Mene Ne Mulkin Allah?
Mutane da dama suna addu’a Mulkin Allah ya zo, amma me ake nufi da Mulkin Allah? Kuma mene ne mulkin zai yi wa ’yan Adam?
GA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE:
Mene ne Mulkin Allah?
Gwamnati ce a sama, kuma Yesu Kristi ne Sarkin Mulkin.—Ishaya 9:6, 7; Matiyu 5:3; Luka 1:31-33.
Mene ne Mulkin Allah zai yi?
Zai cire mugunta kuma zai kawo zaman lafiya a ko’ina a duniya.—Daniyel 2:44; Matiyu 6:10.
Idan aka ce mutum ya biɗi Mulkin Allah farko, me ake nufi?
Ana nufin ya goyi bayan Mulkin, kuma ya yarda cewa Mulkin ne kaɗai zai sa duniya ta zama yadda Allah yake so.—Matiyu 6:33; 13:44.