Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Yuli-Satumba
“Yana wa wasu mutane wuya su amince da wasu. Kai kuma fa? [Ka bari ya ba da amsa.] Da akwai wanda za ka iya dogara da shi, da ba zai ci amanarka ba. [Karanta Misalai 3:5.] Wannan talifin ya tattauna dalilin da ya sa ya kamata mu dogara ga Jehobah.” Ka gabatar da talifin da ke shafi na 29.
Satumba
Karanta Matta 5:39. Sai ka ce: “Kana tsammani cewa Yesu yana nufin mu yi shiru sa’ad da aka yi mana laifi? [Ka bari ya ba da amsa.] Wannan talifin ya nuna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da kāre kanmu da kuma neman kāriya daga wajen hukuma.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 10.
Oktoba-Disamba
“Kana tunani cewa mutane suna bukatar mene ne don su yi farin ciki? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka buɗe Matta 5:3.] Wannan ɗaya ne daga cikin abin da Yesu ya faɗa game da batun farin ciki. Wannan talifin ya tattauna abin da muka koya daga wurin Yesu game da yadda za mu iya samun farin ciki na gaske.” Ka gabatar da talifin da ya soma daga shafi na 16.
Oktoba
“Mun saba jin cewa ma’aurata sun ci amanar junansu, ’yan siyasa sun ci amanar mutane, da kuma sauransu. Kana tsammani cewa yana daɗa wuya a samu mutane masu aminci kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa suna ji cewa wannan Nassin yana samun cikawa. [Karanta 2 Timotawus 3:1-5.] Wannan mujallar ta bayyana inda za a iya samun amintattun mutane.”