Ana ba da warƙar nan Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa? a ƙasar Tuvalu
Gabatarwa
AWAKE!
Tambaya: Me ya sa ya kamata mu yi shiri tun da wuri kafin bala’i ya auku?
Nassi: Mis 27:12
Littafi: Wannan mujallar ta bayyana abin da ya kamata mu yi kafin bala’i ya auku, sa’ad da yake aukuwa da kuma bayan haka.
KU KOYAR DA GASKIYA
Tambaya: Ta yaya za mu nuna cewa muna ƙaunar Allah?
Nassi: 1Yo 5:3
Gaskiya: Idan muna bin dokokin Allah, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar sa.
MATATTU ZA SU SAKE RAYUWA KUWA? (T-35)
Tambaya: Mutane da yawa a duniya sukan yi bukukuwa kowace shekara don su tuna da matattu. Za mu sake ganin waɗanda suka mutu kuwa?
Nassi: A. M. 24:15
Littafi: Wannan warƙar ta bayyana yadda za ka amfana daga tashin matattu. [Idan zai yiwu, ka nuna bidiyon nan Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?]
KA RUBUTA TAKA GABATARWA
Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.