Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 2/14 p. 4
  • Gabatarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gabatarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 2/14 p. 4

Gabatarwa

Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Maris

“Mutane suna da ra’ayoyi dabam-dabam game da Littafi Mai Tsarki. Wasu sun yarda cewa Kalmar Allah ce, wasu kuma suna masa kallon wani littafi ne kawai. Mene ne ra’ayinka game da Littafi Mai Tsarki?” [Ka bari ya ba da amsa.] Ka nuna masa shafin baya na Hasumiyar Tsaro na Maris-Afrilu, sa’an nan ku tattauna sakin layi na farko a ƙarƙashin tambaya ta farko da kuma nassosi biyu da aka rubuta a wurin. Ka ba shi mujallun kuma ka gaya masa cewa za ka dawo don ku tattauna sakin layi na gaba.

Hasumiyar Tsaro Maris–Afrilu

“Mun ziyarce ku ne don mu tattauna wani abu da ya shafi dukanmu a yau, wato mutuwar wani danginmu ko abokinmu. Shin ka yarda cewa ba abin da ya fi birkitar da mu kamar mutuwar wani abokinmu ko kuma danginmu? [Ka bari ya ba da amsa.] Nassin da za mu karanta yanzu ya ƙarfafa mutane da yawa. [Karanta Ishaya 25:8.] Wannan mujallar ta tattauna alkawarin da Littafi Mai Tsarki ya yi cewa za a kawo ƙarshen mutuwa kuma a ta da mutanenmu da suka mutu.”

Awake! Maris

“Muna ziyartar mutane ne don mu taimaka musu su fahimci wani batu da ke tayar wa mutane da yawa hankali. Ga batun a wannan ayar. [Karanta Farawa 1:1.] Wasu sun gaskata cewa an halicci sama da ƙasa amma wasu ba su gaskata da hakan ba. Mene ne ra’ayinka game da hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Mutane da yawa sun kasa yarda cewa an halicci sararin samaniya domin shugabannin addinai suna koyar da abin da Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba. Wannan mujallar tana ɗauke da bayanin Littafi Mai Tsarki dalla-dalla game da halittar sama da ƙasa.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba