Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Wa’azi ga Mutumin da Ke Wani Yare
Muhimmancinsa: Jehobah yana son mutanen “kowace al’umma” su ƙarfafa dangantakarsu da shi. (A. M. 10:34, 35) Shi ya sa Yesu ya ce za a yi wa’azin bishara a “iyakar duniya” da kuma “ga dukan al’ummai.” (Mat. 24:14) Zakariya ya annabta cewa mutanen “dukan harsunan al’ummai” za su ji saƙon bisharar. (Zak. 8:23) Wahayin da aka sauƙar wa manzo Yohanna ya nuna cewa waɗanda za su tsira wa babban tsanani za su ƙunshi mutane daga “cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” (R. Yoh. 7:9, 13, 14) Saboda haka, sa’ad da muka sami wani a yankinmu da ke wani yare, zai dace mu yi ƙoƙari mu yi masa wa’azi.
Ku Bi Shawarar Nan a Wannan Watan:
Sa’ad da kuke Ibada ta Iyalinku na gaba, ku gwada yadda za a iya yin wa’azi ga mutumin da ke wani yare.