Yadda Za Ku Yi Amfani da Sauti
1. Ban da littattafanmu da aka buga, waɗanne abubuwa kuma muke da su?
1 Mutane da dama suna jin daɗin yin amfani da dandalin jw.org wajen karanta kalmomi masu daɗin ji da kuma na gaskiya. (M. Wa. 12:10) Amma, ka taɓa amfani da sautin littattafanmu kuwa? Hakan yana ba wa mutane damar sauraron abubuwan da muke da su a dandalinmu. Ta yaya za mu amfana idan muna sauraron sautin littattafanmu?
2. Ta yaya mu da iyalinmu za mu amfana daga sautin littattafanmu?
2 Don Nazari Mu Kaɗai ko Kuma da Iyalinmu: Idan muna so mu yi amfani da lokacinmu yadda ya dace, ya kamata mu riƙa sauraron sautin Littafi Mai Tsarki ko na mujallunmu ko kuma na wasu littattafanmu sa’ad da muke cikin mota da kuma lokacin da muke yin ayyukanmu na yau da kullum. (Afis. 5:15, 16) Za mu iya amfani da sauti sa’ad da muke ibadarmu ta iyali. Kowa zai iya riƙe nasa littafin kuma ya bi karatun yayin da ake sauraron sautin. Yin amfani da sauti yayin da muke nazari mu kaɗai zai taimaka mana mu kyautata yadda muke karatu kuma mu iya yaren da kyau.
3. Su waye ne a yankinmu za su amfana daga sautin littattafanmu?
3 Don Wa’azi: Wataƙila mutanen da suke ganin ba su da lokacin karanta littattafanmu za su so sauraron sautin littattafanmu. Ko kuma za mu iya haɗuwa da wasu da suke wani yare da muke gani za su so su ji saƙonmu a ‘nasu harshe.’ (A. M. 2:6-8) Wasu al’adu suna daraja kasa kunne sosai. Alal misali, a al’adar Hmong, tsofaffi suna gaya wa yaransu tarihi a baƙi kawai, amma duk da haka ba sa manta abin da aka gaya musu. Al’adu da yawa a Afirka suna koyar da muhimman darussa ta wajen ba da tatsuniya.
4. Waɗanne tambayoyi ne za mu iya yi wa kanmu game da taimaka wa mutane a yankinmu?
4 Zai dace ku yi amfani da sautin littattafanmu na yaren mutanen da ke yankinku kuwa? Shin akwai wani da zai amfana idan muka aika masa ɗaya daga cikin sautin littattafanmu ta saƙon imel kuwa? Za mu iya sauko da wani cikin littattafanmu a faifai kuma mu ba wa wani da yake son saƙonmu, idan zai yiwu mu ba shi har da littafin. Idan muka tura wa wani ɗaya daga cikin littattafanmu ko ƙasidu ko mujallu ko kuma warƙa ta waya ko kwamfuta, za mu iya ba da rahotonsa a ƙarshen wata. An wallafa sautin littattafanmu don mu yi amfani da su wajen yin nazari da kuma taimaka wa waɗanda muke musu wa’azi.—1 Kor. 3:6.