gargaɗi zai nufa a garesu. Game da waɗannan masu ba’a, manzo Bitrus ya rubuta: “Gama da gangan su ke manta da wannan, akwai sammai tun dā, da duniya kuma a tattare daga bisa ruwa, cikin tsakiyar ruwa kuma, bisa ga maganar Allah; bisa ga wannan fa duniya wadda ta ke a sa’an nan, yayinda ruwa ya sha kanta, ta halaka: amma sammai da su ke yanzu, da duniya kuma, bisa ga wannan magana kanta an tanaje su domin wuta, ajiyayyu zuwa ranar shari’a da halakar mutane masu-fajirci.”—2 Bitrus 3:3-7.
12 Ka gwada wannan da zaɓi da Nuhu da iyalinsa suka yi. “Ta bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al’amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi.” (Ibraniyawa 11:7) Bin gargaɗin ya sa ya ceci iyalinsa. (Ibraniyawa 11:7) Bari mu kasance da hanzarin jin saƙon Allah kuma mu yi biyayya da shi.—Yaƙub 1:19, 22-25.
13, 14. (a) Me ya sa ‘manne wa Jehobah’ yake da muhimmanci? (b) Ta yaya za mu ƙyale Jehobah “mai-yin tukwane da mu” ya mulmule mu?
13 Ta wajen manne wa Jehobah: ‘Zaɓan rai domin a rayu,’ ya ƙunshi fiye da ƙauna da kuma sauraron Jehobah, ya kuma ƙunshi ‘manne wa Jehobah,’ wato, nacewa a yi nufinsa. “Jurewarku ce za ta fisshe ku,” in ji Yesu. (Luka 21:19) Hakika, zaɓin da muka yi game da wannan zai bayyana abin da ke cikin zuciyarmu. Misalai 28:14 ta ce: “Mai-farinciki ne mutum wanda ya ke jin tsoro kullum: Amma shi wanda ya taurare zuciyassa za ya fāɗi cikin masifa.” Fir’auna na ƙasar Masar ta dā misali ne a wannan. Sa’ad da kowane annoba cikin annoba goma ya faɗa wa Masar, Fir’auna sai ya taurara zuciyarsa maimakon ya nuna tsoron Allah. Ba Jehobah ba ne ya tura Fir’auna cikin rashin biyayya amma ya ƙyale sarkin nan mai fahariya ne ya zaɓa. Ko yaya dai, an cika nufin Jehobah, kamar yadda manzo Bulus ya yi bayani game da yadda Jehobah ya ɗauki Fir’auna: “Saboda wannan nufi da kansa na tashe ka, domin in gwada ikona a cikinka, labarin sunana kuma shi watsu cikin dukan duniya.”—Romawa 9:17.
14 Shekaru ɗarurruwa bayan ceton Isra’ilawa daga hannun Fir’auna, annabi Ishaya ya ce: “Ya Ubangiji, kai ubanmu ne, mu yimɓu ne, kai ne mai-yin tukwane da mu: mu dukanmu kuma aikin hannunka ne.” (Ishaya 64:8) Sa’ad da muka ƙyale Jehobah ya mulmule mu ta wurin nazari da kuma bin Kalmarsa, a hankali sai mu yafa sabon hali. Sai mu zama masu tawali’u masu sauƙin hali, sai ya kasance da sauƙi a garemu mu manne wa Jehobah cikin aminci domin da gaske muna so mu faranta masa zuciya.—Afisawa 4:23, 24; Kolossiyawa 3:8-10.
‘Sanar da Su’
15. In ji Kubawar Shari’a 4:9, waɗanne hakki biyu ne Musa ya tuna wa Isra’ilawa?
15 Ga al’ummar Isra’ila da ta taru, tana shirye ta shiga Ƙasar Alkawari, Musa ya ce: “Ka yi lura da kanka, ka kiyaye ranka da ƙwazo, domin kada ka manta da al’amuran da idanunka suka gani, kada kuma su rabu da zuciyarka dukan kwanakin ranka; amma ka sanar ma ’ya’yanka da su da ’ya’yan ’ya’yanka.” (Kubawar Shari’a 4:9) Domin su sami albarkar Jehobah kuma su bunƙasa a ƙasar da za su gada, dole ne mutanen su cika hakkinsu biyu ga Jehobah Allahnsu. Ba za su manta da ayyukan al’ajabi da Jehobah ya yi a gaban idanunsu ba, kuma dole ne su koyar da su ga jikokinsu. Dole ne mutanen Allah su yi haka a yau, idan muna so mu ‘zaɓi rai domin mu rayu.’ Menene muka gani da idanunmu da Jehobah ya yi dominmu?
16, 17. (a) Menene masu wa’azi a ƙasashen waje da aka koyar da su a Gileyad suka cim ma a wa’azin Mulki? (b) Wane misali ne na ƙwazo ka sani?
