Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Wa’azi a Wuraren Kasuwanci
Muhimmancinsa: Da yake mutane da dama suna daɗewa a wuraren kasuwancinsu, hanya mafi kyau da za mu yi masu wa’azi ita ce ta wajen zuwa inda suke aiki. Muna jin daɗin yin wa’azi a wuraren kasuwanci kuma hakan na kawo sakamako mai kyau. Me ya sa? Domin muna samun mutane da yawa kuma ’yan kasuwan suna yin fara’a don suna gani kamar mu kwastomomi ne. Masu shela suna bukatar nuna sanin yakamata da kuma yin shiga mai kyau idan suna so su sami sakamako mai kyau. (2 Kor. 6:3) Saboda haka, ya kamata mai kula da hidima ya riƙa lura da yadda ake yin wa’azi a wuraren kasuwanci da kuma masu shela da ke zuwa wuraren.
Ku Bi Shawarar Nan a Wannan Watan:
Sa’ad da kuke Ibada ta Iyalinku na gaba, ku gwada yadda za ku iya yin wa’azi a wuraren da ake kasuwanci a yankinku.