Gabatarwa
Don Soma Nazarin Littafi Mai Tsarki a Asabar ta Farko a Watan Maris
“Mutane da yawa suna zato cewa kiyaye dokokin Allah zai hana mu jin daɗin rayuwarmu. Kana ganin cewa waɗanda suke kiyaye dokokin Allah sun fi farin ciki ne? [Ka bari ya ba da amsa.] An tattauna wasu bayanai masu ban sha’awa a wannan talifin a kan wannan batun.” Ka ba mai-gidan kofi na Hasumiyar Tsaro ta Janairu-Maris, kuma ku karanta da kuma tattauna abin da ke ƙarƙashin kan magana da ke shafi na 16-17. Ka karanta aƙalla nassi guda. Ka ba da mujallun, kuma ka shirya yadda za ka koma ziyara don ka amsa tambaya ta gaba.
Hasumiyar Tsaro Janairu-Maris
“Yana daɗa wa ma’aurata da yawa wuya kullum su kasance tare. Kana tunanin cewa yin nazarin Littafi Mai Tsarki tare zai taimaka wa ma’aurata su kusaci juna? [Ka bari ya ba da amsa.] Ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. [Karanta Matta 4:4.] Wannan talifin da ya soma daga shafi na 29 ya bayyana yadda za a iya jin daɗin yin nazarin Kalmar Allah.”
Awake! Maris
“Muna yi wa mutane magana game da wani mugun hali da ke ko’ina a yanzu. Kamar dai mutane a yau suna yawan yin fushi. Mene ne kake ganin ya jawo hakan? [Ka bari ya ba da amsa.] Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da fushi. [Karanta Zabura 37:8.] Wannan mujallar ta faɗi wasu dalilai da suka sa mutane suke yawan fushi a yau da kuma hanyoyin da za mu iya kame kanmu.”