DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AMOS 1-9
“Ku Biɗi Jehobah, Kuma Za Ku Rayu”
5:6, 14, 15
Mene ne biɗan Jehobah yake nufi?
Yana nufin mu ci gaba da koya game da Jehobah kuma mu yi rayuwar da ta jitu da nufinsa
Mene ne ya faru da Isra’ilawa bayan sun daina biɗan Jehobah?
Sun daina ‘son nagarta da ƙin mugunta’
Sun mai da hankali ga abin da zai amfane su kawai
Sun ƙi bin umurnin Jehobah
Mene ne Jehobah ya tanada don su taimaka mana mu koya game da shi?