16 Muna farin cikin ganin yadda Jehobah ya albarkaci aikinmu na wa’azi da almajirantarwa. Tun da aka buɗe Makarantar Littafi Mai Tsarki ta Gileyad a shekara ta 1943, masu wa’azi a ƙasashen waje sun yi ja-gora wajen aikin almajirantarwa a ƙasashe masu yawa. Har zuwa yanzu, ɗaliban makaranta na farko suna da ƙwazo wajen wa’azin Mulki, ko da yake sun tsufa kuma wasu suna da matsalolin ƙoshin lafiya. Wata misali mai kyau Mary Olson ce, da ta sauke karatu daga Gileyad a shekara ta 1944. Ta yi hidimar mai wa’azi a ƙasashen waje da farko a Uruguaye, sai kuma a Kolombiya, a yanzu kuma a Puerto Rico. Ko da yake matsalolin tsufa sun rage abin da take yi, ’Yar’uwa Olson ta kasance da ƙwazo wajen wa’azi. Tana amfani da iliminta na harshen Sfanisanci, ta tsara lokaci tana fita wa’azi da ’yan’uwa kowane mako.
17 Ko da yake yanzu gwauruwa ce, ’Yar’uwa Nancy Porter, da ta sauke karatu a Gileyad a shekara ta 1947, har yanzu tana hidima a Bahamas. Ita ma wata mai wa’azi ce a ƙasashen waje da ta shagala wajen aikin wa’azi. “Koyar da wasu gaskiya ta Littafi Mai Tsarki, hanyar samun farin ciki ne na musamman,” in ji ’Yar’uwa Porter a tarihin rayuwarta.a “Ya sa na kasance da tsari a ayyukana na ruhaniya kuma ya tallafa wa rayuwata.” Sa’ad da ’Yar’uwa Porter da wasu masu aminci suke tuna baya, ba sa mantawa da abin da Jehobah ya yi. Mu kuma fa? Muna godiya domin yadda Jehobah ya albarkaci hidimar Mulki a unguwarmu?—Zabura 68:11.
18. Menene za mu koya daga karanta tarihin rayuwar masu wa’azi a ƙasashen waje?
18 Muna farin ciki domin abin da waɗannan da suka yi shekaru masu yawa suna hidima suka cim ma. Karanta tarihin rayuwarsu yana ƙarfafa mu domin sa’ad da muka ga abin da Jehobah ya yi wa waɗannan mutane masu aminci, yana ƙarfafa tabbacinmu mu bauta wa Jehobah. Kana karanta kuma ka yi bimbini a kan irin waɗannan labarai masu ban sha’awa da aka buga a Hasumiyar Tsaro kuwa?
19. Ta yaya iyaye Kiristoci za su yi amfani da tarihin rayuwar wasu da ke rubuce cikin Hasumiyar Tsaro da kyau?
19 Musa ya tuna wa Isra’ilawa cewa kada su mance dukan abin da Jehobah ya yi musu, kuma kada wannan ya fita daga zuciyarsu a dukan kwanan ransu. Sai kuma ya ce: “Ka sanar ma ’ya’yanka da su da ’ya’yan ’ya’yanka.” (Kubawar Shari’a 4:9) Tarihin rayuwa yana da ban sha’awa. Matasa da suke tasowa suna bukatar misali mai kyau. ’Yan’uwa mata marasa aure suna iya koyon darasi daga misalan ’yan’uwa mata tsofaffi waɗanda suka ba da tarihin rayuwarsu a Hasumiyar Tsaro. Hidima a yankin wani yare a ƙasarsu tana ba da zarafin faɗaɗa zarafin shagala cikin wa’azin bishara ga ’yan’uwa maza da mata. Iyaye Kiristoci, me ya sa ba za ku yi amfani da misalan masu wa’azi a ƙasashen waje da kuma wasu su motsa ’ya’yanku su zaɓi hidima ta cikakken lokaci ba?
20. Menene za mu yi domin mu “zaɓi rai”?
20 To, ta yaya kowanenmu zai iya “zaɓan rai”? Ta wajen amfani da kyauta ta ’yanci mu nuna wa Jehobah cewa muna ƙaunarsa da kuma ta wajen ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu a hidimarsa har iyaka yadda ya ƙyale mana wannan gatar. “Domin” kamar yadda Musa ya ce, Jehobah “shi ne ranka, da tsawon kwanakinka.”—Kubawar Shari’a 30:19, 20.
[Hasiya]
a Dubi “Joyous and Thankful Despite Heartbreaking Loss,” da aka bugu a cikin Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuni, 2001, shafuffuka na 23-27 na Turanci.
Ka Tuna?
• Menene ka koya daga misalan zaɓe dabam dabam da muka yi la’akari da su?
• Waɗanne matakai ne dole mu ɗauka domin mu “zaɓi rai”?
• Waɗanne hakki ne biyu aka aririce mu mu cika?
[Hoto a shafi na 24]
“Na sa rai da mutuwa a gabanka”
[Hoto a shafi na 27]
Sauraron muryar Allah ya kawo wa Nuhu da iyalinsa ceto
[Hoto a shafi na 28]
Mary Olson
[Hoto a shafi na 28]
Nancy Porter