DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 26-33
Ka Roƙi Jehobah Ya Ba Ka Ƙarfin Zuciya
Dauda ya kasance da ƙarfin zuciya don ya tuna yadda Jehobah cece shi
27:1-3
- Jehobah ya ceci Dauda daga bakin zaki sa’ad da yake matashi 
- Jehobah ya taimaka wa Dauda ya kashe bear don ya kāre tumakinsa 
- Jehobah ya taimaki Dauda ya ci nasara a kan Goliyat 
Me zai taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciya kamar Dauda?
27:4, 7, 11
- Addu’a 
- Wa’azi 
- Halartan taro 
- Nazari na kai da ibada ta iyali 
- Ƙarfafa wasu 
- Tuna yadda Jehobah ya taimaka mana a dā