Gabatarwa
Don Kamfen na Ba da Gayyata Zuwa Taron Tuna da Mutuwar Yesu
“Muna gayyatar mutane zuwa wani muhimmin taro. A ranar 3 ga Afrilu, miliyoyin mutane a faɗin duniya za su halarci taron Tuna da mutuwar Yesu Kristi kuma za su saurari jawabi da za a bayar kyauta a kan yadda mutuwarsa take amfanar mu. Wannan takardar gayyata ta nuna lokacin da za a soma taron da kuma inda za a yi taron a yankinmu.”
Hasumiyar Tsaro Maris–Afrilu
“Kamar dai cin hanci da rashawa a gwamnati ya daɗe yana yi wa ’yan Adam barazana. Me kake ganin ya jawo hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Akwai wani abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa da zan so in nuna maka. [Karanta Mai-Wa’azi 7:20.] Wannan mujallar ta nuna matakan da Allah zai ɗauka don ya magance matsalar cin hanci da rashawa. Ga naka mujallar, kuma zan so ka ɗan nemi lokaci don ka karanta ta.”
Awake! Maris
“Muna ɗan ziyartar maƙwabtanmu ne don mu nuna musu mujallar Awake! na kwanan nan. [Ka nuna masa bangon gaba.] Kowane mutum yana da nasa ra’ayin a kan wannan tambaya ta farko da ta ce: ‘Shin Allah ya wanzu kuwa?’ Tsakanin waɗanda suke imani da Allah da kuma waɗanda ba sa imani da shi, su waye ne kake ganin suke da ra’ayi mai kyau game da abin da zai faru a nan gaba? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga wani alkawarin da Allah ya yi da ke ba mutane da yawa bege. [Karanta Zabura 37:10, 11.] Wannan mujallar tana ɗauke da dalilai huɗu da suka sa zai dace mutum ya bincika ya gani ko Allah ya wanzu da gaske.”