DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYYUKAN MANZANNI 4-5
Sun Ci gaba da Koyar da Kalmar Allah da Ƙarfin Zuciya
Mene ne ya taimaka wa manzannin su zama ƙwararrun malamai? Me ya taimaka musu su yi wa’azi da ƙarfin hali? Domin sun kasance “tare da Yesu,” wanda shi ne Babban Malami kuma sun bi misalinsa. (A. M 4:13) Wane abu ne za mu iya koya daga misalin Yesu da zai taimaka mana mu zama ƙwararrun malamai?