Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Fabrairu
“Zan so in nuna maka wata aya mai ban sha’awa a cikin Littafi Mai Tsarki. [Ka karanta Ibraniyawa 11:4.] Ta yaya Habila da ya mutu tun da daɗewa zai iya mana magana a yau?” Ka nuna wa maigidan Hasumiyar Tsaro ta Janairu-Fabrairu. Ka karanta sa’an nan ka tattauna sakin layi na 2 da 3 na talifin da ke shafi na 12 tare da mutumin. Sai ka bar wa maigidan mujallun kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna tambayar da ke sakin layi na 4.
Hasumiyar Tsaro Janairu-Fabrairu
“Wasu suna gani cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki sau da kafa zai hana su jin daɗi. Mene ne ra’ayinka game da bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a nan. [Ka karanta 2 Korintiyawa 3:17.] Labarin da ke shafuffuka na 10 da 11 a cikin wannan mujallar ya nuna cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki yana kai ga samun ’yanci na gaske.”
Awake! Fabrairu
“Mutane da yawa suna zuwa wasu ƙasashe don su more rayuwa mai kyau. Kana ganin suna yawan samun abin da suke nema? [Ka bari ya ba da amsa.] Ba sabon abu ba ne a ga mutane suna ƙaura zuwa wasu ƙasashe. Ka lura da wannan misali da ke littafin farko na Littafi Mai Tsarki. [Ka karanta Farawa 46:5, 6.] Wannan mujallar ta ba da amsa ga waɗannan tambayoyin.” Sai ka nuna wa mutumin tambayoyin da ke ƙarshen shafi na 6.