Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb21 Janairu p. 5
  • Ku Kāre Aurenku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Kāre Aurenku
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Kiristoci Za Su Yi Nasara a Aurensu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Ka Kasance Da Farin Ciki A Aurenka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka Kasance Da Ra’ayi Mai Kyau Idan Kana Fuskantar Matsala A Aurenka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
mwb21 Janairu p. 5
Wani mutum ya zauna tare da matarsa suna wanke kaya da farin ciki.

RAYUWAR KIRISTA

Ku Kāre Aurenku

Jehobah yana ɗaukan alkawari da ma’aurata suka yi wa juna da muhimmanci kuma ya ce dole ne su manne wa juna. (Mt 19:​5, 6) A ƙungiyar Jehobah, akwai ma’aurata da yawa da suke kafa mana misali mai kyau. Duk da haka, ba ma’aurata da ba sa fuskantar matsala. Amma kada mu yarda da ra’ayin mutanen duniya cewa rabuwa ko kashe aure ne zai magance matsalolin. Ta yaya Kiristoci ma’aurata za su kāre aurensu?

Bari mu bincika hanyoyi guda biyar.

  1. Ku guji kwarkwasa da nishaɗi da ke ɗauke da lalata domin yin hakan zai ɓata aurenku.​—Mt 5:28; 2Bi 2:14.

  2. Ku ƙarfafa dangantakarku da Allah kuma ku ƙara ƙwazo wajen nuna cewa kuna so ku faranta masa rai a aurenku.​—Za 97:10.

  3. Ku ci gaba da nuna sabon hali kuma ku riƙa yi wa juna alheri domin ku ji daɗin aurenku.​—Kol 3:​8-10, 12-14.

  4. Ku riƙa tattauna abubuwan da suke damin ku a kullum kuma ku yi hakan da daraja.​—Kol 4:6.

  5. Namiji ya ba matarsa hakkinta na aure, matar ma ta yi hakan.​—1Ko 7:​3, 4; 10:24.

Idan Kiristoci suka daraja aurensu, hakan zai nuna cewa suna daraja Jehobah wanda ya kafa aure.

KU KALLI BIDIYON NAN WAJIBI NE KU YI TSERE DA JIMIRI​—KU BI DOKOKIN GASAR, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon nan ‘Wajibi ne Ku Yi Tsere da Jimiri’​—Ku Bi Dokokin Gasar.’ Dan’uwa da ’Yar’uwa Calou suna murmushi bayan an gama daura musu aure a Majami’ar Mulki.

    Ko da yake ma’aurata sukan soma aure da farin ciki, waɗanne matsaloli ne za su iya fuskanta?

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon nan ‘Wajibi ne Ku Yi Tsere da Jimiri’​—Ku Bi Dokokin Gasar.’ Dan’uwa da ’Yar’uwa Calou suna tattauna matsalolin da suke fuskanta cikin natsuwa. Sun kuma bude Littafi Mai Tsarki sun ajiye shi a kan teburi.

    Ta yaya ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su taimaka ma waɗanda suke ganin ba sa jin daɗin aurensu?

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon nan ‘Wajibi ne Ku Yi Tsere da Jimiri’​—Ku Bi Dokokin Gasar.’ Dan’uwa Calou yana karanta wa matarsa da ’yan matansa biyu littafin nan ‘Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki.’

    Ku bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don ku yi farin ciki a aurenku

    Waɗanne dokoki ne Jehobah ya ba wa ma’aurata?

  • Me ya zama dole ma’aurata su yi idan suna so su yi farin ciki a aurensu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba