DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 1-5
Ayuba Ya Yi Aminci Sa’ad da Ya Fuskanci Gwaji
Ayuba yana zama a ƙasar Uz a lokacin da Isra’ilawa suke bauta a Masar. Ko da yake Ayuba ba Ba’isra’ile ba ne, amma ya bauta wa Allah da aminci. Mutanen gidansa suna da yawa, yana da arziki kuma yana da suna a yankinsa. Shi mashawarci da kuma alƙali ne mai adalci. Karimi ne ga talakawa. Babu shakka, Ayuba mutumi ne mai aminci.
Ayuba ya nuna sarai cewa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarsa
1:8-11, 22; 2:2-5
Shaiɗan ya lura cewa Ayuba yana da aminci. Bai musanta cewa Ayuba yana da aminci ba, amma ya ce ba da zuciya ɗaya yake hakan ba
Shaiɗan ya ce Ayuba yana bauta wa Jehobah saboda alherin da yake masa
Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya gwada Ayuba domin ya san cewa da’awarsa ƙarya ce. Shaiɗan ya sa Ayuba ya fuskanci matsanancin yanayi
Sa’ad da Ayuba ya ci gaba da yin aminci, sai Shaiɗan ya ƙalubalanci dukan mutane
Ayuba bai yi zunubi ba kuma bai ɗaura wa Allah laifi ba