Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko A Watan Satumba
“Yawancin mutane suna kiran Allah da laƙabi irin su “Ubangiji” ko kuma “Maɗaukakin Sarki.” Kana ganin yana da muhimmanci ne mu riƙa yin amfani da ainihin sunan Allah? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da yadda Allah yake ji game da hakan.” [Ka karanta Ishaya 12:4.] Ka ba mutumin Hasumiyar Tsaro na Yuli-Satumba, ku tattauna tambaya ta farko da ke shafi na 26. Ka ba shi mujallar, kuma ka gaya wa mutumin cewa za ka dawo don ku tattauna tambayar da ke gaba.
Hasumiyar Tsaro Yuli-Satumba
“A kowace rana, yana kasance mana da wuya mu samu isashen abin biyan bukata. Abubuwa suna iya ƙara yin muni idan ba ma samun kuɗi kamar yadda muka saba samuwa. A ganin ka Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana a wannan yanayin? [Ka bari ya ba da amsa. Sai ka karanta 2 Timotawus 3:16, 17.] Talifin da ke shafi na 28 ya tattauna abubuwa huɗu da suka taimaka wa mutane da yawa.”
Awake! Satumba
Mutane da yawa suna ganin cewa dukan halittu da ke duniya za su halaka wata rana, mai yiwuwa sakamakon yaƙin nukiliya ko kuma wani bala’i da zai auku haka kawai saboda canjin yanayi ko kuma faɗowar manyan duwatsu daga sararin sama. Kana ganin hakan zai faru da gaske ko kuma ƙage ne kawai? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da albishiri mai ban ƙarfafa. [Karanta Zabura 37:29.] Wannan mujallar ta tattauna wasu abubuwan da mutane suke gani zai faru a Ranar Hukunci da kuma abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da abin da zai auku nan gaba.”