Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 5/13 p. 2
  • Wa Zai Fi Son Wannan Talifin?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wa Zai Fi Son Wannan Talifin?
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Gabatar da Talifi Ɗaya, Amma Ku Ba da Mujallu Biyu
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 5/13 p. 2

Wa Zai Fi Son Wannan Talifin?

1. Mene ne ya kamata mu yi tunani a kai sa’ad da muke karanta mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! da muka karɓa, kuma don me?

1 An shirya talifofin da ke cikin mujallun Hasumiyar Tsaro da Awake! don mutane dabam-dabam a dukan duniya su amfana. Saboda haka, waɗannan talifofin suna ɗauke da batutuwa dabam-dabam. Yayin da muke karanta kowane talifi a cikin mujallun da muka karɓa, zai dace mu yi tunani a kan waɗanda za su fi son batun da aka tattauna a cikin talifin kuma mu yi ƙoƙari don mu ba su.

2. Waɗanne batutuwa ne a cikin mujallunmu mutane za su so?

2 Shin Hasumiyar Tsaro ta kwana nan ta tattauna wani batu daga Littafi Mai Tsarki, wanda kai da abokin aikinka kun taɓa yin magana a kai? Akwai wani talifi da ya yi magana game da zaman iyali da zai iya taimaka wa wani danginka? Ka san wani da yake shirin zuwa wata ƙasa da aka taɓa ba da labarinta a cikin mujallar Awake!? Shin akwai ’yan kasuwa ko kuma ma’aikatan ƙananan hukumomi da ke yankinku da za su so wani cikin mujallun? Alal misali, tsofaffi da waɗanda suke kula da su za su so mujallar da ta yi magana game da ƙalubale da tsofaffi suke fuskanta. Jami’un tsaro za su so mujallar da take magana a kan aikata laifi.

3. Ka ba da labarin da ya nuna cewa ba da wasu mujallu wa mutanen da suke son batun da aka tattauna a ciki yana da amfani.

3 Sakamako: Sa’ad da wasu ma’aurata a Afirka ta Kudu suka karɓi mujallar Awake! na Oktoba 2011 mai jigo “How to Raise Responsible Children,” wato, “Yadda Za A Yi Renon Yara Su Zama Masu Kirki” sai suka kira makarantu 25 a waya don su tambaye su ko suna son mujallar. Makarantu ashirin da biyu daga ciki suka karɓi kofofin mujallun kuma suka rarraba wa ’yan makarantarsu. Wasu ma’aurata dabam a ƙasar sun ɗauki irin wannan matakin kuma suka ba da mujallu a makarantun da ke yankinsu. Malaman ɗaya daga cikin makarantun sun yi amfani da mujallun wajen koyar da ɗalibansu. Ma’auratan sun gaya wa wani mai kula da da’ira wannan labarin. Sai ya ƙarfafa ikilisiyoyin da ke da’irarsa su riƙa zuwa makarantun da ke yankinsu don ba da mujallu. Wannan ya sa ’yan’uwa da yawa suka bukaci ƙarin waɗannan mujallu daga ofishin reshe, kuma hakan ya kai ga sake buga ƙarin kofofi na wannan mujallar!

4. Me ya sa yake da muhimmanci mu rarraba mujallunmu wa mutane da yawa?

4 Mujallunmu suna bayyana ma’anar abubuwan da suke faruwa da darussan da za mu iya koya, kuma suna sa mutane su dogara da Littafi Mai Tsarki da kuma Mulkin Allah. Su ne kaɗai mujallun da ke “shelan ceto” a dukan duniya. (Isha. 52:7) Saboda haka, zai dace mu rarraba wa mutane da yawa sosai. Hanya ɗaya da ta dace da za mu yi hakan ita ce mu tambayi kanmu, ‘Wa zai fi son wannan talifin?’

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba