DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | ZABURA 79-86
Wane ne Ya Fi Muhimmanci A Rayuwarka?
Wataƙila wanda ya rubuta Zabura ta 83 ya fito ne daga zuriyar Balawi Asaph, da ya yi rayuwa a zamanin Sarki Dauda. An rubuta wannan zaburar ne a lokacin da magabta suke wa bayin Allah barazana.
83:1-5, 16
- Sa’ad da marubucin zaburar yake addu’a, ya mai da hankali ne ga suna da kuma sarautar Jehobah ba nasa yanayin ba 
- Bayin Allah a yau suna fuskantar matsaloli da yawa. Jimrewa da muke yi yana ɗaukaka Jehobah 
83:18
- Jehobah yana so mu san sunansa 
- Wajibi ne mu nuna ta ayyukanmu cewa Jehobah ne ya fi muhimmanci a rayuwarmu