Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Satumba
“Dukanmu muna da dangi ko kuma abokai da suka rasu. Kana bege za ka sake ganinsu kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da wannan kalami mai ban ta’aziya.” Ka karanta kuma ka tattauna sashen da ke ƙarƙashin kan magana na farko da ke shafi na 26 na Hasumiyar Tsaro ta Yuli-Satumba da kuma nassi ɗaya da aka ambata a ciki. Ka ba da mujallar, kuma ka shirya ka koma ziyara don ku tattauna amsa ga tambaya ta gaba.
Hasumiyar Tsaro Yuli-Satumba
“Yana wa wasu wuya su yi amfani da kuɗi yadda ya dace. Mene ne kake tsammani zai taimaka? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a wannan ayar. [Karanta Misalai 21:5.] Ayar nan ta nuna cewa tsara yadda za a kashe kuɗi zai iya taimaka wa mutum. Wace ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce za ta iya taimaka mana mu yi amfani da kuɗin da muke da shi yadda ya dace? Wannan talifin da ya soma daga shafi na 9 ya ba da bayanai da yawa.”
Awake! Satumba
“Mutane da yawa a yau suna alhini saboda matsalar kuɗi. Me kake tsammani ya sa samun abin biyan bukata yake da wuya sosai a yau? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da kalaman hikima da suka taimaki mutane da yawa su yi amfani da kuɗaɗensu yadda ya dace. [Ka karanta nassi guda da ke cikin shafuffuka na 8-9.] Wannan mujallar ta ba da shawara mai amfani ga waɗanda ake binsu bashi.”