Za a Soma Rarraba Takardun Gayyata na Tuna Mutuwar Yesu a Ranar 2 ga Afrilu
1. A yaushe ne za mu rarraba takardun gayyata na Tuna Mutuwar Yesu na wannan shekarar, kuma mene ne amfanin wannan kamfen da ake yi a kowace shekara?
1 Somawa daga ranar 2 ga Afrilu zuwa 17 ga Afrilu, za mu rarraba takardun gayyata na aukuwa mafi muhimmanci na shekara, wato, Tuna Mutuwar Yesu. A shekaru da suka gabata, waɗanda suke son saƙonmu da yawa sun yi na’am da wannan kamfen da ake yi a kowace shekara. Alal misali, a ranar Tuna Mutuwar Yesu, wata mata ta kira ofishin reshe ta ce: “Yanzu nake shiga gida, kuma na tarar da takardar gayyata a ƙarƙashin ƙofata. Ina so na halarci taron, amma ban san lokacin ba.” Ɗan’uwan ya bayyana mata inda za ta sami bayanin a takardar. Matar ta kammala da yin alkawari cewa, “Zan halarci taron da yamman nan!”
2. Mene ne za mu iya faɗa sa’ad da muke gabatar da takardar gayyatar?
2 Yadda Za Mu Gabatar da Takardar: Ya kamata mu taƙaita muhawwarar tun da yake lokaci kaɗan ne kawai muke da shi na rarraba takardun a dukan yankin. Za mu iya cewa: “Barka dai. Muna son mu ba iyalinka wannan takardar gayyata mai muhimmanci na tunawa da ake yi kowace shekara wanda za a yi a ranar Lahadi, 17 ga Afrilu. [Ka ba maigidan takardar gayyatar.] Wannan kwanan wata shi ne ranar tuna mutuwar Yesu. Za a ba da jawabi daga Littafi Mai Tsarki da zai bayyana yadda za mu iya amfana daga fansar Kristi. Wannan takardar gayyata ta nuna adireshi da kuma lokacin da za a yi taron a yankinmu.”
3. Ta yaya za mu iya gayyatar mutane da yawa?
3 Idan ikilisiyarku tana da babbar yanki, dattawa za su iya tsai da shawara a saka takardar gayyatar a ƙofar masu gidan muddin za a ajiye ta yadda wani ba zai gani ba. Ka tabbata cewa ka gayyaci waɗanda kake koma ziyara wurinsu da danginka da abokan aikinka da abokan makarantarka da kuma waɗanda ka sani. Sa’ad da kuke rarraba takardun gayyatar a ƙarshen mako, ku ba da mujallu a duk inda kun ga ya dace. Za ku iya yin hidimar majagaba na ɗan lokaci a watan Afrilu kuma ku saka hannu sosai a yin wannan kamfen mai daɗi.
4. Me ya sa muke son waɗanda suke son saƙonmu su halarci Tuna Mutuwar Yesu?
4 Masu son saƙonmu da suka halarci taron za su samu shaida sosai! Za su ji game da ƙauna mai girma da Jehobah ya yi ta wajen tanadar da fansa. (Yoh. 3:16) Za su koya yadda Mulkin Allah zai amfani ’yan Adam. (Isha. 65:21-23) Za a kuma gayyace su su yi magana da ’yan atenda kuma su nemi yadda za a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su don a koya musu ƙarin abubuwa. Fatanmu ne cewa masu zukatan kirki da yawa za su yi na’am da wannan kamfen kuma su halarci Tuna Mutuwar Yesu tare da mu!