DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | FITOWA 12
Muhimmancin Idin Ƙetarewa ga Kiristoci
12:5-7, 12, 13, 24-27
Dole ne Isra’ilawa su bi umurnin Jehobah don kada annoba ta goma ta shafe su kuma ’ya’yansu na fari su mutu. (Fit 12:28) An bukaci iyalai su zauna a gidajensu a daren 14 ga Nisan. An gaya musu su yanka lafiyayyen ɗan rago ko bunsuru. Kuma su yayyafa jinin a bakin ƙofofin gidajensu da kuma saman ƙofofin. Ƙari ga haka, an bukace su su gasa duka naman kuma su cinye da sauri. An gaya musu kada su fita ƙofar gida, sai gari ya waye. —Fit 12:9-11, 22.
A waɗanne hanyoyi ne yin biyayya yake kāre mu a yau?