Ka Taɓa Gwada Yin Nazari a Haɗuwa ta Farko?
Sa’ad da aka gabatar da nazarin Littafi Ma Tsarki a gare su, wasu masu gida sukan ce ba sa marmari ko kuma suna nazarin Littafi Mai Tsarki a cocinsu. Tun da ba su san cewa yadda muke nazarin Littafi Mai Tsarki ya bambanta da na wasu addinai ba, ba su san cewa nazarin na da kyau kuma zai wayar da kansu ba. Saboda haka, maimakon gabatar da nazari, me zai hana ka ɗauki ’yan mintoci don ka nuna musu yadda ake nazarin Littafi Mai Tsarki a haɗuwa na farko? Alal misali: Kada ka gaya musu cewa ka iya girki sosai kuma komo musu da abinci, ka ba su abincin a take su ɗanɗana! Ga yadda za ka iya yin hakan a cikin ’yan mintoci, ta wajen yin amfani da shawarar da ke shafi na 6 na Hidimarmu Ta Mulki ta Janairu 2006:
“Kana tsammanin cewa lokaci zai taɓa zuwa da waɗannan kalaman za su samu cika kuwa? [Karanta Ishaya 33:24, sai ka bari ya ba da amsa.] Bari in nuna maka wani abu mai daɗi game da batun.” Ka ba maigidan littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, sai ka ja hankalinsa ga sakin layi na 22 a shafi na 36. Ka karanta tambayar da ke ƙarƙashin shafin, sai ka tambayi maigidan ya nemi amsar yayin da kake karanta sakin layin. Ka sake yin tambayar, kuma ka saurari kalamin maigidan. Ku karanta ɗaga daga cikin nassosin tare. Ka yi tambayar da za ka amsa sa’ad da ka sake dawowa, kuma ku kafa tabbataccen lokaci na komawa. Ka riga ka soma nazarin Littafi Mai Tsarki ke nan!