Yadda Za Mu Yi Wa’azi da Gaba Gaɗi a Inda Ake Kasuwanci
1. Me ya sa bai kamata mu fid da rai ba idan muna jin tsoron yin wa’azi a inda ake kasuwanci?
1 Kana jin tsoron yin wa’azi a inda ake kasuwanci? Idan haka ne, kada ka fid da rai, Bulus ma wanda manzo ne marar tsoro, ya “yi ƙarfin hali” don ya yi wa’azi. (1 Tas. 2:2) Za mu tattauna wasu ƙalubale da kuma yadda za mu magance su.
2. Me ya sa bai kamata mu damu da cewa za mu ɓata wa ma’aikatan rai ba?
2 Katse Wa Mutane Hanzari a Wurin Kasuwancinsu Zai Sa Su Fushi Ne? A yawancin wuraren da ake yin kasuwanci, waɗanda suke yin aiki a wurin suna yi wa masu sayen kaya hidima saboda haka sun san cewa za a riƙa katse musu hanzari. Tun da yake suna tunanin cewa kai ɗan ciniki ne, za su nuna maka sanin yakamata. Idan ka saka tufafi mai kyau kuma kana fara’a, hakan zai sa su girmama ka.
3. Ta yaya za mu guji ba wa masu ciniki haushi?
3 Ina Bukatar Yin Wa’azin Ne a Gaban Masu Ciniki da Yawa? Idan zai yiwu, ka zaɓi lokacin da mutane ba su da yawa a inda ake kasuwanci, kamar a lokacin da suka buɗe kantinsu. Ka jira har sai lokacin da babu kowa wajen manajar ko mai sayar da kaya a kantin kafin ka je ka yi masa wa’azi. Ka gajerta abin da za ka ce.
4. Mene ne za mu ce sa’ad da muke wa’azi a inda ake kasuwanci?
4 Me Zan Ce? Ka yi magana da manajan ko mai shagon, idan yana da ma’aikata da dama da suke aiki a ƙarƙashinsa. Kana iya cewa: “Yana da wuya mu samu ’yan kasuwa a gida, shi ya sa muka zo wurin kasuwancinka. Na san cewa kana bakin aiki, saboda haka ba zan ɗauki lokacin ka ba.” Domin kada a ɗauka cewa mu ’yan talla ne, zai dace kada mu ambata batun ba da gudummawa, idan ba su tambaye mu yadda ake tallafa wa aikinmu ba. Kana iya neman izini daga manajan don ka ɗan tattauna da masu yi masa aiki, idan irin kasuwancin da suke yi zai sa ka yi hakan. Ka sake gaya musu abin da ka gaya wa manajan. Idan ma’aikaci yana da aiki mai yawa da yake yi, ka gajerta maganarka kuma ka ba shi warƙa. Idan ba zai yiwu ka tattauna da ma’aikatan ba, wataƙila za a yarda ka ajiye musu littattafai a wani wuri.
5. Waɗanne dalilai ne ke akwai na yin wa’azi da ƙarfin zuciya a inda ake kasuwanci?
5 Yesu da Bulus sun yi wa mutane wa’azi a wuraren da suke kasuwancinsu cike da gaba gaɗi, kai ma za ka iya yin hakan. (Mat. 4:18-21; 9:9; A. M. 17:17) Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka don ka yi magana da ƙarfin zuciya. (A. M. 4:29) Ana samun mutane da yawa a wuraren da ake kasuwanci, kuna iya gwada yin wa’azi a irin wuraren nan.