Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb22 Janairu p. 13
  • Darussa da Muka Koya Daga Rayuwar Sama’ila

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa da Muka Koya Daga Rayuwar Sama’ila
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Ci Gaba da Yin Girma a Gaban Jehobah
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Jehobah Ya Yi Magana da Sama’ila
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ya Jimre da Yanayin da Bai Yi Tsammani Ba
    Ka Yi Koyi Da Bangaskiyarsu
  • Sama’ila Ya Manne wa Nagarta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2022
mwb22 Janairu p. 13
Hotuna: Hotuna da aka dauko daga bidiyon “Ku Yi Koyi da Su—Sama’ila.” 1. Danny. 2. Sama’ila sa’ad da yake yaro.

RAYUWAR KIRISTA

Darussa da Muka Koya Daga Rayuwar Sama’ila

Sama’ila ya kasance da aminci ga Jehobah. Sa’ad da yake yaro, bai yi mugayen ayyuka kamar yaran Eli wato, Hophni da Phinehas ba. (1Sam 2:22-26) Sama’ila ya ci gaba da girma, kuma Jehobah ya kasance tare da shi. (1Sam 3:19) Sa’ad da ya tsufa ma, ya ci gaba da kasancewa da aminci ga Jehobah duk da cewa yaransa ba su bi halinsa ba.—1Sam 8:1-5.

Mene ne labarin Sama’ila ya koya mana? Idan kai matashi ne, zai dace ka kasance da tabbaci cewa Jehobah ya fahimci ƙalubale da kake fuskanta da kuma yadda kake ji. Zai iya taimaka maka ka kasance da karfin zuciya. (Ish 41:10, 13) Iyaye da ɗansu ko ’yarsu ta daina bauta wa Jehobah kuma fa? Ku ma za ku iya yin koyi da yadda Sama’ila bai tilasta wa yaransa su ci gaba da bin ƙa’idodin Jehobah ba. Amma ya bar kome a hannun Jehobah, sa’an nan ya ci gaba da riƙe amincinsa da kuma faranta ran Jehobah. Misali mai kyau da kuka kafa zai iya sa ɗanku ko ’yarku ta komo ga Jehobah.

KU KALLI BIDIYON NAN KU YI KOYI DA SU—SAMA’ILA, SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon “Ku Yi Koyi da Su—Sama’ila.” Sama’ila yana dauke da itatuwa a farfajiyar mazauni.

    Ta yaya Sama’ila ya nuna ƙarfin zuciya sa’ad da yake yaro?

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon “Ku Yi Koyi da Su—Sama’ila.” Danny yana yi wa yayansa magana game da irin salon rayuwar da bai dace ba da yake yi.

    Ta yaya Danny ya nuna ƙarfin zuciya?

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon “Ku Yi Koyi da Su—Sama’ila.” Annabi Sama’ila sa’ad da ya tsufa.

    Ta yaya Sama’ila ya kafa misali mai kyau sa’ad da ya tsufa?

  • Hoton da aka dauko daga bidiyon “Ku Yi Koyi da Su—Sama’ila.” Iyayen Danny bayan da suka gama wa’azi tare da shi.

    Jehobah yana taimaka ma waɗanda suka kasance da aminci

    Ta yaya iyayen Danny suka kafa misali mai kyau?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba