Gabatarwa
Hasumiyar Tsaro Maris–Afrilu
“Masana sun gano cewa matsayin namiji yana da muhimmanci sosai a cikin iyali. Me kake ganin ya kamata namiji ya yi don ya zama maigidan kirki? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya bayyana abubuwa da ya kamata namiji ya yi don ya zama maigidan kirki. [Karanta Afisawa 5:28.] Wannan talifin ya tattauna fannoni shida da magidanta za su iya bin misalin Yesu.” Ka nuna masa talifin da ya soma a shafi na 10.
Awake! Afrilu
“Mun zo wurinku ne yau don mu tattauna wani abu da ke faruwa a iyalai da yawa. A dā iyaye ne ke iko a kan yara, amma a wasu iyalai a yau, yara sun fi ƙarfin iyayen. Kuna ganin iyaye suna tarbiyyar da yaransu yadda ya kamata kuwa? [Ka bari ya ba da amsa.] Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa tarbiyya yana da muhimmanci. [Karanta Misalai 29:17.] Wannan mujallar ta yi magana a kan yadda ya kamata iyaye su tarbiyyar da yaransu.”