Gabatarwa
Abin da Za Mu Faɗa Sa’ad da Muke Kamfen Ɗin
“Barka dai. Mun kawo wa kai da iyalinka wata gayyata zuwa taro na musamman da ake yi kowace shekara a duk faɗin duniya. Za a yi wannan taron a ranar 26 ga Maris don Tuna mutuwar Yesu. Za a ba da jawabi daga Littafi Mai Tsarki kyauta wanda zai bayyana mana yadda mutuwar Yesu zai taimaka mana. Takardar tana ɗauke da adireshi da kuma lokacin da za a yi taron a yankinmu.”
Hasumiyar Tsaro Maris-Afrilu
“Muna son mu ji ra’ayinka game da wani mutum da Kiristoci da Yahudawa da kuma Musulmai suke girmama shi. Mutumin Musa ne. Me yake zuwa zuciyarka sa’ad da aka ambaci sunan nan Musa? [Ka bari ya ba da amsa.] Ko da yake ya yi kurakurai, Littafi Mai Tsarki ya faɗi abubuwa masu kyau sosai game da Musa. [Ka karanta Kubawar Shari’a 34:10-12.] Wannan mujallar ta tattauna abubuwa dabam-dabam guda uku game da halinsa da yadda za mu iya bin gurbinsa.”
Awake! Maris
“Za ka yarda cewa bai da sauƙi ga iyaye su yi renon yaransu, ko ba haka ba? [Ka bari ya ba da amsa.] Iyaye da yawa sun amfana daga shawara mai kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, wannan ayar ta taimaka wa magidanta da yawa su riƙa yaba wa yaransu a lokacin da ya dace kuma hakan zai sa su kasance da gaba gaɗi. [Ka karanta Kolosiyawa 3:21.] Wannan talifin ya tattauna abubuwa guda biyar da za su taimaki magidanta.”