Takardun Gayyata na Tuna Mutuwar Yesu Wanda Za a Rarraba a Dukan Duniya!
1. Wane shiri aka yi don rarraba takardun gayyata na musamman kafin Tuna Mutuwar Yesu?
1 “Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.” (Luka 22:19, Littafi Mai Tsarki) Don yin biyayya ga wannan umurni daga Yesu, masu bauta wa Jehobah za su taru tare da masu son gaskiya a ranar 30 ga Maris, na shekara ta 2010, don su tuna mutuwar Yesu. Za a rarraba takardun gayyata na musamman na Tuna Mutuwar Yesu a dukan duniya farawa daga 13 ga Maris zuwa 30 ga Maris.
2. Ta yaya za mu rarraba takardar gayyatar?
2 Yadda Za a Gabatar da Takardar: Za a iya ba maigida takardar gayyatar don ya ga hoton da ke bangon, sai ka ce: “A yamman ranar 30 ga Maris, miliyoyin mutane a dukan duniya za su taru don Tuna Mutuwar Yesu. Na zo ne don in ba kai da iyalinka wannan takardar gayyata don ku halarta. Muna yi wa abokanka ma maraba. Don Allah ka lura da lokaci da kuma wurin da za a yi wannan tunawar a yankinmu.” Bisa ga yanayin, kana iya karanta Luka 22:19 daga Littafi Mai Tsarki don nuna masa umurnin da ke cikin Nassi. Ka tuna cewa, tun da muna da ƙanƙanin lokaci don rarraba takardun a yankin, yana da kyau mu sa gabatarwar ta zama gajeriya.
3. Su wanene za mu iya gayyata?
3 Idan ikilisiyarku tana da babban yanki, dattawa wataƙila za su iya ce ku bar takardar a gidan da masu gida ba sa nan a farkon ziyararku. Sa’ad da ya dace, ku ba da mujallu tare da takardar gayyatar. Ku tabbata cewa kun gayyaci waɗanda kuka koma ziyara wurinsu, ɗaliban Littafi Mai Tsarki, abokan aiki, abokan makaranta, iyali, maƙwabta, da sauran mutanen da kuka sani.
4. Nuna godiya ga ƙaunar Jehobah na yin tanadin fansa zai motsa mu mu yi me?
4 Ku Yi Shirin Saka Hannu Sosai: Lokacin Tuna Mutuwar Yesu lokaci ne mai kyau na daɗa ayyukanmu. Za ku iya daidaita tsarin ayyukanku don ku yi hidimar majagaba na ɗan lokaci? Shin kuna da yara ko kuma ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke samun ci gaba mai kyau a ruhaniya? Idan haka ne, ku tattauna da dattawa don su ga ko waɗannan sun ƙware su yi saka hannu a rarraba waɗannan takardu a matsayin masu shela waɗanda ba su yi baftisma ba. Nuna godiya ga ƙaunar Jehobah na yin tanadin fansa zai motsa mu mu halarci Tuna Mutuwar Yesu kuma mu gayyaci mutane da yawa su halarta tare da mu.—Yohanna 3:16.