Za A Soma Kamfen na Gayyatar Mutane Zuwa Taron Tuna da Mutuwar Yesu a Ranar 22 ga Maris
A wannan shekarar za mu soma kamfen na gayyatar mutane zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu a ranar Asabar, 22 ga Maris. Ana ƙarfafa dukanmu mu saka hannu a wannan kamfen. Za mu iya ba da mujallu na kwanan nan sa’ad da muke wa’azi a ƙarshen mako idan da hali. A Asabar ta farko a watan Afrilu, za mu rarraba takardun gayyatar maimakon soma nazari da mutane. Amma idan muka sadu da wani da yake so mu yi nazari da shi, za mu iya yin hakan. Mai kula da hidima zai iya yanke shawarar ko zai fi dacewa a rarraba takardun ta hanyar yin wa’azi ga jama’a, idan za a fi samun mutane ta hakan. Ka rubuta sunayen dangoginka da abokan aikinka da abokan makaranta da kuma waɗanda kake nazari da su don ka gayyace su tun da wuri idan aka soma kamfen ɗin. Muna fatan mutane da yawa za su halarci wannan taron tare da mu yayin da za mu tuna da hanyoyi biyu mafi girma da aka nuna mana ƙauna.—Yoh. 3:16; 15:13.