RAYUWAR KIRISTA
Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Wa’azi ga Kowa a Yankinmu
ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI: Zakariya ya yi annabci cewa mutane daga dukan harsuna za su ji bishara. (Zak 8:23) Amma su waye ne za su koya musu bisharar? (Ro 10:13-15) Muna da gata da kuma hakkin yaɗa bishara ga koya a yankinmu.—od-E 84 sakin layi na 10-11.
YADDA ZA KA YI HAKAN:
Ku yi shiri. Kuna haɗuwa da mutanen da suke wani yare? Idan haka ne, za ku iya yin amfani da manhajar JW Language wajen koyan yadda za ku yi musu wa’azi. Ko kuma za ku iya yin amfani da na’ura wajen nuna musu yadda za su iya samun ƙarin bayani a dandalin jw.org a yarensu
Ku riƙa lura. Idan kuna wa’azi gida-gida, ku yi amfani da dukan zarafin da kuka samu wajen yi wa mutanen da suke wucewa a hanya da kuma waɗanda ke jira a cikin motocinsu wa’azi. Idan kuna wa’azi da amalanke, ku kasance a shirye don yi wa mutane wa’azi
Ku yi ƙwazo. Ku ci gaba da neman zarafin yin wa’azi ga mutanen da ba ku tarar da su a gida ba. Ku yi ƙoƙari don ku tattauna da mutum a kowane gida. Za ku iya zuwa wurin da safe da rana ko da yamma, ko kuma a ranaku dabam-dabam a makon. Za ku iya rubuta wa wasu wasiƙa ko ku yi musu waya ko kuma ku yi musu wa’azi a bakin titi
Ku koma ziyara. Kada ku yi jinkiri wajen zuwa wajen mutanen da suke son saƙonmu. Idan mutumin yana wani yare dabam, ku nema musu waɗanda suka iya yarensu. Ku ci gaba da ziyartar mutumin har sai wani mai shela da ya iya yarensu ya soma zuwa wurinsa.—od-E 94 sakin layi na 39-40
KU KALLI BIDIYON NAN SUN YAƊA BISHARA A ‘IYAKAR DUNIYA,’ SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:
Waɗanne shirye-shirye ne ʼyan’uwan suka yi don su yi wa mutanen da ke cikin ƙauyuka wa’azi? (1Ko 9:22, 23)
Waɗanne ƙalubale ne suka magance?
Waɗanne albarku ne suka samu?
Me za ku iya yi don ku yi wa mutane da yawa wa’azi a yankinku?