Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 1/1 p. 21
  • Jehobah Ya Ba Mu Zaɓi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jehobah Ya Ba Mu Zaɓi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Ka Zaɓi Rai Domin Ka Rayu’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Kai Za Ka Zaɓi Yadda Rayuwarka Za Ta Kasance a Nan Gaba!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
  • Menene Jehobah Yake Bukata a Gare Mu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Musa—Mutumi Ne Mai Ƙauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 1/1 p. 21

Ka Kusaci Allah

Jehobah Ya Ba Mu Zaɓi

Kubawar Shari’a 30:11-20

“NAKAN ji tsoro marar kyau cewa zan yi rashin aminci ga Jehobah.” In ji wata mata Kirista wadda take jin cewa abubuwan da ta aikata sa’ad da take ƙarama za su sa ta yi laifi. Hakan gaskiya ne? Waɗannan kalamai na sama gaskiya ne kuwa? A’a. Jehobah Allah ya ba mu baiwar ’yancin zaɓi, don mu samu yin zaɓin kanmu game da yadda muke son mu yi rayuwa. Jehobah yana son mu yi zaɓi mai kyau, kuma Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki, ya gaya mana yadda za mu yi hakan. Ka yi la’akari da kalaman Musa, kamar yadda suke a Kubawar Shari’a sura 30.

Shin yana da wuya mu san abin da Allah yake bukata a gare mu kuwa?a Musa ya ce: “Wannan doka wadda na dokace ka da ita yau, ba ta fi ƙarfinka ba, ba ta kuwa da nisa.” (Aya ta 11) Jehobah ba ya bukatar abin da ba za mu iya yi ba. Farillansa masu sauƙi ne kuma za mu iya yin su. Kuma za mu iya sanin farillansa. Ba ma bukata mu haura “cikin sama” ko kuma mu tafi “gaba da teku” don mu koyi abubuwan da Allah yake bukata a gare mu. (Ayoyi na 12, 13) Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana dalla-dalla yadda za mu yi rayuwa.—Mikah 6:8.

Amma, Jehobah ba ya tilasta mana mu bauta masa. Musa ya ce: “A gabanka yau na sa rai da nagarta, mutuwa da mugunta.” (Aya ta 15) Muna da ’yancin zaɓan rai da mutuwa, nagarta da mugunta. Za mu iya zaɓan mu bauta wa Allah kuma mu yi masa biyayya don samun lada, ko kuma za mu iya zaɓan ƙin yi masa biyayya kuma mu fuskanci sanadin yin hakan. Ko yaya, zaɓin namu ne.—Ayoyi ta 16-18; Galatiyawa 6:7, 8.

Jehobah ya damu da zaɓin da muka yi kuwa? Hakika, ya damu! Ta huriyar Allah, Musa ya ce: “Ka zaɓi rai fa.” (Aya ta 19) Ta yaya za mu zaɓi rai? Musa ya bayyana: “Garin ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka, ka ji muryatasa, ka manne masa.” (Aya ta 20) Idan mun soma ƙaunar Jehobah, za mu so mu yi biyayya da shi kuma mu manne masa da aminci, ko me ya faru. Ta wannan hanyar, za mu zaɓi rai, hanya mafi kyau ta rayuwa da niyar samun rai na har abada a sabuwar duniya ta Allah mai zuwa.—2 Bitrus 3:11-13; 1 Yohanna 5:3.

Kalaman Musa sun koya mana gaskiya mai ba da tabbaci. Ko menene ka taɓa fuskanta a wannan muguwar duniya, ba zaka kaɗaita ba, kuma ba za ka kasa ba. Jehobah ya ɗaukaka ka da baiwar yin zaɓi. E, za ka iya zaɓi ka ƙaunaci Jehobah, ka yi biyayya da shi, kuma ka yi imani da shi. Idan ka yi irin wannan zaɓin, Jehobah zai albarkaci ƙoƙarce-ƙoƙarcenka.

Wannan gaskiyar, wato, cewa muna da ’yancin zaɓar mu ƙaunaci da kuma bauta wa Jehobah ya ƙarfafa matar da aka ambata da farko. Ta ce: “Ina ƙaunar Jehobah. A wasu lokatai, nakan manta cewa abu mafi muhimmanci shi ne cewa ina ƙaunar Jehobah. Don hakan zan iya kasancewa da aminci.” Da taimakon Jehobah, za ka yi hakan.

[Hasiya]

a Ka duba talifin nan “Ka Kusaci Allah—Menene Jehobah Yake Bukata a Gare Mu?” a Hasumiyar Tsaro ta Janairu-Maris 2010.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba