Abin da Za a Ce Game da Mujallun
Janairu-Maris
“Abokanmu suna iya shafanmu sosai. Ka amince da hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a wannan ayar. [Karanta Misalai 13:20.] Abokanmu suna iya sa mu kasance da wadar zuciya ko kuma su sa mu ƙasa yin hakan. Wannan talifin da ke shafi na 7 ya tattauna abin da zai taimake ka ka san ko ka zaɓi abokan kirki.”
Fabrairu
“Domin Littafi Mai Tsarki tsohon littafi ne, wasu suna zato cewa bayanin da ya yi a kan kimiyya ba daidai ba ne. Mene ne ra’ayinka? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa suna mamaki cewa Littafi Mai Tsarki ya faɗi wannan kalamin. [Karanta Ishaya 40:22.] Talifin da ya soma daga shafi na 22 ya amsa wannan tambayar, Shin kimiyya da Littafi Mai Tsarki sun jitu kuwa?”
Janairu-Maris
“Mutane da yawa a wasu coci a yau, suna da’awar cewa suna magana da harsuna dabam-dabam ta mu’ujiza. Kana tunani cewa irin wannan yin magana da harsuna daga wurin Allah ne? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da aka bayyana a nan. [Karanta 1 Korintiyawa 13:8.] Don ka daɗa bincika wannan batun sosai, wannan talifin da ya soma daga shafi na 29 ya tattauna wannan tambayar ‘Yin Magana a Harsuna Dabam-Dabam Ya Fito Ne Daga Wurin Allah?’”
Maris
“Muna tattauna wannan aya mai ban ƙarfafa tun da yake mutane da yawa suna fama da rashin lafiya. [Karanta Ishaya 33:24.] Yaya kake ganin cewa rayuwa za ta kasance idan wannan ayar ta samu cikawa? [Ka bari ya ba da amsa.] Kafin Allah ya kawo wannan canjin, akwai matakai da yawa da dukanmu za mu iya ɗauka don mu kyautata lafiyarmu. Wannan mujallar ta bayyana hakan.”