DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
Jehobah ‘Yana da Ikon Ba Ka Abin da Ya Fi Wannan Yawa’
Amaziya ya yi hayar sojoji don su yaƙi maƙiyan Allah (2Tar 25:5, 6)
Wani mutumin Allah ya shawarci Amaziya ya sallami sojojin (2Tar 25:7, 8; it-1-E 1266 sakin layi na 6)
Jehobah zai iya biyan Amaziya fiye da kuɗin da ya kashe (2Tar 25:9, 10)
KA TAMBAYI KANKA: ‘Wace sadaukarwa ce zan iya yi don in ƙara ƙwazo a ibadata ga Jehobah? Waɗanne albarku ne zan samu idan na yi hakan?’—Mal 3:10; w21.08 30 sakin layi na 16.