KA YI WA’AZI DA KWAZO
Yadda Za Mu Yi Wa’azi
Haɗuwa ta Fari
Tambaya: Allah yana jin addu’o’i kuwa?
Nassi: Za 65:2
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Waɗanne batutuwa ne za mu iya addu’a a kai?
AN TATTAUNA NASSIN A LITTAFIN NAN:
Komawa Ziyara
Tambaya: Waɗanne batutuwa ne za mu iya addu’a a kai?
Nassi: 1Yo 5:14
Tambaya don Ziyara ta Gaba: Ta yaya Allah yake amsa addu’o’inmu?
AN TATTAUNA NASSIN A LITTAFIN NAN:
Rarraba Takardar Gayyata Na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu (27 ga Fabrairu–27 ga Maris)
“Muna gayyatar ka zuwa wani taro da miliyoyin mutane za su halarta. Taron na Tunawa da Mutuwar Yesu ne.” Ka ba [ko ka tura masa ta imel ko sakon tes] wa maigidan takardar gayyatar. Sai ka ce, “a cikin wannan takardar, akwai lokaci da kuma wurin da za a yi taron [ko kuma yadda za ka halarci taron ta na’ura]. Ban da haka, muna so mu gayyace ka zuwa wani taro na musamman da za a yi mako ɗaya kafin makon da za a yi taron Tunawa da Mutuwar Yesu.”
Tambayar da Za Ka Yi Idan Mutumin Ya So Wa’azin: Me ya sa Yesu ya mutu?