Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/14 p. 4
  • AGayyata ta Musamman

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • AGayyata ta Musamman
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Gayyata ga Kowa
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Za A Soma Kamfen na Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tuna da Mutuwar Yesu a Ranar 1 ga Maris
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Rarraba Takardun Gayyata na Taron Yanki
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Za A Soma Kamfen na Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tuna da Mutuwar Yesu a Ranar 22 ga Maris
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 4/14 p. 4

Gayyata ta Musamman

1. Yaushe za a soma gayyatar mutane zuwa manyan taro na shekara ta 2014?

1 A ce kana shirya wa abokanka ko kuma iyalinka liyafa ta musamman, kuma ka san cewa za ka kashe kuɗi da kuma lokaci mai yawa wajen yin hakan. Babu shakka za ka gayyace su da himma sosai, ko ba haka ba? Hakanan ma, an ɗauki lokaci sosai ana shirya abubuwan da za a tattauna a taron yanki da kuma na ƙasashe da za a yi a shekara ta 2014. Za mu soma gayyatar mutane zuwa wannan taron makonni uku kafin taron. Me zai taimaka mana mu yi hakan da ƙwazo?

2. Mene ne zai motsa mu mu yi wannan kamfen da ƙwazo sosai?

2 Idan muka yi tunani a kan yadda muke amfana daga koyarwar da Jehobah yake yi mana a manyan taro, hakan zai motsa mu mu yi wannan kamfen ɗin da ƙwazo sosai. (Isha. 65:13, 14) Ban da haka ma, ya kamata mu tuna cewa muna samun sakamako masu kyau daga kamfen da muke yi kowace shekara. Wasu da muka gayyata za su halarci taron. Amma ko da mutane nawa ne suka halarta, za mu ɗaukaka Jehobah kuma mu nuna cewa shi mai alheri ne ta wajen yin kamfen ɗin da ƙwazo.—Zab. 145:3, 7; R. Yoh. 22:17.

3. Wane tsari ne za mu bi don rarraba takardun gayyatar?

3 Rukunin dattawa a kowace ikilisiya zai tsara yadda za a rarraba gayyatar a yankinsu, kuma zai tsai da shawara ko za a bar takardun gayyatar a gidajen da ba a samu kowa ba da kuma rarraba su a wuraren da jama’a suke. A ƙarshen mako, ya kamata a ba da mujallunmu tare da takardun gayyatar idan da hali. Idan ranakun kamfen ɗin sun ƙunshi ranar Asabar ta farko a watan, a mai da hankali ga rarraba takardun gayyata maimakon soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane. Hakika a ƙarshen kamfen ɗin, za mu yi farin ciki sosai cewa mun yi shi da ƙwazo kuma mun gayyaci mutane da yawa don su zo su ji koyarwar da Jehobah ya shirya mana!

Abin da Za Mu Faɗa

Bayan gaisuwa, za ka iya cewa: “Muna kamfen ne na gayyatar mutane zuwa wani babban taro da za a yi a faɗin duniya. An rubuta kwanan wata da lokaci da kuma wurin taron a cikin takardar gayyatar.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba