Za A Soma Kamfen na Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tuna da Mutuwar Yesu a Ranar 1 ga Maris
1. Yaushe ne za mu soma gayyatar mutane zuwa taron Tuna da mutuwar Yesu kuma me ya sa lokacin kamfen ɗin ya fi na bara tsawo?
1 A ranar Jumma’a, 1 ga Maris, za mu soma kamfen da muke yi shekara-shekara don mu gayyaci mutane su zo su halarci taron Tuna da mutuwar Yesu tare da mu. Da yake za mu tuna da mutuwar Yesu a ranar 26 ga Maris ne, hakan yana nufi cewa tsawon lokaci na kamfen ɗin zai fi wanda aka saba yi a dā. Wannan zai sa mu sami zarafin gayyatar mutane da yawa fiye da dā, musamman ma a yankin da ikilisiyar da take wa’azi a yankin tana da yanki mai girma.
2. Wane tsari ne aka yi don karɓan takardun gayyata da kuma na rarraba su a yankinku?
2 Tsarin da Za A Bi: Dattawa za su ba da ja-gora a kan yadda za a yi wa’azi a yankunan, kuma za su gaya mana ko za mu iya barin takardun gayyatar a gidajen mutane idan ba su nan. Idan takardun gayyatar sun rage bayan mun gama yin wa’azi gida-gida a dukan yankunanmu, za mu iya rarraba su ta wajen yin wa’azi a tituna ko tashoshi ko kasuwa ko duk inda muka ga mutane. Mai kula da hidima zai tabbatar cewa an saka takardun gayyata da aka rubuta lokaci da kuma inda za a yi taron a kai a wurin karɓan littattafai, amma ba duka ba ne za a saka a wurin a lokaci ɗaya. Zai dace mu riƙa karɓan kofofin da za mu iya bayarwa a makon da ake ciki kawai.
3. Wane tsari ne za mu bi sa’ad da muke ba da takardun gayyatar?
3 Abin da Za Mu Faɗa: Zai dace mu taƙaita saƙonmu don mu iya gayyatar mutane da yawa. An tattauna yadda za mu ba da takardun ga mutane a shafi na 4 kuma za mu iya daidaita gabatarwar don ya dace da yankinmu. Hakika, bai kamata mu hanzarta saƙonmu ba idan maigidan yana jin daɗin tattaunawar kuma yana da tambayoyi. Sa’ad da kuke rarraba takardun gayyatar a ƙarshen mako, ku ba da mujallu a duk inda kun ga ya dace. A ranar 2 ga Maris, za mu mai da hankali ga rarraba takardun gayyatar, maimakon soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane kamar yadda muka saba yi a Asabar ta farko a kowace wata.
4. Me ya sa yana da kyau mu kasance da himma a yin wannan kamfen?
4 Muna fatan cewa mutane da yawa za su halarci wannan taron Tuna da mutuwar Yesu tare da mu. Jawabin da za a yi zai bayyana mana ainihi ko wane ne Yesu. (1 Kor. 11:26) Jawabin zai tattauna yadda mutuwarsa yake taimaka mana. (Rom. 6:23) Kuma zai bayyana mana abin da ya sa yana da muhimmanci mu riƙa tunawa da shi. (Yoh. 17:3) Bari mu kasance da himma sosai a yin wannan kamfen!